Hamas ta ce ta amince da shawarar tsagaita wuta a Gaza wacce Masar da Qatar suka bayar. : Reuters / Photo: AFP

1644 GMT — Hamas ta amince da shawarar Qatar da Masar ta tsagaita wuta a Gaza na — Haniya

Hamas ta ce ta amince da shawarar tsagaita wuta a Gaza wacce Masar da Qatar suka bayar.

Ƙungiyar gwagwarmayar a wata sanarwa ta ce, shugabanta Ismail Haniya ya sanar da firaministan Qatar da shugaban leƙen asirin Masar kan amincewarsa a kan shirin.

Zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan abin da sanarwar ta ƙunsa.

1518 GMT — Sanatocin Republican sun yi wa mai gabatar da ƙara na ICC barazana kan sammacin kama Netanyahu: Zeteo

Wasu jiga-jigan 'yan majalisar dattawan jam'iyyar Republican sun aike da wata wasika zuwa Karim Khan, babban mai shigar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC), da ke nuna gargadinsa game da bayar da sammacin kama Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da wasu jami'an Isra'ila.

Wasikar, wacce Zeteo ya samu kuma Sanatocin GOP 12 suka sanya wa hannu, ta gargadi Khan game da yuwuwar "fuskantar takunkumai masu tsanani" idan aka tabbatar da irin wannan sammacin.

Ta ce duk wani mataki da kotun ICC za ta dauka kan Netanyahu da mukarrabansa dangane da abin da suke yi a Gaza ba za a kalle shi a matsayin barazana ga ƴancin Isra'ila ba kawai ba har ma da na Amurka.

1224 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya zarce 34,700 yayin da Isra'ila ta fara kai farmaki Rafah

Akalla Falasdinawa 34,735 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza tun a watan Oktoban bara, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu mutum 78,108 kuma sun jikkata a yaƙin.

Sanarwar ta ce "Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 52 tare da jikkata wasu 90 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata."

Ya kara da cewa "har yanzu mutane da dama na maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu ɗauki."

0754 GMT — Kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah na iya jawo mummunar ta'azzarar rikicin — Hamas

Falasɗinawa na jimamin mutuwar ƴan'uwansu da aka kashe a wani hari da Isra'ila ta kai Rafah.

Babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kwashe mutane da Isra'ila ke yi daga Rafah gabanin hare-haren da ake sa ran za ta ƙaddamar wani "mummunan lamari ne da ka iya ta'azzara yaƙin da ake yi, kuma zai jawo ɗumbin matsaloli."

Kazalika jami'an Hamas sun yi ikirarin cewa matakin kwashe Falasdinawa daga Rafah zai jawo tsaiko wajen sasantarwar sakin mutanen da ake garkuwa da su.

Sojojin Isra'ila sun fara kwashe mutane da ga yankunan da ke kusa da kan iyakar gabashin Rafah, gabain wani farmaki ta ƙasa da ake sa ran za a kai a birnin Falasɗinun da ke kudancin Gaza a yau.

Duk da ƙaruwar adawa da yake fuskanta daga ƙasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin kai farmaki Rafah, yankin da ke ɗauke da Falasɗinawa fiye da miliyan 1.4 da ke neman mafaka a wajen.

0615 GMT — Hezbollah ta Labanon ta ce ta harba gomman rokoki a wani sansanin sojon Isra'ila

Ƙungiyar Hezbollah ta Labanon da ke samun goyon bayan Iran ta ce ta harba gomman makaman rokokin Katyusha a wani sansanin sojin Isra'ila da ke Tuudan Golan da aka mamaye, a wani martani ga wani hari da Isra'ilan ta kai gabashin Labanon.

Mayaƙan Hezbollah sun ƙaddamar da "gomman hare-haren makaman rokoki na Katyusha" da nufin samun hedikwatar sansanin soji da ke Tuddan Golan," kamar yadda ƙungiyar ta faɗa a wata sanarwa, tana mai cewa "harin martanin ne kan harin da maƙiya suka kai yankin Bekaa."

TRT Afrika