Zaben Turkiyya: Mata sun samu  adadi mafi yawa na kujerun majalisar dokoki

Zaben Turkiyya: Mata sun samu  adadi mafi yawa na kujerun majalisar dokoki

Mata 121 ne suka yi nasarar samun kujeru a majalisar dokokin kasar mai wakilai 600.
Hoton dakin majalisar dokokin Turkiya / Hoto: Getty Images

Wakilcin mata a majalisar dokokin Turkiyya zai kasance adadi mafi yawa da aka taba samu a tarihin kasar, bayan zaben 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa aka gudanar na kasar a ranar Lahadi.

Wani sakamako da aka fitar, wanda ba a hukumance ba, ya nuna cewa mata 121 ne suka yi nasara a zaben majalisar dokokin kasar mai wakilai 600.

A zabukan da suka gabata, adadin wakilcin mata a majalisar ya kai kashi 17.1, a bana kuma adadin ya haura zuwa kashi 20.1.

Jam'iyyar Green Left ce ke kan gaba da mafi yawan wakilcin mata 30 daga cikin 61 na 'yan majalisun dokoki da aka samu.

Hakan ya biyo bayan yawan adadin da jam’iyyar AK da Jam’iyyar CHP da Jam’iyyar IYI da da kuma MHP suka samu.

Jam'iyyar Justice and Development Party, AK ke biye mata, sai kuma jam'iyyun Republican People's Party (CHP), IYI Party da kuma Nationalist Movement Party (MHP).

Jimilla jam'iyyar AK ta samu mata 'yan majalisa 50, CHP da Green Left Party sun samu 30, IYI Party ta samu shida, MHP ta samu hudu yayin da Turkish Workers' Party ta samu daya.

'Yan majalisar biyu da aka samu a bana wadanda suka fi karancin shekaru mata ne, Zehranur Aydemir yar shekaru 25 wace ita ce mataimakiyar shugaban jam'iyyar AK a Ankara sai kuma Rumeysa Kadak mai shekaru 27 da kasance mataimakiyar shugaban jam’iyyar AK a Istanbul.

Miliyoyin masu kada kuri'a yan Turkiyya ne suka fita rumfunan zabe a ranar Lahadi don zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin kasar.

Wakilcin mata a Majalisar Dokokin Turkiyya/ Hoto: TRT World

An kai ga karshen zaben zagaye na farko ba tare da wani dan takara ya iya samun kashi 50% na kuri'un da ake bukata ba, sai dai ana iya cewa Shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan ne ke kan gaba, in ji Ahmet Yener, shugaban kwamitin koli na zaben, yana mai nuni da sakamakon da ba a fitar ba a hukumance.

Adadin da aka samu na wadanda suka kada kuri'a a zaben na ranar Lahadi ya kai kashi 88.92, yayin da 'yan Turkiyya da ke kasashen waje suka ba da kashi 52.69%, in ji Yener.

Jam’iyyar kawance ta Erdogan ta samu rinjaye a majalisar dokokin kasar, yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Mayu.

TRT World