Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai ‘yan Kenya miliyan 4.4 da suke fuskantar tsananin yunwa Photo/ AA

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa alkamar da aka samu ta hanyar yarjejeniyar jigilar tsaba tsakanin Ukraine da Rasha da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya ta isa Kenya daga Ukraine.

Shirin na Black Sea Initiative – shiri ne na musamman da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wanda Turkiyya ta jagoranta a Yulin 2022, wanda zai bayar da dama a yi jigilar tsaba da sauran kayan abinci da takin zamani daga tashoshin jiragen ruwa na Bahar Aswad uku da ke Ukraine a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki.

“Tsaba daga manoman Ukraine ta iso, wadda za a ba iyalan da masanancin fari ya tagayyara da kuma wadanda suka rasa muhallansu a yankin,” kamar yadda WFP ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Tan 25,000 shi ne lodin tsabar da Kenya ta karba a karon farko a karkashin shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya domin wadata kasashen da ke bukatar agaji ta hanyar yarjejeniyar hatsi ta Ukraine da Rasha.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai ‘yan Kenya miliyan 4.4 da suke fuskantar tsananin yunwa a sassan kasar sakamakon farin da ya ki ci ya ki cinyewa.

Majalisar ta kuma yi gargadin wannan adadin zai iya karuwa zuwa miliyan 5.4 zuwa watan Yuni. WFP ya samar da sama da tan 500,000 na alkama daga Ukraine karkashin wannan yarjejeniya.

Habasha ita ma ta amfana da wannan shiri. A ranar 18 ga watan Maris din 2022 Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kara wa’adin wannan yarjejeniya.

Rasha ta bayyana cewa a shirye take domin kara wannan wa’adi da kwanaki 60.

Majalisar Dinkin Duniya ta jinjina wa Turkiye kan irin rawar da ta taka ta fuskar diflomasiyya da kuma tallafa wa wannan shirin.

TRT Afrika