Biontech-Produktion in Marburg / Photo: AFP

Ministar Lafiya ta Tanzaniya Ummy Mwalimu ya ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar Marburg a yankin Kagera da ke arewa maso yammacin kasar.

Minista Ummy Mwalimu ta bayyana hakan ne a ranar Talata 22 ga watan Maris tana mai cewa an fara gano bullar cutar ne bayan da hukumomin lafiya na Tanzaniya suka gudanar da gwaje-gwaje.

“Marburg wata kwayar cuta ce da aka fara gano ta a kauyen Marburg da ke kasar Jamus a shekarar 1967, kuma tun lokacin aka saka mata wannan sunan," in ji Dr Edesio Henry Makaria, wata kwararriya a Asibitin Muhimbili National Referral na Tanzania, gundumar da annobar ta barke.

"Dabbobi ke yada ta"

A cewar Dr Makaria, dabbobi ne suka fara yada cutar a tsakanin mutane, kuma mai yiwuwa mu'amalar da mutane ke yi da dabbobi a gundumar ce ta sa ta kara yaduwa.

Cutar ta fi yaduwa ne ta hanyar taba ruwan jiki kamar gumi da yawu.

Cutar kan fara The disease incubation period in the body is from the second day of exposure to the 21st day. However, many patients experience severe symptoms of bleeding within seven to nine days based on the knowledge gained from previous outbreaks, and there is no vaccine or treatment until now.

Cutar kan fara bayyana ne bayan kwana daya zuwa kwana 21 bayan ta shiga jikin mutum.

Sai dai kuma masu fama da cutar da yawa suna ganin alamun cutar na zubar da jini cikin kwana bakwai zuwa tara bisa da kamuwa bisa ga abubuwan da aka gani a lokutan da cutar ta barke a baya, kuma har yanzyu babu rigakafi ko maganin cutar.

"Alamun cutar Marburg sun hada da zafin jiki cikin kankanin lokaci, ciwon kai mai radadi da kuma gajiya." Inji Dakta Makaria a lokacin da take zantawa da TRT Africa.

Ta kara da cewar: "kwayar cutar Marburg ‘yar uwar kwayar cutar Ebola ce; cuta ce mai hadari dake sa zazzabi mai lalata sassan jiki ciki har da hanyoyin jini, inda kashi 90 cikin 100 na masu fama da cutar ke mutuwa."

Duk da cewar cutar Marburg 'yar uwar cutar Ebola ce, cutar Marburg ba ta yaduwa kamar cutar Ebola

Sabanin cutar Ebola, yaduwar cutar ba sosai ba, amma tana kashe mutum sosai. Dakta Makaria ta shawarci mutane su garzaya asibiti dake kusa duk lokacin da suka fara ganin alamun cutar.

"kada ku yi jinyar kanku a gida," inji Makaria

Kwayar cutar tana yaduwa ne zuwa ga mutane daga jemagu da kuma dabbobin da ake ci a yankunan.

Hukumar lafiya ta Majalisar dinkin Duniya ta ce tana taimaka wa ma’aikatar lafiya wajen tura ma’akatan ba da tallafin gaggawa yankin Kagera don bincike kan cutar.

Ta shafinsa na Twitter, shugaban hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka, Dr Ahmed Ogwell, ya ce hukumar za ta hada kai da Tanzaniya.

“Muna tare Tanzaniya a kan wannan cutar ta Marburg din da ta barke. Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka za ta tura ma’aikatanta bakin aiki kai tsaye don don karfafa yadda ake ba da agaji tare da dakile hadarin yaduwar cututtukan ta yadda za a kiyaye lafiyar Afirka,” inji Ogwell.

Yadda za ka kiyaye kanka daga cutar

Edesio Henry Makaria, kwararren likita a sashin kula da cututtukan kananan kwayoyin cuta a babban asibitin kwararru na Muhimbili dake Tanzaniya, ya ce akwai hanyoyin da za ka iya bi wajen kare kanka daga kamuwa da cutar.

Ga wasu shawarwari kadan:

  • Saka kayan kariya na asibiti (PPE)
  • Sa safar hannu da takunkumin rufe fuska
  • Kebe mara lafiya
  • Wanke wuraren da mutumin da ya kamu da cutar ya taba, alluran da yay a yi amfani da su da kuma duk abin da ya fito daga jikinsa ( wannan ya hada ba-haya da jini da yawu da fitsari).

A Afirka, an ba da rahoton barkewar wannan cutar a wannan shekarar a karon farko a Equatorial Guinea a ranar bakwai ga watan biyu na shekara 2023, kuma a ranar sha uku ga watan biyu na shekarar 2023, aka bayya cutar a matsayin cutar Marburg.

TRT Afrika