'Yan kasar Turkiyya sun sake fita rumfuna don zaben shugaban kasa bayan a zagaye na farko aka gaza samun dan takarar da ya ci kashi 50 na kuri'un da za su ba shi damar yin nasara ranar 14 ga watan Mayu.
An soma zabe ranar Lahadi da misalin karfe 8 na safe a agogon kasar (0500GMT) kuma za a kammala kada kuri'a da karfe 5 na yamma (1400GMT).
A zagayen farko, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na jam'iyyar People's Alliance, wato Kawancen Al'umma, ya samu kuri'u mafi rinjaye a kujerun majalisar dokoki sannan ya samu kashi 49.52 a zaben shugaban kasa.
Erdogan zai fafata da Kemal Kilicdaroglu, shugaban babbar jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP), kuma dan takarar gamayyar jam'iyyu shida karkashin Nation Alliance, wato Kawancen Kasa.
Fiye da mutum miliyan 60 ne suka yi rajistar zabe, cikinsu har da mutum miliyan 4.9 da za su yi zabe a karon farko.
Akwai akwatun zabe 191,885 a fadin kasar.
1701 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 97.9 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 52.14
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 47.86
1700 GMT - Firaministan Libiya: Nasarar zabe ta nuna farfadowar karfin gwiwar mutane
Firaministan Libiyan Dbeibeh ya taya Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan murnar "nasarar zaben da ya yi", yana mai cewa hakan ya nuna farfadowar kwarin gwiwar mutane kan manyan ayyukan da ya aiwatar da kuma tsare-tsarensa.
1657 GMT - Mataimakin shugaban kasar Turkiyya: 'Kasarmu ta yi nasara'
Mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay ya ce "sabon Karnin Turkiyya ya fara."
Ya ce: "Kasarmu ta yi nasara, kasarmu ta yi nasara, kuma Turkiyya mai karfi ta yi nasara."
1651 GMT — Firaministan Hungary ya taya Erdogan murna
Firaminstan Hungary Viktor Orban ma ya taya Shugaban Kasar Turkiyya murna kan nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben."
1649 GMT — Sarkin Qatar ya taya shugaban kasar Turkiyya murna
Sarkin Qatar ya taya Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan murna bisa nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben inda zai yi ta-zarce.
1646 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 97.1 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 52.21
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 47.79
1630 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 94.1 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 52.43
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 47.57
1620 GMT- An yi zabe cikin lumana: Jami'in Jam'iyyar AK
Mai magana da yawun jam'iyyar AK Omer Celik ya ce an gudanar da zabe a yanayi mai cike da tsaro.
Ya ce jam'iyyar adawa ta CHP ta yi ta kokarin gabatar da nata bayanan da take ikirarin su ne na gaskiya.
"Za mu girmama sakamakon zabe na karshe na abin da 'yan kasa suka zaba," ya fada a yayin da yake yi wa manema labarai jawabi.
1615 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 89.8 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 52.72
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 47.28
1600 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 85.4 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 53.15
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 46.85
1556 GMT — YSK: Babu matsala a tattara bayanai
Shugaba Hukumar Koli ta Zabe (YSK), Ahmet Yener, ya ce babu wata matsala a harkar shigowar bayanai sannan ana rarraba bayanan ga jam'iyyun siyasa.
Da yake jaddada yadda wakilan jam'iyyun ke bin diddigin yadda bayanan ke shigowa a cibiyar YSK, Yener ya ce "Mun bukaci al'umma da 'yan kasa su jira sakamako har sai an sanar da shi. Babu wata matsala a yadda bayanan ke shigowa, ana bai wa jam'iyyun siyasarmu."
1550 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 79.1 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 53.70
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 46.30
1545 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 71.4 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 54.37
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 45.63
1525 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 55.1 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 55.80
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 44.20
1515 GMT — Sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan ya nuna an kirga kashi 35.8 cikin 100 na jumullar kuri'un
• Erdogan: Ya samu kashi 58.00
• Kilicdaroglu: Ya samu kashi 42.00
1512 GMT — An dage hanin da aka yi na sanar da sakamakon zabe a kafafen watsa labarai
An dage hanin da aka yi na sanar da sakamakon zabe a kafafen watsa labarai da hukumar koli kan zabe ta kasar ta sanya.
Hukumar Koli ta Zabe (YSK) ta dage hanin da ta sanya din ne da misalin karfe 6.15 na yamma agogon kasar (1515GMT), kamar yadda shugaban hukumar Ahmet Yener ya shaida wa manema labarai a babban birnin kasar Ankara.
1415 GMT — Ba a samu rahoton faruwar wani abu mara kyau ba
Shugaban Hukumar Koli ta Zaben Turkiyya Ahmet Yener ya ce ba a samu rahoton faruwar wani abu marar kyau ba a yayin kada kuri'a.
Da yake wa manema labarai jawabi bayan rufe rumfunan zabe, Yener ya ce hukumomin da suke dace sun karbi ragamar komai sannna ya gode wa duk wadanda suka taimaka wajen gudanar da zaben cikin lumana.
