Duk da matsalolin da ake fuskanta ta fuskar zuba jari a Turai, amma duk da haka Turkiyya ta zama wata cibiya wadda take jawo hankali nmasu zuba jari a nahiyar. / Hoto: AA

Turkiyya ta zama ta huɗu a nahiyar Turai ta ɓangaren jawo masu zuba jari cikin ƙasar daga sauran ƙasashen waje, kamar yadda ofishin zuba jari na ƙasar ya sanar.

“Turkiyya ta zama muhimmin wuri ga masu zuba jari sakamakon wurin da ƙasar take da kuma damar da ke da akwai mai ƙarfi ta zuba jari. Dala biliyan 10.6 da muka samu kai tsaye ta hanyar zuba jari daga ƙasashen waje a 2023 ita ce babbar alamar wannan nasara,” in ji Burak Daglioglu, shugaban ofishin.

Ya nanata cewa, Turkiyya ta ci gaba da bunkasar da take yi wajen jawo masu zuba hannun jari kai tsaye a cikin Turai bayan annobar korona.

Kamar yadda Daglioglu ya bayyana, wani rahoto da wani kamfanin bincike da tuntuɓa na EY ya yi ya gano cewa an samu raguwa a shekarar da ta gabata ta ɓangaren zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje zuwa cikin Turai a karon farko tun bayan korona.

An samu ayyuka 5,694 ta hanyar zuba jari a 2023 a Turai, inda ya ragu da kaso huɗu cikin 100 daga shekarar da ta gabata sakamakon matsaloli waɗanda suka haɗa da hauhawar farashi da ƙruwar farashin makamashi da sauransu.

Daglioglu ya ƙara da cewa Faransa ce a gaba wajen samun akasarin masu zuba jarin a bara sai dai ta samu raguwa da kaso biyar cikin 100 a 2022.

Birtaniya ce ta biyu sai dai ita ta samu ƙaruwa ne da kaso shida cikin 100.

Jamus ce ta uku inda ta samu raguwa matuƙa da kaso 12 cikin 100.

Turkiyya ce ta bakwai a ƙasashen Turai a 2020 inda ta dawo ta biyar a 2022. A halin yanzu ƙasar ta zama ta huɗu a cikin ƙasashe 10 mafi girma ta ɓangaren zuba jari.

Turkiyya ta samu ƙaruwa da kaso 17 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata ta 2023.

TRT World