Rashin ƙarfin Manchester United ya ƙara bayyana a wasan da kuskuren Andre Onana ya janyo musu ɓarin maki. / Hoto: AFP

Manajan Manchester United, Erik Ten Hag ya roƙi ƙarin haƙuri game da gazawar ƙungiyar na taɓuka komai a kakar Firimiya ta bana, inda a yanzu ta tabbata ba za ta buga gasar Zakarun Turai ta baɗi ba.

Ten Hag ya roƙi masoyan ƙungiyar ne bayan da United ta yi kunnen doki da Burney a makon wasannin na 35 a kakar bana, inda a yanzu Man United take da maki 54, duk da dai ita ya rage mata wasanni 4 ne a gasar.

Kocin ya samu gagarumar suka kan yadda yake riƙe da kulob ɗin tun zuwansa a shekarar 2022. Tuni ake ta raɗe-raɗin za a kori Ten Hag daga Man United a bazarar da ke tafe.

A yanzu dai, ko da United ta samu mafi girman maki, 12 daga wasanni huɗu da suka rage mata, za ta samu jimillar maki 66 ne, ƙasa da Aston Villa mai maki 67 a yanzu, wadda kuma take da sauran wasanni uku a hannunta.

Unite na da damar ƙarkewa a mataki na biyar a teburi, amma fa sai idan Tottenham ta gaza cin maki 7 daga wasanni 6 da suka rage mata.

Wannan ya sa ake ganin ko da gasar Europa ma za ta gagari Man United a baɗ, tun da Tottenham ce ke mataki na biyar ɗin a yanzu da maki 60 daga wasanni 32, kuma tana da damar ƙara maki 18 daga wasanni 6 da suka rage mata.

Sai dai duk da wannan yanayin, Ten Hag yana nuna kyakkyawan fata na ci gaba da kasancewa jagoran United a kaka mai zuwa, inda ya doge kan cewa yana buƙatar lokaci kafin gina tawagar da za ta iya lashe gasar Firimiya.

Da yake jawabi ga tashar ESPN, Ten hag ya ce, "Muna da matasan 'yan wasa masu ƙananan shekaru, kuma da haka ake gina tawaga amma sai an ɗauki lokaci."

Ya ba da misali da 'yan wasa irinsu Alejandro Garnacho, Rasmus Højlund, da Kobbie Mainoo, waɗanda dukansu suke buga kakar wasan Firimiya karon farko a bana. Ya ce 'yan wasan suna buƙatar lokaci kafin su gama gogewa.

Tuni rahotannin kamar daga ESPN suka nuna cewa Ten Hag zai fuskanci zaftarewar kashi 25% na albashinsa, sakamakon gazawar United na samun gurbin buga wasa a gasannin Turai baɗi.

A yanzu, hankali zai koma kan wasan ƙarshe na gasar FA na ranar 25 ga Mayu, inda za a ga ko Man United za ta iya kaucewa maimaita abin da ya faru a bara, inda Manchester City ta doke ta wajen lashe kofin na FA.

TRT Afrika