An soma zabe a Togo bayan amincewar ƴan majalisar dokokin kasar kan sabon kundin tsarin mulki. Hoto: AP      

An soma kaɗa ƙuri'u a zaɓen ƴan majalisun dokoki a ƙasar Togo a yau Litinin bayan sake fasalin tsarin mulkin kasar da ƴan adawa suka ce zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe damar tsaiwaita wa'adin mulkin danginsa.

Zaben kasar na zuwa ne bayan amincewar ƴan majalisa na yi garambawul ga kundin tsarin mulki na ƙasar a farkon watan Afrilu da ya haifar da wani sabon tsari irin na Firaiminista.

Ƴan adawa dai na fargabar tsarin zai dace da Gnassingbe don kauce wa ƙayyade wa'adin mulkin shugaban ƙasa tare da ci gaba da riƙe muƙamin.

Gnassingbe dai ya shafe kusan shekaru 20 riƙe da kujerar shugaban kasa a Togo bayan da ya gaji mahaifinsa Gnassingbe Eyadema, wanda shi ma ya riƙe mulkin ƙasar na kusan shekaru 40 bayan juyin mulkin da aka yi.

Za a zabi ƴan majalisa 113 a ranar Litinin, sannan a karon farko za a gudanar da zaben shugabannin shiyya-shiyya 179 daga gundumomi biyar na kasar, wadanda tare da kansilolin kananan hukumomi za su zabi sabuwar majalisar dattawa.

Ƴan majalisa ne za su zabi shugaban kasa

Wannan tsarin ga jam'iyyar UNIR mai mulki ta Gnassingbe zai bai wa Togo damar samun wakilai, sai dai ga jam'iyyun adawa waɗanda suka tattara magoya bayansu don su kada kuri'ar adawa sun kira tsarin da ''juyin mulki''.

"Muna son mutane da dama su fito kada kuri'a a ranar litinin sosai don mu samu damar iya bai wa ƴan adawa damar samun nasara da kuma iko a majalisa,'' a cewar Afi Akladji, wani mai sayar da takalma kana mai goyon bayan babbar jam'iyyar adawa ta ANC.

Tuni dai Gnassingbe mai shekaru 57 ya lashe zaɓuka hudu, wadanda ƴan adawa suka ce suna cike da kura-kurai.

A karkashin kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi wa garambawul, zai samu damar sake tsayawa takara ne sau ɗaya kacal a matsayin shugaban kasa a shekarar 2025.

Bisa ga sabon kundin tsarin mulkin ƙasar da ƴan majalisa suka amince da shi a ranar 19 ga watan Afrilu, za a zabi shugaban kasar Togo ne a wa’adin shekaru hudu ta hanyar zabe daga ƴan majalisu kai tsaye ba wai jama'a ba.

Ingantattun ababen more rayuwa

Ƙasar Togo ta sake fasalin tsarin mulkin kasar daga shugaban ƙasa zuwa tsarin majalisar dokoki, wanda a yanzu mulki zai kasance a hannun Firaminista wanda dole ne ya zama "shugaban jam'iyyar masu rinjaye" a Majalisar Dokoki ta kasa.

Tuni dai jam'iyyar Gnassingbe ta ''Union for the Republic'' ko kuma jam'iyyar UNIR ta samu rinjaye a majalisar dokoki.

Idan har jam'iyya mai mulki ta yi nasara a ranar Litinin, Gnassingbe na iya riƙe wannan sabon mukami.

Ga magoya bayansa, tsawaita wa'adin shugabancin Gnassingbe na nufin ci gaba da shirye-shiryensa na raya ƙasa da suka ce sun taimaka wajen inganta ababen more rayuwa a Togo.

“Muna da hanyoyi musamman a Lome, sannan an gina makarantu, an kuma soma gudanar da ayyuka da suka shafi mata, matasa da manoma,” in ji Evariste Yalo, ƴar shekara 31, mai gyaran na'urar kwamfuta kana mai fafutuka ta jam''iyyar UNIR.

Masu sa ido kan zaɓen

''Ƙasar ta na tafiya a hanyar da ta dace, don haka dole ne shugaban ya ci gaba."

Ƙungiyar tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta ce, ta tura tawagar masu sa ido kan zaɓe zuwaTogo karkashin jagorancin tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Gambia Fatoumata Jallow-Tambajang.

Tuni dai hukumomi suka hana yunkurin ƴan adawa na shirya zanga-zangar adawa da sauye-sauyen da aka yi kundin tsarin mulkin ƙasar.

Kazalika ita ma babbar hukumar kula da harkokin sadarwa ta Togo (HAAC) ta ƙi amincewa ta bai wa duk wasu kafafen yada labarai na kasashen waje damar daukar bayanai zaɓen.

AFP