Daga Firmain Eric Mbadinga
Madame Zouléath, mai kimanin shekaru sama da hamsin 'yar asalin Jamhuriyar Benin ce sannan tana da 'ya'ya hudu, kana ba ta taɓa mafarkin cewa wata rana za ta iya mallakar fili a ƙauyensu na Naro ba sai shekaru biyu da suka wuce.
Arzikinta ya samu ne bayan wata tattaunawa da mijinta ya yi da wanda ya kafa wata kungiya mai zaman kanta ta Tonkouro da ke wayar da kan jama’a game da ‘yancin hakkokin mata.
Yanzu da take da fili mai girman kadada 2.5 da sunanta, Zouléath na ganin ta samu tallafi ta kowace hanya. Tana da niyyar ƙirƙirar wata ƙaramar gona, inda za ta noma kayan abinci kamar dangin doya da dankali da dawa domin ita ma ta samu damar ba da gudunmawar kuɗaɗɗen shiga a gidanta.
Zouléath, wacce ƙauyen da ta fito ke yankin arewacin sashen Borgou a Benin, za ta iya zama abar kwatance a ƙauyen duk da cewa kunɗin tsari da doka sun bai wa mata damar mallakar gado ta hanyar haihuwa da aure.
Kundin tsarin mulkin Jamuriyar Benin na 1990 ya ba da tabbacin samar da daidaiton jinsi, ciki har da mallakar fili ga wanne jinsi. Zahirin abin da ya bayyana ya ƙara wayar da kai tare da cire shakkun farin cikin da Zouléath ke ciki.
Wani bincike da kungiyar Women in Law and Development in Africa (WILDAF) reshen Benin ta gudanar a shekarar 2020 ya nuna cewa kasa da kashi 30 cikin 100 na matan kasar ne suka samu ikon mallakar filaye.
Tahiri ya yi nuni da cewa a kasashen Afirka da dama, maza ne suka fi samun damar mallakar filaye duk da cewa galibi mata ne suka fi ayyukan noma, ciki har da aikin gyaran gonaki.
A takaice, samun wannan damar na zama abin damuwa ga kungiyar Tarayyar Afirka AU, wacce ta yi alkawarin yin aiki tukuru don tabbatar da cewa nan da shekarar 2030, akalla kashi 30 cikin 100 na filayen nahiyar mata ne suka mallake su.
A Jamhuriyar Benin, kungiyoyin al'umma daban-daban na taimakawa wajen shawo kan ire-iren koma bayan da al'adu ke janyo wa mata.
Yaƙi da son zuciya
Wadda ta kafa kungiyar Tonkouro Tamou Charaf Yarou mai shekaru 27, ta yi imanin za a iya aiwatar da dokar ne kawai idan an sauya al'amuran zamantakewa na al'adu da gargajiya masu tsauri.
"Mata suna fuskantar matsaloli masu yawa da ke hana su haɓaka amfanin gonakinsu. Wadannan sun hada da samun damar mallakar filaye da kuma tsaro,'' kamar yadda Yarou ya shaida wa TRT Afrika.
''Batun bai wa mata damar mallakar ƙasa ba wai kawai batun shari'a ba ne, har da zamantakewa da al'adu da siyasa," in ji shi.
Yana mai ba da tabbacin cewa tattaunawa mai ma'ana za ta iya kawo sauyi. Yarou ya fara aikin wayar da kan al'umma ne a shekarar 2019 ta hanyar zantawa da jama'a a garuruwa da ƙauyuka.
Ƙungiyar Tonkouro ta samu kanta ne a wannan shekara duk da ƙarancin kudi don ƙaddamar da irin wannan shiri.
“Wata rana, na tambayi ’yan’uwana uku daga Niaro da ke yankin Sinendé dalilin da ya sa suke ƙin barin matansu su mallaki fili da shuka amfanin gona da kansu,” in ji Yarou.
“Sun bayyana min cewa idan suka yi haka, al’umma ba za su mutunta su ba, sai na tambaye su abin da zai faru bayan sun mutu, sai shiru ya cika dakin, a kakar da ta biyo baya kowanne daga cikinsu ya bai wa matansa wani fili. Zan iya cewa wannan yunkuri da na yi ya yi aiki."
Wani masanin zamantakewa da al'adun al'umma a kasar Benin Edith Assangbe na son gwamnati ta ƙarfafa manufa da dokokinta na bai wa mata damar mallakar filaye.
"Tabbas akwai dokar a ƙasa, Sai dai a yankunan karkara, tasirin al'adu na iya hana wasu mata samun damar mallakar filaye. Yawancinsu ba su san hakkokinsu kan mallakar filaye ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Irin wannan lamarin na matukar nuna muhimmancin yin gangamin wayar da kan jama’a kamar irin wanda Yarou ke yi.
Ba da fifiko kan abubuwa masu alaƙa
Bisa ga bayanan Bankin Duniya, noma ya kunshi kusan kashi 25 cikin 100 a ma'aunin tattalin arzikin Afirka GDP, sannan ƙididdigar da ta fi daukar hankali ita ce, yadda mata suke kusan rabin yawan ayyukan da ake.
Idan aka yi la'akari da yanayin tattalin arzikin noma, samun damar mallakar filaye ga mata na iya tasiri ga GDP na yawancin ƙasashen Afirka.
Kungiyar Yarou mai zaman kanta na da burin horar da mata sana’o’in da za su ba su damar shiga ayyukan samar da kudaden shiga kamar kiwo da noma da haɗa man kaɗanya da dai sauransu.
“Ta hanyar bai wa matan ƙarfin gwiwa, za mu iya kawo sauyi ga fannin ilimi baki daya, idan suka samu damar mallakar filaye, wadannan matan za su iya bunƙasa ayyukan gonaki, sannan su samu isassun kuɗaɗɗen da za su dogara da kansu tare da ciyar da iyalansu, da tura ‘ya’yansu makaranta, da taimakawa wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci, da kare ƙasarmu, da halittu, da dai sauransu ” in ji Yarou.
Baya ga bayanai da aka samu daga binciken da Majalisar Dinkin Duniya da cibiyoyi irin su Oxfam da Enabel na Belgium da UNICEF da CARE International suka yi, Yarou na gudanar da nasa binciken domin tsara ayyukansa a wannan fanni.
"Kungiyata ta Tonkouro, wadda ke nufin 'mace' a harshen yarena na Bariba, wata hanya ce ta bayyana manufa ta wajen karfafawa mata," in ji shi.