Gwamnatin Nijeriya ta haramta amfani da Binance ɗin a kwanakin baya kan zarge-zarge da dama ciki har da zargin hannu a karya darajar naira. / Hoto: Reuters

Shugaban kamfanin Binance Richard Teng ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta saki ɗaya daga cikin manyan jami’an kamfanin da take tsare da shi.

Mista Teng ya bayyana haka ne a wani saƙo da kamfanin na Binance ya wallafa a shafinsa na intanet inda ya buƙaci gwamnatin ta saki Tigran Gambaryan domin ya tafi wurin iyalinsa.

Gwamnatin Nijeriya ta kama Mista Gambaryan wanda shi ne shugaban kula da sashen laifukan kuɗi na Binance kan zargin halasta kuɗin haram inda kuma yake tsare a ƙasar sama da kwanaki 70.

An kama Gambaryan a watan Fabrairu bayan ya je ƙasar domin tattaunawa.

A cikin sanarwar da shugaban na Binance ɗin ya fitar, ya ce kamfaninsa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa an warware matsalolin harajin da ake zargin ƙasar na bin kamfanin.

Shugaban na Binance ɗin ya bayyana cewa yana da muradin kamfaninsa ya yi aiki tare da Nijeriya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

A watan Maris, hukumar EFCC ta Nijeriya wadda ke yaƙi da rashawa ta zargi Binance da Gambaryan da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla da abubuwa da dama.

Daga ciki har da batun “aiki ba tare da lasisi ba, da cinikin kuɗin waje ba bisa ƙa’ida ba da ƙin biyan haraji da kuma ƙin bayyana asalin kuɗin shiga na dala miliyan 35.4.”

Sai dai tuni Nadeem Anjarwalla ya gudu daga Nijeriya a lokacin da yake tsare a hannun jami’an tsaro, lamarin da ya yi matuƙar tayar da ƙura a Nijeriya.

TRT Afrika da abokan hulda