'Yan sanda sun ce maharan sun kashe wasu jami'ansu. Hoto/ Reuters 

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun ce ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka biyu da aka sace a jihar Anambra da ke kudancin kasar.

Sanarwar da kakakin rundunar reshen jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya fitar ranar Juma'a ya ce "da sanyin safiyar yau, 19 ga watan Mayun 2023, gamayyar jami'an tsaro ta ceto sauran mutum biyu da aka sace lokacin da aka kai hari kan tawagar motocin ofishin jakadancin Amurka" a jihar Anambra.

Ya kara da cewa babu abin da ya samu mutanen da aka kubutar.

A cewarsa 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kuma zai sanar da manema labarai da zarar an samu karin bayani kan maharan.

Yadda aka kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka a Anambra

Akalla mutum hudu aka kashe a harin da aka kai wa ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a kan hanyar Atani zuwa Osamale a Jihar ta Anambra.

Tun da farko, DSP Tochukwu ya shaida wa TRT Afrika cewa wadanda suka kai harin sun kashe ‘yan sanda biyu da ma’aikatan ofishin jakadancin na Amurka biyu.

“Bata-garin sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu da wasu ma’aikatan ofishin jakadancin, suka kuma cinna wa gawarwakinsu da motarsu wuta.

“Ko da maharan suka ga jami’an ‘yan sanda na zuwa wurin, sai suka yi garkuwa da ‘yan sanda biyu da direban mota ta biyun inda suka gudu. Babu wani dan kasar Amurka a cikin kwambar motocin,” in ji shi.

TRT Afrika