Erdogan a UNGA: Gaza ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da abin kunya a zamaninmu

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi Isra'ila da rungumar manufar "kisan kare dangi da kuma nuna halin "rashin kakkautawa a kashe-kashen," a yayin jawabinsa da ya gabatar a Babban taron Zauren MDD da ke birnin New York.

By
Shugaban Reccip Tayip Erdogan ya gabatar da jawabi mai tsawo a taron UNGA karo na 81

Shugaba Erdogan ya yi kira da a fara sake gina Gaza ba tare da ɓata lokaci ba, inda ya buƙaci kasashen duniya su kara matsin lamba kan Isra'ila.

Yayin da yake jawabi a Zauren Babban Taron MDD karo na 81 a New York a ranar Talata, Erdogan ya ce ya kamata a soma ƙoƙarin sake gina Gaza da wuri-wuri.

"Dole ne mu soma sake gina Gaza ba tare da ɓata lokaci ba. Dangane da haka, ina kira a gare ku da ku kara matsin lamba kan Isra'ila," in ji shi.

Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya tana tare da wannan yarjejeniya da aka kulla a Sharm el-Sheikh shekara ɗaya da ta wuce, kuma za ta ci gaba da sa ido kan yadda ake aiwatar da ita.

Ya ce, a ƙarshe ba a yi nasara a duk wani kokari na hana kafa kasar Falasdinu ba.

"Ya kamata kowa ya fahimci kuma ya amince da wannan: Kokarin hana samar da kasar Falasdinu zai kare a rashin nasara," in ji shi.

Ya bayyana fatansa na ganin an kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta da cikakken ikon mallakar ƙasa, bisa yarjejeniyar da aka shata kan iyakoki na shekarar 1967, tare da sanya Gabashin Kudus (wadda Isra'ila ta mamaye) a matsayin babban birninta.

"Da yardar Allah, za mu ga waɗannan kwanaki masu muhimmaci inda za a samu ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta da cikakken ikon mallakar kasa, bisa yarjejeniya kan iyakoki na 1967 tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta," in ji Erdogan.

Kasar Falasdinu, rashin halartar Abbas a taron UNGA

A yayin soma gabatar da jawabinsa, Erdogan ya bayyana bakin ciki game da rashin baiwa Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas damar halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya tsawon shekaru biyu a jere.

"Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, ya kasa zuwa wannan zauren tsawon shekaru biyu a jere. Wannan rashin adalci ga 'yan'uwanmu Falasdinawa yana baƙanta zukata da kuma tayar da hankali," in ji shi.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da yin magana a madaɗin ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta da cikakken iko, duk da rashin halartar Abbas.

"Duk da cewa Abbas bai samu damar kasancewa a nan da kansa ba, kamar yadda muka yi a bara, za mu zama muryar Falasdinu mai 'yanci da cikakken ikon mallakar kasa," in ji shi.

Erdogan ya yi kira ga ƙasashe da su amince da ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. "A yau, na sake yin kira ga dukkan ƙasashen da ba su riga sun amince da ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta ba, da su sake duba matsayinsu," in ji shi.

Yanayin jinƙai a Gaza

Da yake magana kan halin da ake ciki a yankin Gaza, Erdogan ya bayyana yankin a matsayin wani babban kabari na yara na duniya, da kuma yankin da ya fi kowanne yawan yaran da suka rasa gabobinsu sakamakon hare-hare.

Erdogan ya ce an kashe Falasdinawa 74,000 a Gaza cikin shekaru uku da suka wuce—wadanda yawancinsu mata da yara ne—yana mai bayyana su a matsayin wadanda suka faɗaa cikin tarkon "ta'addancin gwamnatin Isra'ila."

Ya ce Falasɗinawa na ci gaba da neman 'yan uwansu a karkashin baraguzan gine-gine da kuma zakulo gawarwakin matansu da 'ya'yansu, da kuma iyayensu, yayin da yaran da suka rasa gabobinsu a hare-haren Isra'ila ke kokarin komawa makaranta da kuma ci gaba da rayuwarsu ta hanyar amfani da gabobin roba ko na katako.

Erdogan ya ce fiye da kashi 70 cikin dari na injinan samar da wutar lantarki a asibitocin Gaza ba sa aiki a halin yanzu saboda karancin man fetur.

"Gaza ita ce sansanin tsare mutane mafi muni da rashin tausayi da kuma abin kunya a zamaninmu," in ji shi.

