TRT tana ci gaba da buɗe ƙarin sassa tare da faɗaɗa hanyoyin bayar da labaranta don dacewa da buƙatun dukkan al'umma. / Hoto: TRT World

Kafar watsa labaran gwamnatin Turkiyya, Turkish Radio and Television Corporation (TRT), ta cika shekara 60 da kafuwa inda ake gudanar da shagulgula a faɗin ƙasar.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya aika da saƙon taya murna ga TRT, inda ya ce ta kwashe waɗannan shekaru ne wajen bayar da labarai na faɗakarwa ga al'umma ba tare da nuna son rai ba.

Shugaba Erdogan ya jinjina wa TRT bisa amfani da hanyoyin fasaha na zamani wajen watsa labaranta, yana mai bayyana jajircewa da ƙarfinta a matsayinta na kafar watsa labarai.

Ya bayyana alfaharinsa ga nasarorin da TRT ta samu a fage watsa labarai, inda ya danganta hakan ga tsarin da aka bi wurin kafa ta da kuma jajirtattun ma'aikatanta.

Da yake bayani game da rawar da TRT ke takawa wajen bautawa al'umma, Erdogan ya nuna cewa abubuwan da take yi suna fayyace matsayin Turkiyya na ƙasa mai al'adu na gari da tarihi da kuma ƙarfinta a duniya.

Shugaba Erdogan ya ce TRT wata cibiyar ilimi ce a fannin watsa labarai, inda take taka rawa wurin samar da 'yan jarida na talbiji da rediyo da intanet sannan tana bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba Turkiyya.

Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa TRT za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da nuna son kai ba da kuma samun ƙarin nasarori a shekaru masu zuwa.

Kazalika Shugaba Erdogan ya taya ma'aikatan TRT murna tare da jinjina musu kan ayyukansu na wayar da kan al'umma.

TRT World