Wannan wani sabon yunkuri ne a kokarin da kasar wadda ke yankin Kudancin Afirka ke yi na yin watsi da sauran alamomin mulkin mallaka a kasar. Hoto: AFP

Daga Takunda Mandura

A makon jiya ne Majalisar Zarwatar kasar Zimbabwe ta amince da bukatar da aka gabatar mata na cire dokokin da tsarin mulkin kasar tun na zamanin mulkin mallaka, wanda ake kira da dokar Fredrick Clayton Trust Act, inda suka bayyana cewa akwai nuna wariya a ciki.

Wannan wani sabon yunkuri ne a kokarin da kasar wadda ke yankin Kudancin Afirka ke yi na yin watsi da sauran alamomin mulkin mallaka a kasar.

Tsohuwar dokar tsarin mulkin kasar Zimbabwe na Frederick Clayton Trust Act (Babi na 17:02) a cike yake da bangarori da suke nuna wariya ga mafiya yawan mutanen kasar, amma yanzu haka ya kama hanyar zama tarihi bayan Majalisar Zartarwar kasar ta amince a yi watsi da shi.

Babban dalilin yunkurin watsar da dokar shi ne majalisar ta aminta cewa dokokin daciki ya bambanta tsakanin yaran Turawa da wadanda ba Turawa ba a komai, ciki har da ranakun bukukuwa na kasar, kamar bukukuwan da aka daina a kasar irin su ‘Ranar Magabata’ da ‘Ranar Kasashe Rainon Birtaniya’.

Ministan Yada Labarai na kasar, Dr Jenfan Muswere, ya bayyana cewa dokar ta yi hannun riga da sashe 56 na Kundin Tsarin Mulkin kasar Zimbabwe na samar daidaito.

“Kowa ya cancanci adalci da daidaito a duk lamuran kasar nan ba tare da bambancin kasa ko launin fata ko kabila ko wajen haihuwa ko jinsi ko yare ko addini da fahimta ko bambancin siyasa ko ra’ayi ko al’ada ko jinsi ko aure ko rashinsa ko samuwar juna biyu ko nakasa ko bambancin arziki ko an haife mutum da aure ne ko kafin aure ba,” kamar yadda sakin layi na 3 na Kundin Tsarin Mulkin kasar ya bayyana.

An tsari dokar ne da nuna wariya

Dokar ta Frederick Clayton Trust Act wadda aka yi a shekarar 1918, tana dauke ne da sunan wanda ya tsara ta.

A lokacin Clayton yana cikin dakarun Column, wadanda Baturen mulkin mallaka Cecil Rhodes da kamfaninsa na British South Africa suka kirkira a shekarar 1890 a kokarinsa kwace wani yanki na Mashonaland, wanda daga bisani ya zama cikin Kudancin Rhodesia.

Masana sun yi kira ga gwamnati da ta yi waje da duk wasu dokoki ‘kuntatawa’ da suke tauye hakkin ’yan kasar. Hoto : AP

Sashe na 13 na dokar ya ce, “Shugabanni za su rika warewa a duk shekara, idan so samu ne a ‘Ranar Magabata’ ko ‘Ranar Kasashe Rainon Birtaniya’ kudi wanda bai wuce Dala 100 akalla sau daya domin yaran Turawa da iyayensu da ke zaune a Salisbury su gudanar da biki a ranar, ko kuma a samo wata hanyar da yaran Turawan da abokansu za su rika shakatawa. Za a rika cire kudin ne daga kudin shiga na rukunin gidajen Hatcliffe.”

Haka kuma dokar ta tanadi tara wasu kudade domin taimakawa magabata na dakarun Column na 1890 da 1893, da wadanda suke biye da su, musamman wadanda suka samu raununa a yakin tsakanin shekarar 1914 zuwa 18.

Tunatarwa mai cike da radadi

Masanin shari’a a Zimbabwe, Farfesa Lovemore Madhuku, ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar ta duba duk doka da ta rage a cikin dokokin da aka yi tun mulkin mallaka da suke cikin dokokin kasar da ba su da wani amfani sai sake fama musu ciwo.

