Mohammed Kassim ya bayyana muhimmancin gaggauta kare bishiyu da tsirrai wadanda su ne jinin rayuwarmu. Photo: TRT World

Daga Muhammad Shakombo

Jelar ruwan Tekun Indiya mai gishiri abu ne da Mohammed ya san shi sosai kamar yunwar cikinsa.

Yana rayuwa a Gazi, wani dan karamin gari a gabar tekun Kenya, tekun ba masamar rayuwa ba ce kawai - na ne wajen wasansa, wajen daukar darasi kuma ma duniyarsa.

Kassim ya dinga rayuwa babu takalmi, yana yawo a kan rairayi mai dumi, yana kama kifaye da namun teku, tare da ci gaba da watayawa a gabar tekun launin shudi mai haske. Amma bayan ya girma, sai ya sauya manufa da ra'ayi game da ruwan da ke Gazi.

Wajen da a baya yake shiru da nutsuwa a yanzu ya zama cibiyar hayaniya. Guguwa mai karfi, wadda bai taba jin ta a lokacin yana yaro ba, a yanzu ta zama abin da aka saba gani yau da gobe.

Kwarran bishiyun 'mangrove', manyan garkuwar da ke hana tekun yin datti, sun fara karewa. Sannan ga wasu ramuka da ke maye gurbin bishiyun na mangrove - ramuka ne da ke dauke da iskar carbon sama da busassun dazukan da ke ban kasa.

Bayan kammala makarantar sakandire, Kassim sai ya kudiri aniya - ya bar yankin Gazi, amma har yanzu yana kewar wajen.

Kassim ya fada wa TRT World cewa "Cibiyar Bincike Kan Teku da Kamun Kifi ta Kenya, fitilar ilimi, ta zama ajina na farko. Akwai kwararrun malaman kimiyya a wajen, a nan na fara tsunduma cikin komar rayuwar nazarin teku."

Kasancewar sa da rashin gamsuwa irin ta kananan yara da ke soan sanin sabbin abubuwa, ya fara sabuwar tafiya a Jami'ar Kenyatta, jami'a ta biyu mafi tsufa a Kenya.

"Bayan shekaru biyar, na kammala digirina a Kimiyyar Teku na san cewa lokaci ya yi da zan koma gida, ba wai a matsyain dan Gazi kawai ba, har ma a matsayin muryar masanan kimiyya," in ji Kassim.

Matar mahaifinsa Rama Salim, mai sayar da kifaye, ta yi kokarin fahimtar me Kassim ke son yi a kimiyyar teku. "Tekun na smaar da yaro," in ji Kazi da ta tuna loakcin da yake cewa, 'me ya sa ake neman ilimi a litattafai bayan a teku ma ana samu dukkan amsoshin?'

Sai dai kuma, karatun da Kassim ya yi a makaranta ba wai zai tafi ba ne a iska ba tare da aiki da shi ba."

Cikowar tafkuna da teku da sauyawar yanayi marar fasali na yin illa ga bishiyun mangrove Hoto: Others

Sauyin yanayi

"Karar kadawar bishiyu da kukan tsuntsaye ne wakokin da suke sanya ni bacci a lokacin ina yaro," in ji Kassim, "sai na samu karin fahimta da haske a tattare da ni. Kimiyya ta zama yaren da na ke fahintar sauyin da aka samu a gidanmu. Kimiyya na bayyana munin suayin yanayi."

"Cikowar tafkuna da teku da sauyawar yanayi marar fasali na yin illa ga bishiyun mangrove, haka ma kifaye, kaguwa da sauran namun teku na fuskantar barazana, jn ji Kazi."

Kassim, wanda wanda ya taba wasanni a gabar tekun, ya bayyana bukatar gaggawar da ake da ita don kare "jinin rayuwar al'ummarmu"

Wannan ne ya sanya shi dawo wa zuwa ga Mangrove din don taimaka wa.

Ya ce "A matsayi na na masanin kimiyyar halittun teku, Sia na samu babban makami - kimiyya. Wani alhaki ne da na runguma nan da nan, na kudiri aniyar kare gadon da ya dinga goya ni yana raino na tare da wasu ma da dama."

Kassim ya fara aiki shekaru biyu da suka gabata inda ya shiga aikin Mikoko Pamoja. Wani aiki na hidimtawa al'umma da ke bayar da tallafin farfado da bishiyun mangrove tare da ba su kariya ta hanyar hada hannayen jama'a waje guda.