Erdogan ya ce an kashe Falasɗinawa fiye da 1,500 bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoban 2025, wadda aka cim ma ta hanyar ƙoƙarin Shugaban Amurka Donald Trump da kuma gudummawar da Turkiyya da sauran ƙasashe suka bayar.

Ya ce duk da cewa ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu ta amince ta shiga mataki na biyu na shirin samar da zaman lafiya, gwamnatin Isra'ila ba ta nuna sha'awar kawo ƙarshen mamayar da take yi wa yankin ba.

Yayin da ya koma kan batun yankin Yammacin Kogin Jordan (West Bank) da Isra'ila ta mamaye, Erdogan ya ce yankin na fuskantar munanan hare-hare daga Yahudawa ‘yan kama wuri-zauna, inda suka hana Musulmai da Kiristoci zuwa wuraren ibadanrsu masu tsarki a birnin Kudus.

Kazalika ya bayyana cewa ana yawan kai wa hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinu (UNRWA) hari.

"Muna fama da wata akida ta kisan ƙare dangi,’’ in ji Erdogan, yana mai kari da cewa babu wani mutum mai imani da tausayi da kuma jinkai da zai iya yin biris da wannan yanayi.

Ya jaddada cewa batun ba wai ya shafe shi shi kadai bane, amma batu ne na " jinƙai" kana "batu ne da ya shafe imaninmu baki ɗaya.’’

Garambawul a tsarin MDD

Erdogan ya ce wannan yanayi ya nuna cewa Majalisar Dinkin Duniya—wadda aka kafa ta shekaru 81 da suka wuce domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro—ta gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Ya ce mutanen da ke yankin Falasɗinu da Lebanon da Sudan da sauran yankunan da ke fama da rikici waɗanda suka dogara ga Majalisar Dinkin Duniya sun yi matuƙar takaici.

"Wata rana, kowa zai iya neman mafaka a cikin lamirin ɗan adam," in ji shi, yana mai gargaɗin cewa duk da cewa wasu mutane suna cikin yanayi na aminci da kuma nesa ga yankunan da ke fama da rikici a halin yanzu, to amma babu wanda ya san abin da makomar za ta iya kawowa.

Erdogan ya ce, ya yi la'akari da jigon Babban Taron na wannan shekarar, wanda ya mayar da hankali kan sake gina aminci ga tsarin ƙasa da ƙasa, yana mai cewa hakan ya dace kuma ya nuna goyon baya ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a Kokarinsa na yin garambawul gami da Shirin UN80.

Ya ce, yarda da MDD zai iya dawo wa ne kawai idan yara a Gaza za su rayuwa cikin tsaro da aminci, kuma idan yaran Falasdinawa za su iya kallon sama ba tare da fargaba da tsroron jiragen marasa matuki ba, inda yara a Lebanon ba su farka daga jin karar bama-bamai ba, inda ba a cin zarafin ma'aikata kana mutanen Afirka za su iya duba makomarsu da kwarin gwiwa.

Erdogan ya kuma jaddada kiransa na yin garambawul ga Majalisar Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa babu adalci a tsarin da kasashe biyar ne kawai za su iya tsara makomar kasashe fiye da 190.

"Dole ne a yi garambawul a tsarin Majalisar Tsaron bisa ga ka'idar cewa 'duniya ta fi grima tsarin kasashe biyar kawai,'" in ji shi.

Dokokin ƙasa da ƙasa, diflomasiyya da rashin daidaito na duniya

Erdogan ya ce dole ne al'ummar duniya su canza hanyar da ake amfani da tsarin kan kasashe masu karfi da kuma masu rauni .

"Tsarin kasa da kasa wanda masu aikata laifi ke tserewa daga abin da suka aikata kuma hukunci ya dauki tsawon lokaci ba tare da aiwatarwa ba," in ji shi.

Da yake bayyana ƙa'idodin samar da tsari mai adalci na ƙasa da ƙasa, Erdogan ya ce ya kamata a yi amfani da ikon mallakar yanki idan aka ga ƙoƙarin ƙasashen duniya na magance rikice-rikice ya kai ga wani yanayi na rashin tabbas, yana mai ambaton hanyar Black Sea Grain Corridor a matsayin misali na wani shiri da ya ba da gudummawa ga tsaron yanki da na duniya.

Ya kuma yi kira da a samar da haɗin gwiwa da diflomasiyya a yanayin dangantakar ƙasashe daban-daban, yana mai jaddda cewa tarihi ya nuna a lokuta da dama siyasar da aka gina ta kan rashin yarda ba ta haifar da masu nasara.

