Matatar man fetur dinmu za ta samar da dubban ayyuka ga matasa - Dangote

Matatar man fetur dinmu za ta samar da dubban ayyuka ga matasa - Dangote

An kafa matatar fetur din ne a yankin Ijebu-Lekki da ke Legas kuma tana da fadin kadada 2,635.
Dangote ya ce babban burinsa shi ne biyan bukatun 'yan Nijeriya a fannin albarkatun fetur. Hoto/Getty

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man fetur dinsa da aka bude za ta samar da "dubban" ayyukan yi ga matasan kasar.

Ya bayyana haka ne ranar Litinin a birnin Legas da ke kudancin kasar.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da wasu shugabannin kasashen Afirka ne suka jagoranci bikin bude matatar man.

Hamshakin attajirin ya ce matatar man za ta samar da "gagarumin" aikin yi ga "dubban daruruwan" matasa 'yan Nijeriya.

Ya ce a watan Yuni za su soma fitar da man fetur da sauran albarkatunsa.

Dangote ya ce “Bayan wannan biki na yau, babban burinmu shi ne mu hanzarta samar da man fetur da dangoginsa domin tabbatar da cewa a wannan shekarar mun biya bukatun kasar nan ta fannin albarkatu masu inganci.”

Ya kara da cewa “mun sha alwashin gudanar da wannan kamfani ta hanyar bin ka'idojin kasashen duniya, da kuma yin la'akari da bukatar kare muhalli, don haka ne muka dauki tsauraran matakai na tabbatar da lafiya.”

A nasa jawabin, Shugaba Buhari ya jinjina wa Aliko Dangote bisa kafa mamatar man, yana mai cewa matakin zai bunkasa tattalin arzikin kasar da ma wasu kasashen Afirka.

Shin matatar man Dangote za ta kawo karshen matsalar fetur a Nijeriya?

Nijeriya na cikin manyan kasashen da suka fi arzikin albarkatun fetur, amma ta dade tana fama da wahalar mai.

Masana sun ce matatar za ta taka rawa wajen magance matsalar man fetur da kasar take fama da ita.

Bayanan da kamfanin Dangote ya fitar sun nuna cewa matatar ita ce daya tilo da ke da rariya mafi girma a duniya da za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kullum.

Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da matatar man:

Matatar man Dangote za ta samar da mai fiye da wanda Nijeriya ke bukata Hoto/Bashir Ahmad/Twitter

  • Matatar ita ce daya tilo mafi girma a duniya da za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kullum.
  • Tana da tankuna 177 da za su iya daukar mai lita biliyan 4.742
  • Akwai injin samar da hasken lantarki mai karfin metawat 345 da ke samar mata da wuta
  • An horars da matasa injiniyoyi 900 a kasashen waje game da ayyukan tace mai don matatar
  • Tsarin ginin matatar ya cika sharudan Bankin Duniya da Hukumar Kula Da Muhalli ta Amurka da takwarorinta na Turai

TRT Afrika