“Gwamnatin ba ta san cewa a dokarmu, ana daina amfani da wata doka ba ce kawai bayan an yi goge ta,” in ji Madhuku a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Shi ma wani lauya, kuma dan siyasa, wanda ya kasance cikin shugaban kwamitin da suka wakilci masu adawa a zaman yi wa Kundin Tsarin Mulkin Zimbabwe garambawul a shekarar 2013, Douglas Mwonzora, ya ce an an so a yi jinkirin yin watsi da dokar ta Frederick Clayton Trust din.

“Muna farin ciki da wannan yunkuri. Frederick Clayton ya so ya tanadi fili domin shakatawar yaran Turawa. Idan ya ce yaran Turawa, yana nufin fararen fata ne, wadanda ba su kunshi Indiyawa da ’yan Asiya da bakaken fata ba. Don haka tun farko, dokar ta nuna wariyar fata,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta share duk wata dokar zamanin mulkin mallaka da ta rage a cikin Kundin Tsarin Mulkin kasar, yana mai cewa a yanzu ba a bukatarsu a Zimbabwe.

“Muna da Dokar Rhodes da sauran iri-irin su da aka sanya wa sunan Turawan mulkin mallaka. Dole a yi musu garambawul domin a cire duk inda suka nuna wariya. Babu dalilin da zai sa mu cigaba da amfani da irin wadannan dokokin.

Muna bukatar ci gaba; an wuce lokacin da ake nuna wariya saboda bambancin launin fata,” inji shi.

Shi ma wani lauya mai fafutikar kare hakkin dan Adam mai suna Christopher Mhike, ya yi kira ga gwamnati da duba duk dokokin da ba a da bukatarsu.

“Wasu dokokin na dindindin ne, wasu kuma na wucin gadi. Matsalar ita ce ana yi wa dokokin garambawul ne ba tare da tsari da shiri mai kyau ba.

"Tsarin da zai nuna yadda gwamnatin take zabar dokokin da take so ta daina amfani da su a duk lokacin da ake garambawul din,” inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Shi ma Mhike ya yi kira ga gwamnati da ta yi waje da duk wasu dokoki ‘kuntatawa’ da suke tauye hakkin ’yan kasar.

“Garambawul din zai fi kyau da tasiri ne da a ce gwamnati ta zabo dokoki wadanda suke ci wa ’yan kasar tuwo a kwarya kamar Dokar Sirri da na kidaya da suke tauye hakkin da ’yanci kamar yadda yake a Kundin Tsarin Mulki.

"Misali a dokar sirrin, an hana fitar da bayanai kamar yadda yake a tsarin yin gwamnati a fili.”

Akwai sauran rina a kaba

A yunkurinta na yin gyare-gyare a Kundin Tsarin Mulkin, an shawarci gwamnatin ta dubi bangarorin da za su taimaka wajen ciyar da kasar gaba tare da inganta rayuwar ’yan kasar.

Masu sharhi sun ce akwai bukatar gwamnati ta share duk wata dokar zamanin mulkin mallaka da ta rage a cikin Kundin Tsarin Mulkin kasar. Hoto: AFP

“Kamata ya yi a cire dokokin da suke hana ci gaban kasar, kuma suke tauye hakkin mutanen Zimbabwe.

"Haka kuma akwai bukatar gwamnatin ta tabbatar an fara amfani da wasu matsaya da cimmawa a taron Kundin Tsarin Mulkin kasar na shekarar 2013. Misali bukatar a kafa Hukumar Karbar Korafe-Korafe mai Zaman Kanta ta Zimbabwe,” kamar yadda Mhike ya bayyana wa TRT Afrika.

Sashe na 21 na Kundin Tsarin Mulkin, wanda kasar Zimbabwe ta amince da shi a shekarar 2023 ya bayyana cewa duk wata doka, ko aiki da ya saba da shi, “ba za a yi amfani da shi ba.”

TRT Afrika