Sarakunan yankin sun sha alwashin bayar da muhimmiyar gudunmawa don magance matsalar tsaron yankin. Hoto/ Fadar shugaban Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya daga yankin Tillaberi a fadarsa da ke Niamey ranar Alhamis.

Sarakunan sun je fadar ne don su yi masa karin haske kan tattaunawar da suka yi da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Hamadou Adamou Souley game da matsalar tsaron yankin.

Ganawar ta mayar da hankali kan tsaro da rikice-rikicen da ake samu tsakanin kabilu a yankin.

Sarkin Sakoira Canton Dokta Moussa Sadou Kalilou ya ce yankin Tillaberi zai dukufa wajen addu'o'i da kokarin lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'ummomin yankin.

Har ila yau sarakunan sun sha alwashin yi wa al'ummominsu tarukan wayar da kai don kawo karshe kyama tsakanin kabilun yankin da dawo da fahimtar juna da aka san yankin da shi a baya.

Shugaba Bazoum ya nuna godiyarsa ga sarakunan game da kokarinsu na magance matsalar tsaro kuma ya sha alwashin ba su goyon baya a kan hakan.

Makarantu fiye da 900 aka rufe a watan Mayu a yankin Tillaberi saboda matsalar tsaro. Hoto/Fadar shugaban Nijar

Akalla makarantu fiye da 900 ne aka rufe a watan Mayu a yankin Tillaberi saboda matsalar tsaro, wanda daukar matakin ya yi sanadin ya tsayawar karatun dalibai kimanin 80,000 a halin yanzu.

Yankin yana kan iyakar kasashe uku ne: Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

TRT Afrika