| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Iran ta yi watsi da zaman rashin tabbas tsakanin yaƙi da zaman lafiya da Amurka
Iran ce za ta ayyana iyakar duk wani rikici da zai iya barkewa nan gaba idan Amurka ta sake yin kuskure, ba Washington ba, a cewar mai magana da yawun majalisar dokokin Iran.
Iran ta yi watsi da zaman rashin tabbas tsakanin yaƙi da zaman lafiya da Amurka
A watan Yunin 2026, Washington da Tehran sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da nufin kawo karshen yakin. / َAA

Iran ta ce ba za ta ci gaba da kasancewa cikin wani yanayi na rashin tabbas tsakanin yaƙi da zaman lafiya da Amurka ba, inda babban jami’in da ke jagorantar tattaunawar ƙasar ya yi gargaɗin cewa a shirye Tehran take ta shiga tattaunawa ko kuma yaƙi da Amurka.

"Idan Amurkawa suka amince da sharuddanmu bakwai masu ma'ana, har yanzu kofar cim ma yarjejeniya a bude take," kamar yadda mai magana da yawun majalisar dokokin Iran kuma jagoran tawagar tattaunawar ƙasar, Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana a ranar Lahadi yayin buɗe zaman majalisar dokokin ƙasar ta yanar gizo, da kamfanin dillancin labarai na ISNA ya rawaito.

Masu AlakaTRT Afrika - Amurka ta kwashe jiragen soji daga sansanin sama na biyu a Birtaniya bayan rahoton barazanar Iran

‘‘Ko da yake, ya yi gargadin cewa ‘‘idan Amurka ta sake yin wani kuskure, karfin sojin Iran da kudurinta ne za su tantance iyakar duk wani fagen yaki, ba bukatu ko muradun Washington ba.’’ in ji shi.

Ghalibaf bai yi wani arin bayani kan sharuɗɗa bakwai ɗin ba, ko kuma irin yarjejeniyar da Iran za ta amince da ita ba.

Sai dai rahotannin baya sun nuna cewa sharuddan sun haɗa da dage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa da Amurka ta kakaba wa Iran,da tabbatar da wucewar jiragen ruwa na kasuwanci da dakon man fetur cikin aminci ta hanyar mashigar ruwan Hormuz, da kuma cire takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta kakaba wa Tehran.

Sauran sharuddan sun haɗa da cire takunkumi kan fitar da man fetur ɗin Iran, da sakin kadarorin ƙasar da aka daskarar, tare da bai wa Tehran damar ci gaba da rike makamanta na nukiliya a cikin ƙasarta da kuma kawo ƙarshen yakin.

Ghalibaf ya yi wadannan kalamai ne yayin bikin kaddamar da wata sabuwar cibiyar kera makamai masu linzami, wadda ya ce an gina ta ne a lokacin yaƙin, duk da hare-haren da ake kai wa ƙasar.

Kazalika, ya bayyana cibiyar a matsayin wata babbar nasara da ta wuce bangaren fasaha da tsaro, yana mai cewa tana nuna sauyin da ake samu a dabarun ƙarfin soji a yankin.

Ya kuma yaba wa rundunar sojin sama na ɗakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC), yana mai cewa ƙarfinta ya ƙalubalanci Isra'ila tare da ƙarfafa wa al’ummar Iran da masu goyon bayan Falasɗinawa gwiwa.

Masu AlakaTRT Afrika - Abin da bayyanar ‘birnin makamai masu linzami’ na karkashin kasa na Iran ke nufi ga yankin

Kakakin majalisar ya kuma soki kalaman da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya yi a baya-bayan nan, inda ya bayyana su a matsayin alamar takaicin Washington kan karfin Iran.

Ya ce ya kamata jami'an Amurka su yi nazari kan abin da ya kira gazawarsu ta fuskar dabarun soji a yankin Gulf, maimakon amfani da kalaman cin mutunci kan Iran.

Wannan martani na zuwa ne bayan Bessent ya yi amfani da kalaman batanci wajen bayyana shugabannin Iran, tare da kwatanta rundunar IRGC da wata dabba mai hatsari da aka jefa ta cikin kunci yayin wata hira da gidan talabijin.

Bessent ya kuma ce ya bar gidansa da ke Washington ya koma wani sansanin soji saboda fargabar tsaro.

Da yake magana kan harkokin cikin gida, Ghalibaf ya ce ƙalubalen tattalin arziki, musamman hauhawar farashin kayayyaki, da rashin aikin yi da kuma sauyin farashi, na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Iran ke mayar da hankali a kai, baya ga batutuwan tsaro da soji.

Amurka da Isra'ila sun kaddamar da yaki kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, inda Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka da ke yankin.

Daga bisani, bangarorin sun cim ma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a watan Afrilu.

A watan Yunin 2026, Washington da Tehran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

Sai dai koƙarin cim ma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya ya tsaya cak sakamakon sabanin ra'ayi kan 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da batutuwan tsaro a mashigar ruwan Hormuz, wadda ke da matukar muhimmanci wajen wucewar makamashi da kasuwanci a duniya.