Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas sun zama shugabannin majalisar dokokin Nijeriya

Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas sun zama shugabannin majalisar dokokin Nijeriya

Sanata Akpabio ya rike mukamin gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015.
Akpabio ya samu kuri'a 63 yayin da Yari ya samu kuri'a 46. Hoto/Fadar Shugaban Nijeriya da Tajudeen Abbas

Sanatocin Nijeriya sun zabi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a matsayin sabon shugaban majalisar dattawan kasar.

Su ma 'yan majalisar wakilan kasar sun zabi Honorabul Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisarsu.

An yi zaben ne ranar Talata yayin kaddamar da majalisun dokokin biyu.

Akpabio ya samu kuri'a 63 a fafatawar da ya doke tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari wanda ya samu kuri'a 46.

Honorabul Abbas ya samu kuri'a 353 a zaben da ya kayar da tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai Ahmed Idris Wase, da dan majalisa Sani Jaji wadanda suka samu kuri'u uku kowannensu.

An kuma zabi Benjamin Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilan kasar.

Kazalika sanatocin sun zabi Sanata Barau Jibrin, daga jihar Kano, a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar.

Mutanen hudu su ne wadanda shugaban kasar Bola Tinubu da jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya suka mara wa baya a zaben.

Sanata Akpabio, wanda tsohon Ministan Yankin Neja Delta ne a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya taba zama Sanata a 2015 kuma ya rike mukamin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan Nijeriya.

Ya rike mukamin gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Tsakanin shekarun 2002 zuwa 2006, Akpabio ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma’aikatu uku.

Ya yi kwamishinan man fetur da albarkatun kasa, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarautu da kuma kwamishinan filaye da gidaje.

Shi kuma Honorabul Abbas, wanda shi ne Dan Iyan Zazzau, ya soma zama dan majalisar wakilai a 2011 karkashin 2011 rusasshiyar jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC).

Sai dai yanzu ya lashe zabe ne a karkashin jam'iyyar APC.

A nasa bangaren, Sanata Jibrin tsohon dan majalisar wakilan kasar ne, kuma ya dade a majalisar dattawa.

TRT Afrika