Erdogan ya yi kira da a samar da sabon tsari don magance gibin rashin daidaiton a kuɗaɗen da duniya ke samu, yana mai cewa ci gaba a tare, da haɗin kai da kuma haɗin gwiwa sune mabuɗin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya kuma yi gargaɗi game da "fasahohin da ke raba kan al'umma" da "ikon mallakar fasahar zamani," yana mai cewa ya kamata ci gaban fasaha ya mai mayar da hankali kan ɗan adam ba wai ya haifar da sabbin rarrabuwar kawuna tsakanin waɗanda ke da damar amfani da fasaha da waɗanda ba su da ita ba.

Diflomasiyyar yankin Turkiyya

Erdogan ya ce Turkiyya tana neman tsarin ƙasa da ƙasa mai adalci da mutuntaka ba wai kawai ta hanyar yin magana ba har ma ta hanyar manufofinta.

 A bangaren ƙungiyar haɗaka ta tsaro da aka kafa tsakanin Pakistan da Saudiyya, Shugaban Turkiyya ya ce ƙasarsa tana da nufin ƙarfafa haɗin kai da kuma haɓaka hanyoyin magance matsalolin yanki.

Ya ce Ankara na ci gaba da kokarin da take yi da masu ruwa da tsaki don kawo ƙarshen rikici a yankin Gulf kuma ya yi gargadi game da yunkurin yada faɗan yankin zuwa yankunan makwabta.

Yakin Syria da Iraki da kuma Ukraine

Kalika Erdogan ya tabo batun Syria, inda ya ce kasar ta shiga wani sabon babi tun daga Disamban 2024 bayan shafe shekaru 14 na kunci.

Ya ce Syria, karkashin jagorancin Shugaba Ahmed al-Sharaa, tana ci gaba da zama kasa mai aminci da zaman lafiya duk da kalubale na ciki da wajen ƙasar, kuma Turkiyya za ta ci gaba da tsayawa tare da al'ummar Syria.

Dangane da batun Iraki kuwa, Erdogan ya ce Turkiyya ta goyi bayan kokarin karfafa ikon gwamnati da kuma karfafa zaman lafiya kuma tana aiki tare da Baghdad kan ayyukan sufuri da makamashi na dabaru, musamman aikin Hanya Mai Ci Gaba.

 Haka kuma a jawabinsa game da yakin Rasha da Ukraine, Erdogan ya ce Turkiyya na son a kawo ƙarshen rikicin tare da tabbatar da 'yancin Ukraine da kuma tabbatar da tsaron yankin.

Ya ce Ankara ta ci gaba da tuntubar bangarorin biyu don dawo da tsaron hanyoyin ruwa a Tekun Bahar Maliya, tare da tabbatar da tsaron abinci da kuma hana yakin ya bazu zuwa wani yanki mai fadi.

Erdogan ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kasuwanci a Bahar Maliya, yana mai cewa irin waɗannan hare-haren "ba za a yarda da su ba ko da kuwa wanene ya kai su."

Gabashin Bahar Maliya da Cyprus

Erdogan ya ce Turkiyya ya yi imanin cewa dole ne a kiyaye 'yancin zirga-zirga ta Tekun Hormuz.

Kan batun yankin Tekun Aegean da Gabashin Bahar Maliya, ya ce ya kamata a warware rikice-rikicen da ke akwai bisa ga kyakkyawar alaƙar maƙwabta da dokokin ƙasa da ƙasa.

Ya kuma ƙara da cewa shawarar Turkiyya a taron Gabashin Bahar Maliya na iya taimakawa wajen kafa daidaito tsakanin al'ummar Cyprus ta Turkiyya da kuma daidaita matsayinsu na ƙasa da ƙasa da kuma kawo ƙarshen ware kansu a duniya.

Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su amince da Jamhuriyar Arewacin Cyprus ta Turkiyya tare da kafa dangantakar siyasa, diflomasiyya da tattalin arziki da ita.

Matsayin Turkiyya a fannin tsaron Turai

Erdogan ya bayyana Turkiyya a matsayin ‘‘tsibiri na kwanciyar hankali’’ a tsakanin rikice-rikicen yanki, yama mai masana’antar tsaro da tattalin arzikinta, yana mai cewa ƙasar ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a tsaro da wadata a Turai.

