Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutum 34,622 aka kashe a yankin Falasdinawa a kusan watanni bakwai da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hamas. / Photo: Reuters / Photo: AA / Photo: AP

1412 GMT — Da gayya Netanyahu ya fitar da sanarwa kan tsagaita wuta don kawo cikas — Hamas

Wani babban jami'in kungiyar Hamas ya zargi Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da yin wasu kalamai da ya yi da gayya don murkushe masu fatan sulhu a yakin da aka kwashe kusan watanni bakwai ana gwabzawa a Gaza.

Hossam Badran ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa Hamas na cikin shirin gudanar da tattaunawar cikin gida a tsakanin shugabanninta da kuma kungiyoyin 'yan mayaƙan sa kai kafin masu shiga tsakani su koma birnin Alkahira domin ci gaba da shawarwarin sulhu.

Sai dai ya yi gargadin cewa furucin da Netanyahu ya yi ta nanatawa na cewa zai tura dakaru zuwa birnin Rafah mai nisa a kudancin yankin, an yi ne da nufin "daƙile duk wata yiwuwar ƙulla yarjejeniya".

“Netanyahu ya kasance mai kawo cikas a duk tattaunawar da aka yi a baya, kuma a bayyane yake cewa har yanzu yana nan,” in ji shi a wata tattaunawa ta wayar tarho.

"Ba shi da sha'awar cimma matsaya, don haka yake faɗin kalmomi a kafafen yada labarai domin daƙile wannan kokarin da ake yi a yanzu."

1214 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya haura 34,600 yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare

Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutum 34,622 aka kashe a yankin Falasdinawa a kusan watanni bakwai da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hamas.

Kididdigar ta hada da mutuwar akalla mutum 26 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sanarwar ma'aikatar, ta kuma kara da cewa mutane 77,867 ne suka jikkata a Gaza tun bayan yakin da ake yi tsakanin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra'ila.

0929 GMT Hamas ta yaba wa Turkiyya kan dakatar da kasuwanci tsakaninta da Isra'ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yaba da matakin da Turkiyya ta dauka na dakatar da kasuwanci da Isra'ila tare da la'akari da hakan a matsayin "nasara ga al'ummar Falasdinu."

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce "Muna matukar mutunta matakin da jamhuriyar Turkiyya ta dauka a baya-bayan nan a matsayin nasara ga al'ummar Falasdinawan da ake yi wa kisan kiyashi.

Ƙungiyar ta yaba da dakatar da kasuwanci da Isra'ila da kuma shawarar da Turkiyya ta yi na shiga cikin karar da Afirka ta Kudu ta shigar a kan Tel Aviv a gaban Kotun Duniya (ICJ).

1040 GMT — Kai hari Rafah na iya haifar da 'yi wa fararen hula kisan kiyashi' - MDD

Masu makoki na jimami a gaban gawarwakin ƴan'uwansu Falasdinawa da aka kashe a wani harin da Isra'ila ta kai a Rafah da ke kudancin zirin Gaza. / Photo: Reuters

Harin da sojojin Isra'ila suke kaiwa Rafah zai jefa rayuwar dubban Falasdinawa cikin hadari kuma zai zama babbar illa ga ayyukan jinƙai a yankin baki daya, in ji ofishin jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya.

Isra'ila ta yi gargadin kai farmaki kan kungiyar Hamas a kudancin birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda kimanin mutum miliyan daya da suka rasa matsugunansu suke cunkushe suna samun mafaka ta wucin gadi, bayan da Isra'ila ta kwashe watanni tana kai hare-hare.

Mai magana da yawun ofishin jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya Jens Laerke a wani taron manema labarai na Geneva ya ce "Zai iya zama kisan gilla na fararen hula da kuma zama tarnaƙi ga ayyukan jinƙai a yankin baki daya."

0912 GMT — Isra'ila ta jinkirta kaɗa ƙuri'a kan rufe gidan talabijin na Aljazeera

Majalisar ministocin Isra'ila ta ɗage kaɗa ƙuri'a kan matakin dakatar da gidan talabijin na Aljazeera a kasar har zuwa ranar Lahadi mai zuwa, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito.

Shafin intanet na Walla na Isra'ila ya bayyana cewa, majalisar ministocin kasar ba ta kaɗa ƙuri'a a taron da ta yi da yammacin ranar Alhamis kan matakin rufe tashar Aljazeera a Isra'ila.

"Majalisar zartaswar, wacce ta gana da yammacin ranar Alhamis, ya kamata ta kada kuri'a kan shawarar da Firaiminista Benjamin Netanyahu da Ministan Sadarwa Shlomo Karhi suka yanke na haramta ayyukan Al Jazeera a Isra'ila, amma a minti na karshe, an dage zaben," in ji shafin intanet din.

0936 GMT — Hamas ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki kan harin da Isra'ila ke kai wa 'yan jarida

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu Hamas ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki don "hana" cin zarafin da Isra'ila ke yi kan 'yan jaridar Falasdinu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya, Hamas ta ce: "Muna kira da a dauki matakin yin Allah wadai da fallasa da kuma aikata laifukan keta hakkin mamaya, da kuma kare 'yan jaridu a Falasdinawa da kwararrun kafafen yada labarai daga zalunci da ta'addanci na mamayar (Isra'ila).

Kungiyar Falasdinu ta tabbatar da cewa "lafukan da Isra'ila ke yi wa 'yan jarida ba za su boye gaskiyar ta'addanci da cin zarafi ba".

Hamas ta jaddada cewa Isra'ila ta "kasa ɓata Falasdinawa a idon ƙsashen Larabawa da na Musulmai da ma na sauran ƙasashen duniya".

Aƙalla ‘yan jarida 141 ne suka mutu, wasu fiye da 70 kuma suka sami raunuka sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka yi musu, baya ga kama wasu da dama a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, in ji ofishin yada labaran gwamnatin da ke Gaza.

TRT Afrika da abokan hulda