A Safaniya, Ingila, Italiya, Faransa, Jamus da ma sauran kasashen Turai, taurarin kwallon kafa daga nahiyar Afirka sun haskaka inda suka taka rawar gani a kungiyoyinsu.
RIYAD MAHREZ
Manchester City ce ta lashe kofin gasar Ingila. Dan kasar Aljeriya ya zura kwallaye goma a raga, kuma ya ba da gudunmawa wajen zura kwallaye goma a dukkan wasannin City, don haka babu tantama cewa ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da kulob dinsa ya samu.
Bayan kulob din ya saye shi a shekarar 2018, Riyad Mahrez ya lashe kofin gasar firimiya sau hudu da kuma kofi biyar a Ingila. Ya lashe kofin da tare da Leicester City a shekarar 2016 kafin ya koma City.
VICTOR OSIMHEN
Napoli ta dauki kofin gasar Serie A na Italiya a karo na uku, sama da shekara 30 bayan ta lashe shi sau biyu a lokacin Diego Armando Maradona (1987 zuwa 1990).
Komawa gaba-gaba da kulob din ya yi ba ya rasa nasaba da kwararrun ‘yan wasan da yake da su ciki har da Victor Osimhen, dan wasan Nijeriya.
Osimhen ya shawo kan kalubalen da ke gabansa. Dan wasan da ya iya murza leda ya taimaka wa kulob dinsa, inda ya zura kwallo 31 a raga, ciki har da har da 26 a gasar lig din Serie A – lamarin da ya mayar da shi dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Seria A gaba da Lautaro Martinez wanda ya zura kwallaye 21 a raga.
FRANCK KESSIE
Bayan an cire ta a gasar Zakarun Turai, Barcelona ta samu ta lashe gasar La Liga ta Sfaniya.
Da taimakon madugun Poland, Robert Lewandowski, wanda ya zura kwallaye 34 a raga cikin wasanni 50, kulob din ta yi nasarar daukar kofin lig din Sfaniya a karon farko karkashin Xavi Hernandez.
Franck Kessié, wanda ya koma kulob din daga AC Milan, ba da gagarumar gudunmowa ga nasarar kulob dinsa.
Dan wasan tsakiyar Côte d'Ivoire din ya buga wasa 50 cikin dukkan gasannin, inda ya zura kwallaye uku raga (3) kuma ya ba da gudunmowa wajen zura kwallaye uku a raga.
SADIO MANE
Kofin da Bundesliga da ba a yi tsammanin Bayern Munich za ta lashe ba, kungiyar ta lashe shi ne da taimakon Mane.
Kungiyar tana cikin wani mawuyacin yanayi kafin ta buga wasanta na karshe, sun kasance suna bukatar nasara a birnin Cologne kuma suna fatar abokanan hamayyarsu Dortmund za su fadi.
A gaban gidansu dake Signal Iduna Park, Dortmund na bukatar nasara ne don ta yanke fargabar.
Amma Mainz ta takura wa kungiyar da ta karbi bakuncinta, kuma ta tilasta mata tashi canjaras 2-2. Bayern ta cika aikin a mintunan karshen lokacin wasa kana ta dauki kofin gasar.
A kakarsa ta farko a Jamus, Sadio Mané ya lashe gasar bayan wahalar da ya sha a kakar a karon da ya yi da Leroy Sané, lamarin da ya sa aka dakatar da shi tare da cin tararsa.
Dan wasan da ciwo ya hana wasa na tsawon lokaci har da gasar kwallon duniya, ya zura kwallaye 13 a raga cikin wasanni 39 kuma ba da gudumawa wajen zura kwallaye 7 a raga.
CHOUPO-MOTING DA MAZRAOUI
Wannan kuma shi ne kofin gasar Bundesliga na farko ga Noussair Mazraoui. Bayan ya taho daga Ajax, dan wasan Morokon ya buga wasanni 28 a kakarsa ta farko a Bayern, inda ya zura kwallo daya a raga tare da ba da gudunmowa wajen zura kwallaye hudu a raga.
Duk da cewa bai yi wasanni da yawa ba cikin wannan kakar, dan wasan Senegal, Bouna Sarr (da ya buga wasa tilo) yana cikin masu nasara.
Kazalika dan wasan Kamaru Éric Maxime Choupo-Moting wanda ya taimaka wa kungiyarsa, Bayern Munic, yin nasarar lashe gasar bayan ya zura kwallaye 17 a raga da kuma ba da gudawa wajen zura kwallaye hudu a ragar cikin wasanni 30 a dukkan gasanni.
ACHRAF HAKIMI
PSG ta karasa gasar 2022-2023 da shan kayen 2-3 a gida a hannun Clermont. Amma wannan bai hana Achraf Hakimi nasara ba, domin ya lashe kofin Faransan tare da kulob dinsa.
Wannan ne kofin lig na biyu da dan wasan Morokon ya lashe tun bayan ya koma kulob din a shekarar.
Bayan nasarar da ya samu a gasar kwallon duniya da kasarsa Moroko, dan wasan bayan ya buga wasanni 45, kuma ya zura kwallaye biyar a ragatare da ba da gudumawa wajen zura kwallaye shidda a raga.
Sacha Boey
A gasar Supa Lig din Turkiyya, Galatasaray, ta yi nasarar daukar kofin da gagarumar gudumawar dan Faransa dan Asalin Kamaru Sacha Boey.
Dan wasan bayan mai shekara 22 ya buga wasanni 38 inda ya zura kwallo daya a raga kuma ya ba da gudunmowa wajen zura kwallaye hudu a raga.