Ayyukansu sun hada da bayar da kariya, wayar da kan jama'a, da sayar da katinn iskar carbon na mangrove.

Duk da kyakkyawar niyyar da ake da ita, amma Kassim ya ce shirin ya fuskanci tirjiya.

Dattawa, da suka zurfafa a al'adu, na yi wa mangrove wani irin kallo, suna alaknat su da mayaudara kuma masu hatsari. Rashin kifaye ya dimauta matasa tsawon shekaru, kuma sun rasa fata mai kyau na dasa bishiyu.

Kassim ya ce ya gaza jan hankali da gamsar da wasu jama'arsu game da niyyarsa. ya sha wahalar nuna musu muhimmancin da mangrove ke da shi wajen wanzar da kifaye a ruwa.

"Ku kare mangrove a yau, komar kamun kifinku za ta cika gobe," in ji shi yayin tattaunawa da jama'ar garin.

Amma Kassim ya yi amfani da damar wajen bayyana wasu alfanu a tattaunawar da yake yi.

Mangrove masu lafiya na bayar da kariya ga teku daga gurbata. Suna kare gabar tekunanmu daga guguwa, kuma hakan na nufin suna kare gidajenmu da iyalanmu," in ji Kassim. "Suna jan hankalin maziyarta don ganin kyawunsu, dama ce da yawon bude ido mai kyau da za ta dawo mana da kudaden da muka kashe."

Bayan wani lokaci, dagewa da kiran da masanin halittun tekun ke yi ga jama'a ya fara samun karbu wa. Sai ya samu abokan aiki daga cikin matasa, da ma yara da ke sha'awar aikin bayar d akariya ga tsirrai da tekun, a karshe dai ya saka a ayyukan bayar da kariya.

Kassim na zuwa tare da fuskantar wani irin kallo daga dattawa a duk lokacin da ya bayyana musu bayanai na kimiyya, yana nuna musu cewar al'ada da ci gaba za su iya zama tare a lokaci guda.

Haifaffen kauyen Gazi, wanda ya dawo gida, ya samu kyaututtuka da yabo da dama, ciki har da Mutumin Majalisar Dinkin Duniya na Shekarar 2023.

Da tsakar ranar wani wuni, a yayin da Kassim ke jagorantar tawaga don shuka bishiyun mangrove a waje mai girman hekta 615, sai wani sabon abu ya bullo.

Mohammed Kassim a wajen aiki a Gazi. Hoto: Others

Cigaban Al'umma

A yayin da Aikin Mikoko ke ci gaba, Kassim ya shirya dukkan kayan aikin da ake bukata, a yayin da su kuma jama'a suke bayar da goyon baya.

Mata sun kafa tasu kungiyar ta taimakon kai da kai, an fara shirin tsaftace ruwa. Sayar da katinan iskar carbon, kusan na dala dubu $25,000, ya sanya an farfado da makarantu da ayyukan motsa jiki.

Matasa ma sun samu dabaru da fasahar harkokin yawon bude ido, sun zama masu aikin gyara gabar teku.

Garin gazi da jama'a suke yi wa kallon ya gaba lalacewa, sai ya fara farfafadowa da burunkasa.

Sai dai kuma, ba za a samu sauyi ba tare da samun kalubale ba. Yaki da sauyin yanayi ba abu ne mai sauki ba. Kassim da da jama'arsa na shan wahala sosai wajen saba wa da wannan aiki, suna kirkirar sabbin abubuwa da neman karfin gwiwa ta hanyar hada hannu waje guda da suke yi.

Bayan shekara uku, garin Gazi ya zama abin misalin ayyukan cigaba na al'umma.

Kwarran bishiyun mangrove, wadanda suka taba zama tarihi a wani lokaci, a yanzu su zama wata babbar garkuwa a gabar teku. An fara samun kifaye da dama sakamakon tasftace gabar tekun da aka yi da samar da bishiyu.

Abu mafi muhimmanci shi ne, an dawo da kyakkyawan fata game da mallakar kadarori, hakan na faranta zukata da karfafa gwiwar jama'ar Gazi.

Kassim na kallon girman Tekun Indiya da albarkatun da ke cikinta, a yanzu ya zama ba dan garin gazi kawai ba, ya samu matsayin mai kula d amangrove.

"Rikcin ya yi nisa sosai, amma Gazi tare da mangrove da suka sake tsirowa da kuma jama'ar da suka hada kai waje guda, mun shirya tunkurar makoma."

TRT Afrika