Taron AMVCA na bana shi ne karo na 10 da za a gudanar domin karrama finafinai da ’yan fim. Hoto: AMVCA      

Daga Charles Mgbolu

Masu ruwa da tsaki a harkokin finafinai a Afrika sun fara shirye-shiryen halartar taron karrama gwarazan finafinai da ’yan fim na nahiyar Afirka na 2023, wato taron karrama finafinai na Africa Magic Viewers' Choice na bana wato AMVCA 2024 wanda za a yi a karshen makon nan.

Akwai fifattun wadanda suka shiga gasar domin lashe kyautar a kowane mataki, sannan su kansu masu kallo sun fara tsimayin ganin ranar Asabar din, wato 11 ga Mayu domin ganin gwarazan da za su samu nasara.

Wanda ya fi samun shiga matakai mafi yawa a gasar shi ne forodusa dan Nijeriya, Bose Oshin da fim dinsa mai suna ‘Over the Bridge,’ wanda ya samu shiga matakan karramawar guda 12, ciki har da Gwarzon Mataimakin jarumi, da Babbar Jaruma, daukar fim mafi inganci, da tace fim mafi inganci da sauransu.

Fim din Over the Bridge ne ya fi samun shiga gasar ta bana: Hoto: Bose Oshin/Instagram

Daga shi sai kuma fim din hasashe shi ma na Nijeriya mai suna, ‘Mami Wata’ wanda C.J “Fiery” Obasi ya rubuta, kuma ya ba da umarni, wanda shi ma ya samu shiga gasar a matakai 11.

Haka kuma akwai finafinan ‘Breath of Life’ da ‘Jagun Jagun’ suma daga Nijeriya wadanda duk sun samu shiga a matakai guda goma-goma.

Fim din din ‘A Tribe Called Judah’ na jaruma Funke Akindele wanda ya samar da kudi Naira biliyan 1.4 (($996,831), wanda kuma ya kafa tarihin zama fim din Nollywood na farko da ya samar da sama da Naira biliyan 1 a sinima, shi ma ya samu shiga a matakan Gwarzuwar Jaruma da Gwarzon Mataimakin Jarumi da kuma Gwarzon fim Afirka ta Yamma.

A Gabashin Afirka, fim din 'Where the River Divides' na forodusa Matrid Nyagah daga Kenya da (The Strong One) na forodusa Evelyn Siololo suna fafatawa a matakin Gwarzon fim din Gabashin Afrika.

Fim din A tribe called Judah ne ya fi samar da kudi a shekarar 2023: Photo: Others

Sauran finafinan wannan matakin su ne Wandongwa na forodusa John Kokolo da Nakupenda na forodusa kuma darakta Juma Saada dan Tanzania da Itifaki na darakta Omar Hamza.

Kyaututtukan da za su dauki hankali sosai su ne mataimakan jarumai, saboda yadda masu shirya taron suka sanar da wasu sauye-sauye a matakin.

Masu shirya taron, sun ce ba zabe ba ne zai tabbatar da wadanda suka samu nasara.

Wasu alkalai ne za su zauna, su fitar da wadanda suka lashe gasar, alkalan za su kasance a karkashin jagorancin fitaccen dan fim kuma masani a bangaren, Femi Odugbemi – wanda yana cikin masu kada kuri’a a gasar karrama ’yan fim na Academy of Motion Picture Arts and Sciences Awards (The Oscars) a Amurka.

Wandongwa yana cikin finafinan da ake sa ran za su samu nasara daga Gabashin Afirka. Hoto: Others

“Kasancewar mun kai shekara 10 muna shirya wannan gasar, muna ta kokarin ganin mun sabunta gasar domin ta yadda za ta yi kafada da kafada da takwarorinnta na duniya,” inji shugaban sashen tashar na Afirka ta Yamma, Busola Tejumola.

Bara, taron na AMVCA ya sha suka a kafofin sadarwa bayan sanar da wadanda suka lashe wasu matakan.

Masu sukar sun ce bai kamata ya zama zabe za a rika yi ba wajen fitar da gwarazan jarumai, saboda fitattun jaruman da suke da masoya ne za su rika lashe kyaututtukan, ba wai asalin wanda ya fi taka rawa mai kyau ba.

Za a gudanar da taron na bana ne a otel din Eko Hotels and Suites da ke Jihar Legas, Nijeriya.

TRT World