Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya sake samun nasarar zama shugaban kasa na 13 ya bayyana manufar kasarsa ta “dabbaka zaman lafiya a duniya baki daya”.
A yayin wani taro da aka gudanar a Ankara Babban Birnin Turkiyya, Erdogan ya bayyana wa jami’an Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Hada-Hadar Hannayen Jari na Turkiyya cewa “Manufarmu ita ce dabbaka zaman lafiya da kwanciyar hankali tun daga Turai zuwa Bahar Maliya, daga Caucasia da Gabas ta Tsakiya zuwa Arewacin Afirka”.
Shugaba Erdogan ya kuma yi alkawarin za su warware matsalar Turkiyya da bizar Tarayyar Turai “Wanda a baya an yi amfani da hakan don bata suna”.
Shugaban da aka sake zaba ya kuma yi fatan gina “Karnin Turkiyya” tare da kasuwancin duniya da kungiyoyin farar hula da cibiyoyin siyasa, a lokacin da Turkiyyan ke shirin bikin cika shekara 100 da kafa Jumhuriya a ranar 29 ga Oktoba.
Erdogan ya kara da cewa sake gina yankunan da girgizar kasa ta shafa da habaka tattalin arzikin Turkiyya ne abu mafi muhimmanci da ke gabansu.
Wadanda suka yi nasarar zaben
“Dikumradiyya da al’ummar Turkiyya ne suka yi nasarar zaben da aka yi,” in shugaban kasar.
A ranar 28 ga Mayu ne aka gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Turkiyya bayan da babu dan takarar da ya samu sama da kashi 50 a zagayen farko da aka yi a ranar 14 ga Mayu.
Shugaba Erdogan ya lashe zaben da kashi 52.14 inda dan takarar adawa Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.86 na kuri’un da aka jefa, kamar yadda Hukumar Zabe ta Koli ta bayyana.
Erdogan ya ce “Duk dan kasar da ya amince da abin da kasa ke so, yake burin kasarmu ta ci gaba, kuma yake jin shi dan kasar nan ne, to shi ne ya yi nasarar wannan zabe.”
Shugaba Erdogan ya kara da cewa Turkiyya ta yi nasarar gudanar da zabe mai muhimmanci a tarihinta.