Isra'ila ta kashe akalla mutane biyar bayan da ta kai hari a Rafah. / Hoto: AP / Photo: Reuters / Photo: AFP

1703 GMT — Isra'ila za ta zafafa kai hare-hare a Gaza idan tattaunawar Alkahira ta gaza — Gallant

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce Tel Aviv a shirye take ta "zafafa" hare-haren da take kaiwa Gaza idan aka gaza cimma nasarar amincewa da sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a yankin Falasdinu, a tattaunawar sulhu da ake yi a Masar.

Gallant ya ce Isra'ila ta shirya tsaf domin ganin ta kuɓutar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, in ji Gallant bayan da ya zagaya yankin Rafah biyo bayan kutsen da Isra'ila ta yi a kan iyakar Rafah da ke kudancin yankin.

Amma "idan aka cire wannan batun a tattaunawar, to mu ci gaba da zafafa hare-haren," in ji shi a cikin wata sanarwa.

Kalaman Gallant na zuwa ne bayan da masu shiga tsakani na Isra'ila suka isa birnin Alkahira domin yin wani yunƙuri na baya-bayan nan na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila ta kwashe watanni bakwai tana yi a Gaza.

1248 GMT — Amurka ta bayyana wa Isra'ila ra'ayinta kan mamayar Rafah —Ma'aikatar Harkokin Waje

Amurka ta bayyana ra'ayoyinta ga Isra'ila kan wani gagarumin farmaki ta ƙasa da ta kai a Rafah, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a martanin farko da Washington ta mayar tun bayan da sojojin Isra'ila suka ƙwace iko da kan iyakar da Gaza.

"Muna ci gaba da yin amanna cewa yarjejeniyar sakin mutanen da ake garkuwa da su zat amfani duka al'ummomin Isra'ila da Falasdinu; hakan zai kawo tsagaitawuta cikin gaggawa tare da ba da damar kara kai agajin jinƙai a Gaza," in ji kakakin a cikin sakon imel.

0759 GMT — China ta yi kira ga Isra'ila ta daina kai hari Rafah

China a ranar Talata ta bukaci Isra'ila da ta daina kai hare-hare a Rafah, bayan da sojojin Isra'ila suka ce sun ƙwace iko da ɓangaren Falasdinawa na kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Jian, ya ce "China... na kira da babbar murya ga Isra'ila da ta yi biyayya ga dumbin bukatun kasashen duniya, ta daina kai hari a Rafah, da kuma yin duk abin da za ta iya don kauce wa mummunan bala'in jinƙai a Zirin Gaza."

2248 GMT — Tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga kudancin birnin Rafah na Gaza — Rahoto

Tankokin yakin Isra'ila sun shiga birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kai kusan mita 200 daga tsallaken Masar, kamar yadda wani jami'in tsaron Falasdinu da wani jami'in Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Jami'in na Masar ya ce da alama "aikin" yana da iyaka. Shi da tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Hamas sun ce jami'an Isra'ila sun sanar da Misirawan cewa dakarunsu za su janye bayan kammala aikin.

Jami'in na Masar da ke yankin Rafah na kasar Masar da kuma jami'in tsaron Falasdinawa sun yi magana ne da manema labarai.

Tun da farko a ranar Litinin, Majalisar Ministocin Yakin Isra'ila ta yanke shawarar ci gaba da kai farmakin soji a Rafah, bayan da kungiyar Hamas ta sanar da amincewa da shawarar Masar da Qatar na cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

2300 GMT — Turkiyya na fatan Isra'ila ta ɗauki irin matakin Hamas na amincewa da tsagaita wuta

Turkiyya ta yi marhabin da shawarar tsagaita wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta sanar da cewa ta amince da ita, inda ta kara da cewa tana sa ran Isra'ila ta ɗauki irin wannan mataki, in ji Shugaba Recep Erdogan.

"Muna maraba da sanarwar Hamas cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tare da kokarinmu, kuma ya kamata Isra'ila ta dauki matakin da ya kamata," in ji Recep Tayyip Erdogan a ranar Litinin bayan taron majalisar ministocin.

Erdogan ya kuma bukaci "masu ruwa da tsaki na Yammacin Duniya" da su matsa wa gwamnatin Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Turkiyya ta sha matsa ƙaimi kan tsagaita a Gaza tun farkon rikicin watanni bakwai da suka gabata, kuma ta yi kira ga dukkan kasashen duniya da su taimaka wajen ganin an cimma matsaya.

2238 GMT — Isra'ila ta kashe akalla mutane biyar a harin Rafah

Isra'ila ta kashe akalla mutane biyar bayan da ta kai hari a Rafah, in ji wani asibiti a yankin, yayin da Isra'ila ta sha alwashin kaddamar da wani gagarumin farmaki a can.

Asibitin Kuwaiti na birnin ya ce ya karbi "Shahidai biyar da waɗanda suka jikkata da dama" bayan harin da Isra'ila ta kai.

A halin yanzu yankin ya kasance wurin da sojojin Isra'ila ke kai hare-hare kamar yadda shaidu da majiyoyin tsaron Falasdinawan suka bayyana.

TRT Afrika da abokan hulda