Farashin mai ya yi kasa a sakamakon tsaikon  da tattalin arzikin China ya samu

Farashin mai ya yi kasa a sakamakon tsaikon  da tattalin arzikin China ya samu

Masu samar da kayayyaki na tsammanin sakamakon rage fitar da albarkatun mai daga Saudiyya a watan Yuli.
Karyewar danyen mai na durkusar da kasashe da suka dogara da shi don samun kudaden shiga. Photo: AA

Farashin danyen mai ya sauka a ranar Litinin, a lokacin da alkaluma ke nuna gwagwarmayar tattalin arzikin da China wacce ta fi kowacce kasa shigar da man ke fuskanta.

A safiyar Litinin ana sayar da ganga na danyen mai samfurin Brent kan $76.11, wanda ya fadi da kaso 0.65 kasa da farashin da aka rufe kasuwar a yammacin Juma’ar makon da ya gabata.

Haka zalika an yi cinikin man samfurin West texas kan dala 71.5 kowacce ganga, inda shi ma ya fadi da kaso 0.59 kasa da yadda aka rufe kasuwar a yammacin Juma’ar makon jiya.

Farashin man na faduwa a lokacin da alkaluma ke nuna cigaban tattalin arzikin China na tafiyar hawainiya, da kuma tsaiko a kokarin da take na farfado da tattalin arzikin nata.

Hukumar Kididdiga ta China ta bayyana cewa kamfanonin China ba su samar da kaya yadda ake tsammani ba, inda hakan ya habaka da kaso 3.5 a watan Mayu, kasa da kaso 5.6 da aka shaida a watan Afrilu.

Sakamakon fargabar bukatar man, matatun mai a China sun yi aiki sama da yadda aka tsammata inda suka kara yawan aikin da kaso 15.4 a watan Mayu idan aka kwatanta da watan Mayun 2022.

Tsoron bukatar man na ci gaba

Amma kuma, akwai tsoron yiwuwar durkushewar tattalin arzikin kasashen Yamma, a lokacin da manyan bankuna na duniya suke kara yawan kudin ruwa da ke janyo matsala a kasuwanni.

A makon da ya gabata, Gwamnan Bankin Amurka Cristopher Waller a yayin wani taron tattalin arziki a Oslo, Norway ya bayyana cewa Baitilmalin Amurka na sanya idanu kan matsaloli a bankunan Amurka don auna bukatar kara kudin ruwa.

A taronsu na karshe da aka kammala a ranar Laraba, Bankin ya daidaita farashin kudaden kasa, wanda wannan ne karo na farko da farashinsu bai daga ba tun watan Janairun 2022.

Tun farkon shekarar 2023, batun rage ma’aikata a kamfanoni na ta yamutsa hazo, wanda hakan ya shafi mutum 140,000 a Amurka.

Wannan matsala ta yi illa ga sashen sadarwar wayoyin hannu da fasahar sadarwa da samar da motoci da bangaren masu sayar da kaya daya-daya.

Sabanin yadda aka tsammata, karuwar samar da danyen man masu samar da kayayyaki a Amurka da ta fi kowacce kasa sayen danyen man, na nuni da karancin bukata.

Ma’ajiyar man syaarwa a Amurka ta karu da ganga miliyan 7.9 a mako guda zuwa zuwa 9 ga Yuli, kamar yadda alkaluman da aka fitar daga Hukumar Bayanai Kan Makamashi suka bayyana a ranar Larabar da ta gabata.

Karuwar mai a ma’ajiyar ya ci karo da hasashen da Cibiyar Man fetur ta Amurka ta yin a za su ragu da ganga miliyan 1.3.

Bukatar gas ma ta raguwa a makon da ya gabata, a lokacin da ma’ajiyar mai suka karu da ganga miliyan 2.1.

Masu zuba jari na jiran Saudiyya ta rage yawan man da take fitarwa a watan Yuli.

Kasar mai jagoranci a OPEC ta bayyana za ta sake rage yawan man da take fitarwa da ganga miliyan daya a watan Yuli, baya ga ganga dubu dari biyar da ta rage a farkon watan jiya.

Kungiyar OPEC ta bayyana akwai yiwuwar kara wa’adin na Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.

AA