Da yake magana game da taron koli na NATO da aka shirya a Ankara a watan Yuli, ya ce taron ya nuna jajircewar Turkiyya ga tsaron bai daya.

"Ba zai taba yiwuwa Turai ta iya ware Turkiyya daga tsarin tsaronta ta zama mai ƙarfi ko aminci ba," in ji Erdogan, yana mai ƙari da cewa Ankara na sa ran Tarayyar Turai za ta ɗauki irin wannan hangen nesa na dabarun a dangantakarta da Turkiyya.

Kasashen Balkan, Kudancin Caucasus da Turkiyya

A kan ƙasashen Balkans, Erdogan ya bayyana muhimmancin alakar tarihi da al'adu da kuma ta ɗan adam da ke tsakanin Turkiyya da wannan yanki, tare da cewa ana daukar matakan haɗin gwiwa ta hanyar shirin Zaman Lafiya na Balkan domin zurfafa wannan haɗin gwiwa.

Game da yankin Caucasus ta Kudu, ya nuna goyon bayansa ga samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Azerbaijan da Armenia, tare da yaba wa Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev da Firaministan Armenia Nikol Pashinyan bisa kuɗirinsu na samar da mafita.

Ya ce Turkiyya na ci gaba da dawo matakan daidaita alakarta da Armenia.

Erdogan ya bayyana cewa Kungiyar Kasashen Turkic ta zama abin koyi wajen haɗin gwiwar yanki, kuma taron shugabannin kungiyar karo na 13, wanda aka tsara za a gudanar a Ankara a ranar 30 ga watan Oktoba, zai bude sabbin damammaki ga ƙungiyar.

Ya ce taron haɗin gwiwa na hudu tsakanin Turkiyya da Afirka, wanda za a gudanar a Libya a watan Disamba, zai zama wata alama ta shekaru fiye da ashirin a haɗin gwiwa da ke tsakanin hukumomin Turkiyya da na Afirka.

Da yake tsokaci kan al'amuran Kudancin Asiya, Erdogan ya ce ya kamata a magance takaddama, ciki har da batun Kashmir, ta hanyar tattaunawa bisa tsarin dokoki da suka dace da na Majalisar Dinkin Duniya.

"Idan aka bi hanyar da za ta haifar da sakamako mai kyau, za a iya magance duk wata matsala," in ji shi.

Afirka, yankin Asiya-Pacific da Latin Amurka

Yayin da ya koma kan Afirka, Erdogan ya bayyana goyon bayan Turkiyya ga kokarin tsagaita wuta da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a Sudan, tare da samar da matakan karfafa tsaro, da ci gaba da kuma karfin hukumomi a Somaliya.

Ya ce tabbatar da kwanciyar hankali a Libya na ci gaba da zama abin da ke kan gaba, inda ya jaddada cewa ya kamata tsarin sulhu ya gudana karkashin jagoranci da kuma ikon 'yan kasar Libya da kansu.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da karfafa alaka da abokan huldarta a yankin Asiya-Pacific ta hanyar shirin "Asia Anew Initiative" (Sabon Tsarin Asiya), kuma ya kwatanta matsayin alaka da kungiyar ASEAN zuwa ga wani mataki na "Abokan Tattaunawa" a matsayin sakamako mai inganci na wannan manufa.

Kazalika ya ce Turkiyya tana ƙara ƙarfafa alakarta da kasashen Latin Amurka da Caribbean ta hanyar girmama juna da haɗin gwiwa da kuma tsarin da zai amfani dukkan bangarori.

Canjin yanayi da taron COP31

Game da batun canjin yanayi, Erdogan ya ce duniya na fuskantar barazanar muhalli mai tsanani da ke shafar iska, ruwa, kasa da halittu masu rai, yayin da kasashe masu tasowa da yankin Pacific ke fuskantar kalubale wajen samun kudade da ake buƙata don tunkarar matsalar yanayi.

Ya ce Turkiyya za ta karbi bakuncin taron COP31 a Antalya a watan Nuwamba, kuma za ta yi kokarin sanya batun adalci a fannin yanayi a matsayin babban jigon taron.

Erdogan ya ce haɗin gwiwar Turkiyya da Australia ta kuduri aniyyar sanya taron COP31 zama wanda zai mayar da hankali kan "aiwatar da ayyuka," inda za a cika alkawuran bayar da kudade, da hanzarta canja fasaha, da kuma cika alkawura da aka dauka zuwa matakai na zahiri.

