Matar shugaban ƙasar Turkiyya, Emine Erdoğan, ta ƙaddamar da Ƙungiyar Kawance ta kawar da Shara ta Duniya (Global Zero Waste Alliance) a yayin taron COP31, inda ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya domin daura damarar haɗin gwiwa mai ɗorewa da ayyukan da suka shafi muhalli da za su samar da sakamako a zahiri.
Da take jawabi a wani taron matan shugabannin ƙasashe da ta shirya a birnin Antalya a ranar Laraba, wanda ya zo a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi, Erdogan ta ce ƙungiyar za ta samar da wani dandali da ƙasashe za su riƙa musayar dabarun da suka yi nasara, da kuma ƙirƙirar ayyukan haɗin gwiwa da yaɗa hanyoyin magance matsalolin muhalli daga matakin cikin gida zuwa duniya baki ɗaya.
Ta ce ƙaddamar da ƙungiyar na nuna ƙudirin ƙasashen duniya na wuce matakin yin alƙawura kawai, zuwa aiwatar da matakan da za su samar da sakamako mai ma'ana.
"Ƙungiyar Kawar da Shara ta Duniya da muke ƙaddamarwa a yau, alama ce ta ƙudirinmu na mayar da wannan nauyi na bai ɗaya zuwa haɗin gwiwa mai ɗorewa," in ji ta.

Erdoğan, wadda ita ce shugabar kwamitin ba da shawara ga babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan batun kawar da shara, ta jaddada cewa lokaci ya yi da duniya za ta daina mayar da hankali kan tattauna barazanar sauyin yanayi kawai, ta fara aiwatar da hanyoyin magance matsalar.
"Yanzu ne lokacin da za mu dora daga kan rahotanni, da gargaɗi da kuma manufofin da ke nuna girman matsalar sauyin yanayi," in ji ta, inda ta ƙara da cewa ya kamata mu auna girman ilimi ga irin matakai da ayyukan da ake samu.
Ta bayyana taron COP31 a matsayin taron aiwatar da matakai (Action COP), inda ta ce Turkiyya na son a duba nasarar taron ba kawai ta yawan alƙawuran da aka ɗauka ba, har ma da sauye-sauyen da za su kawo sauyi ga rayuwar al'umma, da birane da kuma tsarin samar da kayayyaki .

Da take magana kan shirin Turkiyya na kawar da shara (Zero Waste Movement), wanda aka ƙaddamar shekaru tara da suka gabata, Erdoğan ta ce shirin ya bunƙasa daga wayar da kan iyalai zuwa wani tsari na ƙasa baki ɗaya da ya haɗa makarantu, da ƙananan hukumomi, da hukumomin gwamnati da kuma masana'antu.
Dole ne a hana samar da shara kafin a yi tunanin sake sarrafa ta
"Ya kamata mu auna nasararmu ba kawai da yawan sharar da muka tattara muka sake sarrafawa ba, har ma da yawan sharar da muka hana samuwarta," in ji ta.
Ta ƙara da cewa ya kamata samar da ingantacciyar rayuwa ta hanyar amfani da ƙananan albarkatu ya zama ginshiƙi a dabarun ci gaban ƙasashe.
Ta kuma yi kira da a ƙara sanya ido kan yadda ake samarwa da amfani da kayayyaki a duniya, tana mai nuna illolin da wasu masana'antu ke haifarwa ga muhalli, ciki har da masana'antar taba, da na masaku da kuma na fasahar zamani.
Da take ambaton alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Erdogan ta ce masana'antar taba na haddasa sare bishiyoyi miliyan 600 tare da amfani da ruwa tan biliyan 22 a kowace shekara.
Ta kuma bayyana cewa masana'antar tufafi da masaku na samar da kimanin tan miliyan 92 na shara a kowace shekara, tana mai cewa rage tsawon lokacin amfani da kayayyaki kafin a yar da su ba za a iya danganta shi da zaɓin masu saye kawai ba.
Erdogan ta ce akwai bukatar a yi tambayoyi game da yawan makamashi da ruwa da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan manyan cibiyoyin fasaha, musamman tsarin kasuwancin intanet da aka tsara domin mutane su daɗe suna amfani da shafuka da manhajoji.
Kira ga kamfanoni su ƙara ɗaukar alhakin kare muhalli
Da take magana kan ci gaban fasaha, Erdogan ta ce fasahar basirar ɗan'adam (AI) na da babbar rawa wajen rage shara da, inganta samar da kayayyaki da kuma hanyoyin magance matsalolin muhalli.
