Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gudanar da taron manema labarai da ya saba yi na shekara-shekara a Moscow/ Hoto: Reuters

Vladimir Putin na fara zango na biyar a kan mulkin Rasha bayan wani biki na ƙasaita da aka gudanar a ranar Talata a Fadar Cremlin, bayan ya rusa abokan hamayyarsa na siyasa tare da samun cikakken ƙarfi a hannuna.

Tuni ya kwashe kusan shekaru 25 a kan mulki kuma wanda ya fi kowa daɗewa a mulkin Fadar Cremlin bayan Josef Stalin, Putin zai kammala wannan wa'adi a shekarar 2030, kuma bayan nan kundin tsarin mulki ya ba shi damar sake tsayawa takara da yin wani wa'adin na shekaru shida.

Bayan fara yaƙin Ukraine a 2022 wanda ya zama yaƙi mafi girma a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na II, ƙasashen Yamma sun kakaba wa Rasha takunkumai, kuma ta koma mu'amala da kasashe irin su China, Iran da Koriya ta Arewa don neman goyon baya.

Abin tambaya a nan shi ne me Putin dan shekara 71 zai yi a sabon wa'adin mulki na shekaru shida, a cikin gida da wajen kasar?

Kare martabar kasa

Dakarun Rasha na samun ƙarfin mamaya a Ukraine, na amfani da dabaru a lokacin da Kyiv ke fama da karancin mayaka da makamai. Dukkan bangarorin biyu na tafka babbar asara.

Ukraine ta kai yakin zuwa yankunan Rasha ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami, musamman a hare-haren yankunan da ke kan iyaka.

A wani jawabi da ya yi a watan Fabrairu, Putin ya yi alkawarin cika manufofin Moscow a Ukraine, sannan zai yi duk mai yiwuwa don kare martaba da 'yancin Rasha tare da samar da tsaron kasa.

Jim kadan bayan sake zabar sa a watan Maris, Putin ya bayyana cewa akwai yiwuwar a yi fito na fito tsakanin NATO da Rasha, kuma ya bayyana yana son samar da yankin samun kariya a kasar Ukraine don kare kasarsa daga harin kan iyaka.

Sai kuma me?

A cikin gida, farin jinin Putin ya ta'allaka ne ga yadda ya inganta rayuwar al'ummar Rasha a yayin da tattalin arzikin kasar ke bunkasa.

Ya fara wa'adin d aya kammala a 2018 ta hanyar yin alkawarin zai sanya Rasha zama daya daga cikin kasashe biyar mafiya karfin tattalin arziki a duniya, yana mai cewa hakan zai zo a zamanance ta hanyoyi daban-daban.

Sai dai kuma Rasha na kashe makudan kudade a bangaren tsaro.

Manazarta na cewa a yanzu da Putin ya samu damar kara yin wa'adi na shekaru shida a kan mulki, gwamnati na iya daukar matakan da ba za a so ba na kara haraji don daukar nauyin yakin da ake yi, tare da takura wa maza su shiga aikin soji.

A farkon fara sabon wa'adi, Putin ya rusa majalisar zartarwar gwamnatinsa ta yadda zai sanar da sabon Firaminista da majalisar ministoci.

Wani bangare da ake ta kallo shi ne ma'aikatar Tsaro.

Maganin 'yan hamayya

A shekarar da ta gabata Ministan Tsaro Sergei Shoigu ya fuskanci matsin lamba kan yadda yake kula da yakin, inda shugaban 'yan bindiga Yevgeny Prigozhin ya dinga sukarsa saboda karancin makamai ga mayakan da suka dauka haya don yaki a Ukraine.

Tawyen da Prigozhin ya yi a watan Yuni don adawa ga Ma'aikatar Tsaro ya zama babbar barazana ga mulkin Putin.

Bayan an kashe Prigozhin a hatsarin jiragen sama da watanni biyu, sai aka fahimci Shoighu ya yi nasarar cin yakin.

Amma a watan da ya gabata, an zargi yaronsa kuma mataimakin Ministan tsaro Timur Ivanov da hannu a ayukan cin hanci da rashawa.

Wasu masu nazari na cewa Shoigu na iya zama wanda sauyin ministoci zai iya shafa, amma hakan zai zama babban mataki saboda ana ci gaba da gwabza yaki a Ukraine.

Babban makiyin putin a siyasa, Alexei Navalny ya rasu a Arctic da ake tsare da shi a watan Fabrairu.

TRT Afrika