Ya yi nuni da Ƙungiyar Zero Waste Movement da matar shugaban ƙasa Emine Erdogan ta ƙaddamar a shekarar 2017, yana mai cewa ta girma zuwa wani gangami na wayar da kan jama'a a duniya. Ya bayyana shirin a matsayin babbar gada da ke haɗa hanyoyi daban-daban na yaƙi da matsalar yanayi.

Sharar abinci da tsaron abinci a duniya

Erdogan ya yi gargaɗin cewa yawan cin abinci da kuma karuwar al'ada ta zubar da shara na haifar da barazana ga sauyin yanayi.

Ya ce ana zubar da tiriliyan 5.8 na abinci, wanda ya kai tan biliyan 2 a faɗin duniya kowace shekara, yayin da ɗaruruwan miliyoyin mutane ke neman abinci a cikin shara.

A shirye Turkiyya take ta bayar da gudummawa ga ƙoƙarin rage sharar gida da ƙarfafa tsaron abinci a duniya, in ji shi.

Erdogan ya kuma sanar da cewa Turkiyya ta zaɓi Mehmet Mehdi Eker a matsayin darakta janar na Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya kuma ta nemi goyon bayan ƙasashe membobinta.

Kiyayya ga Musulunci, wariya da kafofin sada zumunta

Haka kuma Erdogan ya tabo batun barazana na zamantakewa da ke tasowa, inda ya ce ƙiyayya ga Musulunci na yaɗuwa a ƙasashen Yamma kuma mata da 'yan mata Musulmai suna fuskantar wariya sosai.

Ya soki haramcin sanya hijabi a makarantu a wasu ƙasashe, yana mai bayyana su a matsayin hari ga haƙƙin mata na asali.

Erdogan ya ce ƙiyayya ga baƙi, da wariyar launin fata da kuma nuna wariyar Yahudawa wani yanayi ne mai cutarwa wanda ke buƙatar ɗaukar mataki mai tsauri.

Ya soki "manufofin raba jinsi," yana mai cewa Turkiyya za ta ci gaba da shirye-shirye kan kare iyali da yara.

Erdogan ya kuma bayyana yada labaran ƙarya a shafukan sada zumunta a matsayin wata barazana ga zaman lafiyar al’umma, kana ya ce kare gaskiya ya fi muhimmanci a kowane lokaci.

Ya yi kira da a hanzarta aiki don shirya da kuma aiwatar da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Majalisar Dinkin Duniya kan fasahar Zam.

Kira ga tsarin AI na ƙasa da ƙasa

Kan batun fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI, Erdogan ya yi kira da a samar da tsarin doka na bai- ɗaya a duniya, yana mai cewa lokacin da za a yi irin wannan tsari ya riga ya yi.

Ya yi kira da a hanzarta aiki don shirya da kuma aiwatar da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Majalisar Dinkin Duniya kan AI.

'Ba za mu yi shiru ba idan aka fuskanci rashin adalci'

Da yake kammala jawabinsa, Erdogan ya ce matsayin da ya bayyana zai dame wasu 'da ke da ruwa da tsaki a ciki, amma Turkiyya za ta ci gaba da magana a madadin waɗanda ke fuskantar rashin adalci.

Yayin da ya ambaton mawaƙin Turkiyya Sezai Karakoc, Erdogan ya ce ko da mutane sun yi shiru, "tarihin ba zai yi ba" kuma "gaskiya za ta yi halinta."

Ya yi alƙawarin ci gaba da kare abin da ya bayyana a matsayin haƙƙin waɗanda aka zalunta, waɗanda abin ya shafa da kuma wadanda ba su da murya, muddin yana da ikon yin hakan.

"Idan ya zama dole, za mu jure wahala; idan ya zama dole, za mu biya duk wani farashi. Amma ba za mu yi shiru ba yayin da ake aikata rashin adalci, kuma ba za mu taba amincewa da zalunci ba," in ji Erdogan.

Ya bayyana cewa duniya na da zabi biyu, woto barin tsoro da rikici da kuma killacewa su kara jefa al'amura cikin rashin tabbas, ko kuma gina makoma ta hanyar adalci, hadin kai, da kuma kudurin bai-daya.

Ya jaddada cewa Turkiyya ta zabi hanyar ta biyu kuma za ta ci gaba da tafiya a kan ta, tare da yin kira ga wadanda ke sauraronsa a Majalisar Dinkin Duniya da kuma sassan duniya baki daya, da su goyi bayan wannan kuduri na bai-daya kan makomar gobe.