Sai dai ta yi gargaɗin cewa bai kamata a ware ci gaban fasaha daga illolin da yake iya haifarwa ga muhalli ba.
"Ba za mu iya gina fasahohin nan gaba bisa halayen almubazzaranci na baya ba," in ji ta.
Ta yi kira da a samar da ƙa'idojin ƙasa da ƙasa domin tabbatar da cewa manyan kamfanoni na bayyana yawan albarkatun da suke amfani da su, su amince da bincike mai zaman kansa kan tasirinsu ga muhalli, tare da ƙarfafa ɗaukar alhaki.
"Alhakin kamfanonin da ke gudanar da ayyukansu a matakin duniya ma ya kamata ya kasance na duniya baki ɗaya," in ji ta.
Erdoğan ta kuma jaddada mummunan tasirin yaƙe-yaƙe ga muhalli, tana mai cewa rikice-rikicen makamai na haddasa lalacewar muhalli da ka iya ɗaukar tsararraki kafin a gyara.
Da take misali da Gaza, ta ambaci ƙididdigar Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP), wadda ta nuna cewa yaƙin ya haifar da tarin baraguzan gine-gine da ya kai tan miliyan 61 a faɗin yankin Falasɗinu.
Ta kuma ce kashi 97 cikin 100 na gonakin itatuwa da lambunan zaitun a yankin sun lalace, yayin da aka gurɓata mafi yawan sauran hanyoyin samun ruwan sha.
Ta yi gargaɗin cewa dawo da muhalli da ababen more rayuwa bayan irin wannan ɓarna na iya ɗaukar tsararraki.
A daidai lokacin da kuɗaɗen da ake kashewa a harkokin soja a duniya suka kai sabon matsayi na dala tiriliyan 2.9, Erdoğan ta buƙaci ƙasashen duniya su yi tunanin irin ayyukan da za a iya cimmawa idan aka karkatar da ko da wani kaso kaɗan na kuɗaɗen zuwa magance matsalolin jin ƙai da na muhalli.
"Za a iya sake gina birane, dawo da martabar wuraren da suka lalace, sannan zaman lafiya ya zama yanayin da zai mamaye kowace nahiya," in ji ta.
Muhimman fannoni biyar da ƙungiyar za ta mayar da hankali a kai
Erdoğan ta ce Ƙungiyar Kawar da Shara ta Duniya za ta mayar da hankali kan muhimman fannoni guda biyar:
Kawar da shara da tattalin arzikin sake amfani da albarkatu.
Sharar leda da kayan marufi.
Samar da yankuna marasa shara.
Sharar abinci da sauran abubuwan da ke ruɓewa.
Ilimi da matasa.
Ta ce ƙungiyar za ta gudanar da ayyukanta ta hanyoyi uku masu taimaka wa juna, ciki har da taron Zero Waste na shekara-shekara, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashe da hanyoyin magance su.
Haka kuma, za a yi amfani da dandalin Istanbul wajen mayar da shawarwari zuwa ayyuka na zahiri da haɗin gwiwa.
Ta ce ƙungiyar za ta haɗa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ƙananan hukumomi, jami'o'i da masana ilimi, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula domin cimma manufofin da suka yi tarayya a kai.
Da take jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya magance matsalolin muhalli ita kaɗai, Erdoğan ta gayyaci matan shugabannin ƙasashen da suka halarci taron da su zama abokan hulɗa masu taka rawa wajen gudanar da shirin, tare da musayar nasarorin da ƙasashensu suka samu.
Ta ce taron ya kamata ya zama matakin farko na samar da sabbin haɗin gwiwa, ayyukan bai ɗaya da ci gaba da za a iya aunawa, tana mai kira ga mahalarta da su koma ƙasashensu da ƙudirin ci gaba da aiki tare.
Manyan baƙi daga ƙasashe daban-daban
Taron ya samu halartar matan wasu shugabannin ƙasashen duniya, ciki har da Janja Lula da Silva ta Brazil, Ziroat Mirziyoyeva ta Uzbekistan, Ancelly Simina ta Micronesia, Sajidha Mohamed ta Maldives da Gueta Selemane Chapo ta Mozambique.
Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Nilden Bektaş Erhürman, matar shugaban Jamhuriyar Cyprus ta Arewa; Francine Ntakarutimana ta Burundi; Zubaida Rahman, matar firaministan Bangladesh; da Zainab Suleman, surukar firaministan Pakistan.
Shugaban Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), Alexander De Croo, da babbar daraktar Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da matsugunan mutane (UN-Habitat), Anacláudia Rossbach, su ma sun gabatar da jawabai a wajen taron.























