Shirin Great Green Wall of the Sahara and the Sahe shiri ne don kare muhalli /Photo: Niger Presidence

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya jagoranci bude taron musamman kan yaki da sauyin yanayi na Forum on Private Sector Engagement for the Great Green Wall Initiative.

Shugaban ya yi hakan ne a babban dakin taro na tuna wa da Mahatma Gandhi da ke birnin Niamey ranar Litinin.

Hukumar bayar da lamuni ta duniya (IMF) da hadin gwiwar Ma'aikatar Muhalli da Yaki da Sare Itace ta Nijar da shirin Futures Agribusiness (FAGRIB) da shirin the Great Green Wall Foundation (GGWoA) da kuma shirin the Pan-African Agency of the Great Green Wall (APGM) ne suka ce suka shirya taron.

Taken taron shi ne "Samar da kasuwa da dawo da kasa da kuma duniya" taron yana fatan kamfanoni masu zaman kansu da ke yankin Sahel za su taimaka wajen cimma wadannan muradan.

Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Nijar Seyni Oumarou da Firaiministan kasar da kuma tsohon Shugaban Nijar Issoufou Mahamdou wanda kuma shi ne jagoran shirin Great Green Wall.

Shirin Great Green Wall of the Sahara and the Sahe shiri ne don kare muhalli wanda a harshen Faransanci ake kira Grande Muraille Verte pour le Sahara et le Sahel.

Kungiyar Tarayyar Afirka ce ta fara shirin a shekarar 2007 saboda yaki da kwararowar hamadar Sahara ta hanyar shuka bishiyoyi a gaba daya yankin Sahel daga kasar Djibouti zuwa birnin Dakar a kasar Senegal.

Da farko fadin katafariyar katangar bishiyoyi da za a shuka an shirya za ta kai kilomita 15, sai tsawonta daga farko zuwa karshe ya kai kilomita 7,775 kodayake daga an fadada shirin, inda aka saka wasu karin kasashe a yammaci da arewacin Afirka.

Shirin yana da burin dawo da hekta miliyan 100 na kasa daga mamayar hamadar Sahara da tsaftace muhallinmu, inda za a rika cire tan miliyan 250 na iskar carbon dioxide da samar da ayyuka miliyan 10 daga nan zuwa shekarar 2030.

TRT Afrika