Rahotanni sun ce za a ci gaba da hulɗar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Amurka da Nijar duk da wannan matakin. Photo: AP Archive

Jami'an Amurka za su gana a yau Alhamis da mambobin gwamnatin Nijar kan janyewar sojojin Amurka daga ƙasar ta Afirka, in ji kakakin Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon.

“A cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, jakadiyar Amurka a Nijar Kathleen FitzGibbon da Manjo Janar Kenneth Ekman, daraktan tsare-tsare na rundunar sojojin Amurka a Afirka, za su gana da jami’an Kwamitin Tsaro na gida (CNSP) a ranar 25 ga Afrilu a Yamai, babban birnin Nijar don fara tattaunawa kan janyewar sojojin Amurka daga Nijar cikin tsari da aminci," kamar yadda Manjo Janar Pat Ryder ya faɗa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Ryder ya ƙara da cewa, Christopher Maier, mataimakin sakataren tsaro na musamman kan ayyuka na musamman da rikice-rikicen da ba gagarumai ba, da Laftanar Janar Dagvin Anderson, daraktan dakarun haɗin-gwiwa, za su gudanar da tarukan bibiyar tattaunawar a babban birnin Yamai a mako mai zuwa.

Amurka tana da sojoji kusan 1,100 a Nijar.

Jamhuriyar Nijar dai na ƙarƙashin mulkin soji ne wanda ya hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata, saboda taɓarɓarewar yanayin tsaro.

Ƙasar Afirka ta Yamma ta soke yarjejeniyar soji da ta daɗe da ƙullawa da Washington a farkon watan Maris na wannan shekara, inda ta bayyana kasancewar dukkan sojojin Amurka da ‘yan kwangila a matsayinn waɗanda ke zaune a cikin ƙasar “ba bisa ƙa’ida ba” saboda “ba a amince da ita ta hanyar dimokuraɗiyya, kuma ta sanya sharuddan da ba su dace ba a Nijar, musamman ta fuskar rashin gaskiya kan ayyukan soji,” a cewar kakakin gwamnatin Nijar Amadou Abdramane.

A lokacin gwamnatocin da suka gabata a Nijar, sojojin Amurka sun horar da sojojin Nijar kan yaƙi da ta'addanci.

TRT Afrika