Alban Sumana Kingsford Bagbin Ghana Parliament

Kakakin majalisar dokokin Ghana, Alban Sumana Bagbin ya soki mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris, dangane da maganarta kan hakkin 'yan luwadi da madigo LGBT, da ke kasar ta yammacin Afirka.

Mr. Bagbin ya ayyana kalaman na Madam Harris a matsayin masu “karan tsaye ga tsarin dimokradiyya”, inda ya jaddada cewa bai kamata a amincewa kalaman nata ba.

Kakakin majalisar ya sanar da martaninsa ne yayin da yake ganawa da wasu shugabannin addini a Ghana ranar Talata.

Mr. Bagbin ya ce Madam Harris ko Amurka ba su da damar kakaba wa kan kasa mai ‘yancin kai kamar Ghana ra’ayinsu kan batutuwan ‘yancin dan Adam,.

An ruwaito Madam Harris tana cewa “Ina da kakkarfan tunani game da muhimmancin goyon bayan ‘yanci da tallafawa yaki don tabbatar da daidaito tsakanin mutane, da kuma cewa dole a mu’amalanci duka mutane daidai wa daida”.

Madam Harris ta ambaci hakan ne a yayin wani taron ‘yan jarida da ta gabatar tare da shugaban Ghana, Nana Akuffo-Addo. A taron, Madam Harris ta yi kalamai da suka nuna damuwarta kan batun ‘yancin ‘yan LGBT a Ghana.

Abin da ke daukar hankali a batun shi ne wani kudurin doka da ke gaban majalisar Ghana mai suna “Kudurin Daukaka ‘Yancin Kyakkyawar Mu’amalar Jinsi da Martabar Iyali”.

Daga cikin tanade-tanaden kudurin akwai dauri a gidan kaso ga mutanen da suka bayyana kansu a matsayin 'yan luwadi da madigo, da kuma haramta daukaka batun LGBT a kasar Ghana.

Duk da cewa majalisar Ghana ta gudanar da jin-ra’ayin jama’a kan kudurin tun daga shekarar 2021, har yanzu ba a gabatar da kudurin a zauren majalisa ba don kada masa kuri’a.

A halin yanzu, akwai dokar haramta luwadi a Ghana wadda ta tanadi dauri har tsawon shekara uku, yayin da sabon kudurin dokar da ake muhawara a kai yake neman kara wa’adin daurin.

Madam Harris ta iso Ghana ne ranar Lahadi, don fara ziyararta ta farko a Afirka a matsayinta na mataimakiyar shugaban kasa.

Ta gana da shugaban Ghana Akuffo-Addo ranar Litinin, wanda ya bayyana cewa kudurin doka kan LGBT ba shi ne ra’ayin gwamnatinsa a hukumance ba.

Mr. Akuffo-Addo ya ayyana cewa ministansa na shari’a ya riga ya gabatar da shawarwarin gwamnatinsa ga kwamitin majalisa, mai suna “Kwamitin Tsarin Mulki da Harkokin Shari’a”, kan wasu tanade-tanaden kudurin, don neman sauya “manyan jigoginsu”.

TRT Afrika da abokan hulda