A arewacin Nijeriya ana kiran nau'in abincin kwalan din  da AWARA, a kudancin kasar kuma da WARA. Hoto: Amina Mayana

Daga Abdulwasiu Hassan

Fitacciyar jarumar nan Ba’amurkiya mai zane kuma marubuciya Maira Kalman ta ce, "Duk wanda na sani yana bukatar abin da zai sanyaya masa rai tare da samun kayan kwalam da makwalashe masu dadi."

Awara, abincin kayan kwalam ne da ake samu daga ‘Tofu’ ko cuku mai tsami a Nijeriya, wadda ake hadawa da waken soya ko madara.

A nahiyar Afirka da ke da fadin tattalin arzikin, Awara - ko wara - ta wuce abincin kwalam ko na marmari da ake ci. Yawanci dai ’yan makaranta ne suka mayar da ita tamkar wata al’ada da ba sa gajiya da ita.

A lokuta da dama marasa lafiya ma na son tu'ammali da awara saboda amfaninta a jikin mutum da kuma yadda take gyara dandanon baki.

Su ko dillalai sun yi imanin ribar da ake samu a sana’ar sayar da awara, la’akari da cewa abu ne da ake ci ako da yaushe sannan a kowane yanayi.

A hirar da TRT Afrika ta yi da Fati Malam Hussaini, wacce ta gina sana'arta ta wannan abinci na kwalam mai sauki da kuma gina jiki ta ce "Mudu biyar na waken soya na iya samar da awara ta naira 20,000."

Ana hada AWARA da madara ko da waken suya. Hoto: Amina Mayana

Fati na kashe kusan Naira 1,600 wajen hada awara daga awon waken soya. Sannan a naira 8,000 dillalan da take ba su, za su iya samun ribar fiye da naira 11,000 ta hanyar sarin awara.

Dandano mai gamsawa

Sana’ar awara ta yi fice a Nijeriya saboda yadda ake sarrafa ta - ko dai a matsayin kayan kwalam da makulashe ko kuma a matsayin wani nau’in abinci da aka ware wa masu bukatar sinadarin furotin a jikinsu.

Ko kuma kayan marmari da za a iya ci a ko da yaushe ba tare da an yi wani dogon tunani ko fargaba ba.

Kamar yadda a arewacin Nijeriyya ake kiranta da suna awara ko wara daga kudancin kasar, ana fitar da cukwui mai tsami ne daga madarar waken suya.

Hanyoyin da ake bi wajen sarrafa wara dai na da sauki kamar yadda ake shuka waken da ake hada ta da shi.

Ana nika waken suya ne bayan an jika shi da ruwa, sannan a rika tacewa.

Daga nan kuma sai a hada ruwan da wasu sinadirai kamar kanwa da alum ko ruwan tsami a dafa har sai ya tafasa.

Wasu na son cin abincin da dan yaji - yaji. Amina Mayana

Daga nan, sai a zubar da ruwan ciki ta hanyar tacewa tare da barin cukwi din dake hade jiki ya zama awara, sannan a yayyanka dai-dai girman da ake so.

Sai a soya, daga nan kuma sai a zuba kayan hadin da ake bukata don samun dandano mai gamsarwa.

Lafiyayyen abinci

An fi hada nau’in abincin da madara inda a wasu yankin tsakiya da kudancin Nieriya suke kiransa da suna wara, a cewar masu hada abincin gargajiya na cikin gida daga yankin an samar da suna wara ne daga wani gari a jihar Kwara inda ake kyautata zaton cukwin ya samo an asali.

Bambancin na madarar saniya da ake samu, mata makiyaya wadanda mafi yawansu Fulani ne da ke yankin Kudu maso yammancin kasar ke tanadinsa.

Da farko bayan tatso nonon shanu, za a tace dattin ciki da rariya. Ana matse wasu ruwan 'ya'yan itacen tuffa a cikin madarar a matsayin abin da zai sa ta yi kauri sai a dafa na dan wani lokaci.

Da zarar madarar ta tafarfasa kuma ta yi kauri, sai a yi wara ko kuma awara ta zama guda guda bayan ta wuce sai a yanka a soya.

Jami'an kiwon lafiya sun ce AWARA na da wadataccen sinadarin furotin a cikinsa.Hoto: Amina Mayana

Baya ga zama abincin kwalam tsakanin daliban ‘yan makarantun firamare a arewacin Nijeriya, an dade ana amfani da awara a madadin nama ko kifi a cikin abinci kala-kala da ake dafawa a gida.

A wasu lokuta, awara na cike gibin nau’ukan sinadaran da jikin dan adam ke bukata daga dabbobi kamar nama da kifi da wasu lokutan ba a iya saya saboda karancin kasafin kudi.

Amfanin da awara take da shi a jikin dan adam na da yawan gaske. Baya ga sinadarin furotin, tana dauke da wasu karin sinadarai kamar magnesium da calcium da fiber da fatty acids da sinadarin carbohydrate mai kara kuzari da bitamin B da C da K da iron da kuma manganese.

Likitoci sun ce tana taimakawa wajen kosarwa da narkewa da sauri a cikin mutum, sannan tana taimakawa garkuwar jiki, tare da karfafa hanyoyin jini, da kuma rage maikon cholesterol, da inganta lafiyar kashi.

Sannan zabi ne mai sauki ga masu ciwon sukari da masu fama da matsalar rashin narkewar abinci a cikinsu.

Masu iya magana kan ce, farin cikin na samuwa ne idan mutum ba shi da wata damuwa kan abin da yake so ya ci. Ga ‘yan Nijeriya kam ana iya cewa sun samu tasu, awara.

TRT Afrika