1414 GMT — Erdogan ya yi kira ga a kare akwatunan zabe
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga jami'an zabe da su kare dukkan akwatunan zabe har sai an kammala tantance sakamako.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Erdogan ya gode wa dukkan abokan aikinsa da suka sadaukar da lokacinsu wajen aiki a rumfunan zabe tun da sanyin safiyar yau.
"Ina kira ga dukkan 'yan uwana da su mike tsaye don kare akwatunan zabe har sai an kammala tantance sakamako. Yanzu lokaci nena kare bukatar kasarmu har sai an kammala komai," in ji Erdogan.
1400 GMT — An kammala kada kuri'a
An kammala kada kuri'a a fadin Turkiyya a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
An bude rumfunan zabe ne da karfe 0800 na safe agogon kasar (0500GMT) aka kuma rufe su da karfe 5 na yamma (1400GMT).
1008 GMT — Marasa lafiya da masu bukata ta musamman na kada kuri'unsu daga gida a zaben Turkiyya
Jami'ai na hukumar zabe na larduna a Turkiyya sun yi ta zagaya wa da akwatunan zabe na tafi da gidanka zuwa gidajen 'yan kasa da ba za su iya fita zabe ba saboda dalilan rashin lafiya ko lalurar nakasa.
A lardin Adiyamna da ke kudu maso gabashin Turkiyya, jami'ai sun kai akwatin zabe na tafi da goidanka gidan su wata yarinya Sumeyye Sahin mai shekara 18. An sanar da ita yadda tsarin kada kuri'ar yake. Da take magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Sahin ta gode wa jami'an da suka je har gida don ba ta damar yin zaben tare da yi wa kasarta fatan alheri.
An samar da akwatin zaben tafi da gidan naka ne don bai wa mutanen da rashin lafiya ta kwantar da su damar kada kuri'a.
0940 GMT - Ana sa ran fitar da sakamakon zabe da wuri
Wakilin TRT World Mustafa Fatih Yavuz, wanda ke aiko da rahotanni daga Ankara, ya ambato majalisar koli ta zaben Turkiyya na cea ana sa ran fitar da sakamakon zaben da wuri.
"Mutanen da ke sanya ido kan zaben sun ce ana sa rai kuri'un da za su lalace ba za su kasance masu yawa ba saboda takardun zaben wannan karon ba su da wahalar ganewa idan aka kwatanta da na zaben ranar 14 ga watan Mayu inda ake da jam'iyyu 24 na zaben majalisar dokoki da jam'iyyu hudu na zaben shugaban kasar," a cewar Yavuz.
0910 GMT - Erdogan da Kilicdaroglu sun kada kuri'unsu
Shugaba Erdogan, tare da rakiyar mai dakinsa, sun isa Makarantar Uskudar Saffet Celebi Middle School da ke Istanbul domin kada kuri'arsa.
A yayin da ya shiga wurin zaben na Uskudar, uunguwar da shugaban kasar Turkiyya yake zama, dandazon jama'a ya yi masa jinjina.
Shi ma jagoran jam'iyyun hamayya Kemal Kilicdaroglu ya kada kuri'arsa a Ankara, babban birnin Turkiyya.
0750 GMT - Ruwan kuri’un da mutanen Hatay ke wa Kawance Al'umma
Rahul Radhakrishnan, wanda ke bayar da rahoto daga kudancin lardin Hatay ya ce jam’iyyar People’s Alliance ta samu goyon baya mai karfi a lokacin zaben ‘yan majalisa. Amma a zaben shugaban kasa, Kilicdaroglu ya samu tazara kadan na kuri’u daga mutanen Hatay”.
“Shugaba Erdogan a yayin wani jawabi a farkon makon nan ya ce yana mutunta kuri’un ‘yan kasarsa kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin rike alkawari domin gina wannan birnin da kuma bayar da taimako ga wadanda suka fi bukata,” in ji Radhakrishnan.
0730 GMT - Sauyi ga yakin neman zaben Kemal Kilicdaroglu
Hotunan dan takarar shugaban kasa daga bangaren adawa Kemal Kilicdaroglu's sun karade titunan Santambul dauke da sakon, “’Yan Syria za su koma,” wanda wata alama ce ta mayar da miliyoyin ‘yan gudun hijirar Syria.
Ravza Kavakcı Kan, wanda mai sharhi ne kan siyasa ya shaida wa TRT World cewa a makonnin da suka gabata, an samu sauyi matuka dangane da yadda Kilicdaroglu ke daukar kansa.
“Da farko yana da kirki kuma yana abubuwa daida. Amma ana kammala zagaye na farko, sai muka soma jin kalamai masu karfi na kiyayya da suka shafi baki da kuma ‘yan gudun hijira.
"An samu sauyi matuka dangane da yadda Kilicdaroglu ya soma bayyana kansa kafin zagayen farko," in ji shi.
0510 GMT – ‘Yan Turkiyya sun soma jefa kuri’a
An soma zabe yanzu haka a Turkiyya kuma za a kamma shi da misalin karfe 5:00 agogon kasar (1400GMT).
0500 GMT - An soma jefa kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Turkiyya
An soma kada kuri'a a dukkan fadin Turkiyya a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
A zaben da aka yi ranar 14 ga watan Mayu, 'yan Turkiyya mazauna kasashen waje kimanin miliyan 1.84 ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.