Faith Patricia Ariokot ta dade tana wayar da kan mutane muhimmancin shuka bishiyoyi. Hoto: Faith Patricia Ariokot      

Ƴar Ugandar mai rajin kare muhalli ta shiga kundin bajinta na duniya na Guinness na kasancewa wadda ta rumgune bishiya mafi daɗewa a duniya.

Matashiyar mai shekara 29 ta kafa tarihin ne a ranar 16 ga Janairun, inda ta rumgune wata bishiya na tsawon awa 16 da dakika 6.

A ranar Juma'a ce Guinness ta tabbatar da bajintar.

"Da ni da bishiyar duk mun shiga kundin bajinta na Guinness. Ina cikin farin ciki. Zai yi kyau kowa ya rika shuka bishiya," inji ta a shafinta na X bayan an tabbatar mata da bajintar.

Yunkuri na uku

Wannan ne karo na uku tana wannan yunkurin na kafa tarihin a tsakanin wata daya, inda na'urar nadar bidiyonta ta samu matsala a yunkurin farko, sannan tsawa ta tilasta mata dakatar da yunkuri na biyu.

"Sai sa kafafuna suka yi tsanu wajen kafa tarihin saboda tsayuwa na sama da awa 16 ba hutawa," in ji ta.

"Jikin bishiyar yana da kaushi, inda ya samu raunuka a hannu, wadanda jawo min radadi sosai, amma duk da haka ban fasa ba."

Faith ta ce tun a awan farko ta so ta yanke kauna. Hoto: Guinness World Record

Faith ta ce shi kan shi zabo bishiyar da za ta rumgune din sai da ya zama tamkar zabo kayan amarya.

"A karshe dai bishiyar ce ta zabe ni, kamar an hada jininmu ne a karon farko da na ganta," in ji ta.

Ta ce ta yi hakan ne, "domin karfafa gwiwar mutane a kan muhimmancin shuka bishiyoyi da kuma wayar da kan mutane a kan muhimmancin ba su kariya."

Ba a kallon nasarar a matsayin famfalaki saboda ba ta haura awa 24 ba.

Don haka, daga cikin sharadin, ba a amince Faith ta huta ba ko kadan-Ba a yarda da cire hannunta daga jikin bishiyar ba, sannan ana so ne ta rumgune bishiyar a tsaye har ta gama.

Tana fata wannan nasarar da ta samu za ta taimaka wajen wayar da kan mutane a kan muhimmancin shuka bishiyoyi.

"Ina magana ne a kan soyayya. Soyayyar duniyar da muke rayuwa a cikin. Soyayyar juna. Ba mu da wata duniyar da ta wuce wannan," in ji ta.

TRT Afrika