| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
’Yansandan Nijeriya sun kama wata mota da ‘abubuwan fashewa’ a Jihar Oyo
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an rundunar 'yansandan sun yi nasarar kama babbar motar ne bayan sun kafa wani shingen binciken ababen hawa sakamakon samun bayanan sirri.
’Yansandan Nijeriya sun kama wata mota da ‘abubuwan fashewa’ a Jihar Oyo
Rudunar 'yansandan ta ce direban babbar mota ya shiga hannu kuma yana bayar da haɗin kai wajen bincike / Nigeria Police
26 Janairu 2026

Rundunar ’yansandan Nijeriya ta ce ta kama wata babbar mota ɗauke da wasu abubuwa da ake zargin masu fashewa ne a Jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da na Jihar Ayanlade Olayinka ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an rundunar sun yi nasarar kama babbar motar ne bayan sun kafa shingen binciken ababen hawa sakamakon samun wasu bayanan sirri.

Masu AlakaTRT Afrika - ‘Yansandan Nijeriya sun kama wata amarya a Jigawa kan zargin kashe angonta da maganin ɓera

Ya ce an kama motar ne a garin Saki kuma Kwamishinan ’Yan sanda na JIhar Oyo Femi Haruna ya umarci jami’an rundunar su fara cikakken bincike kan abubuwan fashewar.

Kazalika sanarwar ta ce tuni wasu ƙwararru suka fara bincike kan abubuwan fashewar kuma jami’in hulɗa da jama’a na ’yansandan ya ce direban babbar mota ya shiga hannu kuma yana bayar da haɗin kai wajen binciken.

Kwamishinan ’yansandan Jihar ya baya wa ƙoƙarin Babban Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya Kayode Egbetokun dangane da salon “shugabancinsa da kuma yadda ya duƙufa wajen tabbatar da cewa rundunar tana aiki da bayanan sirri a duk faɗin ƙasar.”

Rundunar ’yansandan Jihar ta Oyo ta bai wa al’ummar jihar tabbaci kan tsaron lafiyarsu kuma ta buƙaci jama’a su kwantar da hankulansu.