Wata sabuwar doka da Tarayyar Turai ta fitar na da manufar hana amfanin gona da noman su ke janyo kwararowar hamada shiga kasuwannin Turai.

Manoma na ta gyara gonakinsu a Liberia don samar da wajen shuka cocoa kuma suna kai waken cocoa din zuwa kasar Côte d'Ivoire mai makota da kasar, wanda hakan ke dakile kokarin Turai na yaki da kwararowar hamada, kamar yadda sakamakon binciken wasu masu rajin kare tsirrai ya nuna a ranar litinin.

Wata doka da Tarayyar Tura ta amince da ita wadda kuma za ta fara aiki a karshen shekarar nan na da manufar hana amfanin gona da manoman suke illata sakamakon kwararowar hamada a duniya shiga kasuwannin Turai.

Dokar ta kuma shafi albarkatun gona irin su coffee, nama da waken suya, amma ana ganin cocoa na matakin farko na gwajin dokar, inda ake bukatar kamfanoni su bayyana yadda suke noman ta hanyar tabbatar da cewa ba su janyo lalata dazuka ba.

A yayin da kokarin da ake yi ya mayar da hankali ga bin diddigin yadda ake samar da cocoa da fitar da shi kasashen waje, kungiyar kare dazuka ta Ivory Coast ta gano manoman kasar na tafiya zuwa Liberia don samun kasar noma.

Lalata dazuka cikin sauri

"Matsala ce da take ta bunkasa cikin sauri, kuma za ta ci gaba da yin saurin," in ji Bakary Traore, daraktan zartarwa na IDEF kuma babban marubucin binciken, yayin tattaunawa da Reuters.

Ko dai a magance kwararowar masu noman cocoa daga Ivory Coast zuwa Liberia, to za a kai ga yanayin da za a karar da dazukan Liberia kamar yadda aka yi wa na Ivory Coast, in ji Traore.

Ivory Coast da ke kan gaba a duniya wajen noman cocoa, na fuskantar matsaloli da dama, ciki har da saurin yanayi, tsufan bishiyu da cututtuka da ke dakile habakar kayayyaki.

Fataucin cocoa

A 2022 kadai Liberia ta yi asarar hekta 15,000 na dazukanta, kamar yadda kungiyar Global Forest Watch da ke snya idanu wajen kare tsirrai ta bayyana.

Hukumar Gandun Daji ta Liberia ta fada wa Rueters cewa suna sane da kwararowar manoman daga Ivory Coast a shekaru ukun da suka gabata, kuma suna shirin daukar mataki.

Majalisar Coffee da Cocoa - Hukumar Kula da Noman Cocoa ta Ivory Coast - da Tarayyar Turai ba su mayar da martani nan da nan ga bukatar cewa wani abu da Reuters ta nema ba.

Matsalar da ke yaduwa

IDEF ta gudanar da nata binciken a tsawon watanni shida a wasu kauyuka da tauraron ɗan'adam ya haska ya gano suna fama da mummunar asarar dazuka da kwararowar habada.

Amma Traore ya bayyana cewa matsalar ta fi yawaita a yankunan kan iyaka da ke tsakanin kasashen biyu na Yammacin Afirka. IDEF sun gano 'yan gudun hijira sun fara shuka cocoa a yankunan da aka baiwa 'yan kasar Liberia su yi noma a 2018.

A yayin da shuke-shuken suke matakin girma, masu binciken sun gano wasu tuni suka fara shuka cocoa.

Duk da batun kamfanoni na cewa sun iya samun damar gano asalin inda ake fito da kayan, kuma ana daukar cocoa din da aka noma a Liberia a kai si Ivory Coast tare da gauraya su a can.

TRT Afrika