Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov da takwaransa na Saliyu Timoth Musa Kabba. 

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce Moscow da Saliyo na tunanin ƙulla wata yarjejeniya ta makamashin nukiliya, daga ciki har da kafa tashar nukiliya ta wutar lantarki a ƙasar da ke Yammacin Afirka.

An sanar da wannan shirin ne a ranar Talata a wani taron manema labarai bayan da Lavrov ɗin ya tattauna da takwaransa na Saliyo Timothy Musa Kabba.

“Mun amince da minista kan cewa zai samar da ƙarin masu zuba jari na Rasha a sassa daban-daban, ciki har da a fannin yiwuwar yin haɗin gwiwa a fannin makamashin nukiliya ta ɓangaren makamashi,” in ji shi.

Sake buɗe ofishin jakadancin Rasha

Ministan harkokin wajen Rasha ya ce Moscow za ta sake buɗe ofishin jakadancinta na Saliyo zuwa ƙarshen shekara.

“Muna shirin buɗe sabbin ofisoshin jakadanci a nahiyar Afirka, daga ciki har da a Freetown.

A Freetown, muna sa ran yin hakan a bana, kafin ƙarshen shekara,” in ji Lavrov.

An ɗauki duka wasu matakai da suka dace kuma lokaci ya yi da za a aiwatar da su, in ji Lavrov.

Kabba ya bayyana cewa sake buɗe ofishin jakadancin bayan shekara 32 zai taimaka wurin ƙara yauƙaƙa dangantaka tsakanin ƴan kasuwan Rasha da Saliyo.

AA