Taliban dai ta karbe iko da Afghanistan bayan janyewar dakarun NATO da Amurka ke jagoranta a kasar a 2021 / Photo: AP

Afghanistan ta yanke shawarar fara amfani da katafariyar hanyar kasuwancin nan ta kasashen China da Pakistan ta biliyoyin daloli, CPEC, wadda za ta taimaka wa kasar wadda ba ta da tashar ruwa zama wata cibiyar kasuwanci da kuma jawo hankalin masu zuba jari, a cewar wani babban jami'in kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Afghanistan Hafiz Zia Ahmad, ya ce "kasar ta dauki matakin amfani da katafariyar hanyar ce a wani bangare na kokarin gwamnatin Taliban na jawo masu zuba jari cikin kasar da ta sha fama da yaki.

"Hanyar kasuwancin CPEC za ta taimaka mana mu zama wani bangare a shirin samar da ababen more rayuwa na BRI da kuma kawo mana wasu ayyuka daban-daban na makamashi da layin dogo da habaka sauran sassan Afghanistan," in ji Ahmad a wata sanarwa da ya yi ta bidiyo a gidan talabijin na kasar, Ariana News.

A makon da ya gabata, mukaddasan ministocin harkokin waje da na kasuwanci a Afghanistan sun kai ziyara birnin Islamabad na Pakistan, inda suka halarci taron tattaunawa na ministocin harkokin waje na kasashen China da Afganistan da kuma Pakistan karo na biyar.

A cewar sanarwa da aka fitar bayan taron, "bangarorin uku sun jaddada matsayarsu wajen amfani da cikakkiyar damar da Afganistan ke da shi a matsayin wata cibiya ta hadin gwiwa ga yankunan."

Sun jaddada aniyarsu ta karfafa hada kai tsakanin kasashen uku a karkashin shirin "Belt and Road Initiative" BRI da kuma ba da dama ga Afganistan ta shiga cikin hanyar kasuwancin ta CPEC, in ji Sanarwar.

Hanyar kasuwanci ta CPEC wani bangare ne na shirin BRI a Beijing kan bunkasa tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli tsakanin Pakistan da China.

An yi ta tattaunawa kan batun shigar da Afganistan da ke karkashin ikon kungiyar Taliban cikin shirin da gwamnatin kasar ta kuduri aniyar amfani da damar wajen mayar da kasar zama cibiyar zirga-zirgar ababen hawa tsakanin yankin Tsakiya da Kudancin Asiya.

Kungiyar Taliban dai ta karbe iko da kasar ne bayan janyewar dakarun NATO da Amurka ke jagoranta daga Afghanistan a watan Agustan 2021.

TRT World