A kowace rana adadin Mutum 111 ke mutuwa ta sakamokon harbin bindiga /Photo (AFP)

Cikin wani bincike da wata kungiyar tattara bayanai kan hare-haren bindiga da ake kaiwa a Amurka ta fitar, ta ce a watan Maris kadai fiye da mutum 10,000 ne suka mutu a kasar sakamakon harbe-harben bindiga.

A kowace rana a kan samu adadin Mutum 111 da ke mutuwa ta dalilin harbin bindiga.

A cewar kungiyar, a shekarar 2023 kadai an samu harbe-harbe sama da 130.

Binciken ya kuma kara da cewa ‘’tun a farkon shekarar nan adadin mutanen da suka harbe kansu har lahira ya haura mutum 5,742 yayin da mutane 4,266 suka mutu ta hanyar kisan killa da kuma amfani da bindiga ta hanyar da ba ta dace ba.

Mutum 7,564 kuwa sun ji munana raunuka ta hanyar harbi. An kuma rasa yara 59 wadanda shekarunsu ke kasa da shekara daya zuwa 11 a irin wannan harin, sannan an rasa yara 347 ‘yan shekara 12 zuwa 17.

A ranar Litinin, labarin harin da aka kai wata makaranta a Nashville ya karade kafafen yada labarai na jihar Tennessee inda aka kashe yara uku da manya uku a wata makaranta yara kanana ta addinin kirista.

Tuni dai hukumomi a jihar suka bayyana cewa an harbe 'yar bindigar da ta kai harin mai suna Audrey Hale mai shekara 28 da haihuwa, a yayin artabun da 'yan sanda biyar suka yi da ita.

An harbe Hale wacce ta kasance tsohuwar daliba a makaranta ne a hawan bene na biyu na makarantar da ke hade da majami’ar.

A ranar Talata Shaugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa dole Mujami’ar ta dauki mataki, ‘’Na yi iyakacin abin da ya kamata na yi a matsayina na mai rike da iko na zartarwa game da batun bindigogi.

‘’Mafi yawan Amurkawa na ganin samun damar mallakar makamai abu ne da hankali ba zai dauka ba. Don haka bas u yarda da hakan ba.’’ In ji Biden

Jami’an 'yan sanadan Nashvillena sun ce suna aikin tabbatar da cewa dalilan da suka ingiza 'yar bindigar kai wannan hari.

TRT World