Tsarin hydroponics dadadden kimiyya ce da ake yin shuke-shuke har su girma cikin tushen sinadarin ruwa maimakon ƙasa. / Hoto: Reuters  

Daga Firmain Eric Mbadinga

Farin cikin shiga harabar gida ko kicin ko dai jingina ta jikin taga don tsinko ganyayyaki kai tsaye da kuma ƙara wa abinci ɗandano na kayan lambun da aka shuka a cikin gida, abu ne da ya kasance tamkar "mafarki".

Sai dai a birane da garuruwa da suka cika maƙil da gidaje waɗanda mafi akasarinsu ƴan ƙanana ne, tsarin ya zama tamkar wani alatu da sai wanda ya dace ne kawai zai iya yi.

Shin ana iya cewa, tsarin gargajiya na shukar lambu a cikin gida, ba tare da dogaro kan ƙasa ba, ya bayyana alfanunsa ? E ko a'a.

Hydroponics, ko kuma daɗɗaɗen tsarin kimiyyar shuke-shuke ta cikin ruwa mai yawa maimakon ƙasa, na sake dawowa a matsayin tsarin da ake iya cimmawa da kuma shukar lambu mai ɗorewa a cikin yanayin rayuwa ta zamani.

A Afirka, yanzu ana amfani da hydroponics a matsayin tsari mai inganci kuma mai amfani wanda ke bai wa mutum damar shuka sabbin kayan amfanin gona a cikin kicin ko falo, ba tare da la’akari da yanayi ko gona ko kuma wuri ba.

Meschac Agbeanon, wani ƙwararre a fannin aikin gona da ke garin Cotonou na ƙasar Benin, na daga cikin sabbin ƴan kasuwa kayayyakin lambu da masu tasowa da ke amfani da tsarin hydroponics wajen bunƙasa harkokin kasuwancinsa.

"Gonakin birane da lambun tsaye da koren rufi da kuma gidajen shuke-shuke suna ba da damammaki wajen noman cikin gida da rage zirga-zirga da kuma ƙara kusancin ayyukan noma ga mazauna birane,'' kamar yadda Agbeanon ya shaida wa TRT Afrika.

Agbeanon ya bayyana cewa, kamfaninsa da ke samar kayayyaki da ayyukan noma a Benin, ya kware wajen nemo damammaki ga kananan masana'antu.

Kamfanin yana gudanar da bincike mai zurfi game da kasuwar noma da kuma nazari kan buƙatu da yanayi don samarwa abokan cinikinsa dabaru da za su iya bi.

An yi imanin cewa, an fara yin amfani da tsarin shuga na hydroponics ne a kogin Nilu na kasar Masar kimanin shekaru 4,000 da suka wuce. Hoto: Meschac Agbeanon

Tsarin shuga na hydroponics mai kyau na haɗa wasu tire da tukwane da kayayyaki da za su taimaka wajen tsare shukar har lokacin da za su girma, da kuma kwanduna masu ƙananan huji da za su na rage ruwa da samar da iskar Oxygen da kuma haɗin sinadarin ruwa (wanda aka haɗa sinadarai iri daban-daban a ciki).

Masu amfani da tsarin hydroponics sun tabbatar da ingancinsa, baya ga magance wasu matsaloli da suka shafi aikin lambu na gargajiya, kamar kwari da cututtuka da kuma cire ciyayi mara kyau.

Da tsarin hydroponics, za a iya shuka ganyayyaki iri daban-daban har ma da 'ya'yan itatuwa cikin yanayi mara cututtuka da kwari.

Dadadden Tarihi

Tarihi ya danganta tsarin hydroponics da daɗaɗɗen dabarun noma a Afirka, musamman daga ƙasar Masar.

An yi imanin cewa, an soma amfani da tsarin ne a kogin Nilu na Masar kimanin shekaru 4,000 da suka wuce.

Tun kafin Dr. William F. Gericke na Jami'ar California ya kirkiro da kalmar "hydroponics" a karni na 20, aka yi imanin cewa tun a zamanin baya ƴan Masar suka kirkiro da tsarin shuka mara ƙasa.

Suna noma ne ta hanyar amfani da ruwan kogin Nilu mai cike da sinadarai masu gina jiki, tsarin da ke kama da hydroponics, wadda ta haɗa kalmomi biyu- ''hydro'' ma'ana ruwa da kuma kalmar girkanci ''ponos,'' ko aiki.

Ambaliyar ruwa a kogin Nilu da ake yi a kowace shekara ya samar da yanayi mai kyau a bakin kogin, da ke samar da tsarin ruwa da zai taimaka wa tsiran da aka shuka su girma ba tare da sun taba ƙasa kai tsaye ba.

An yabawa Dr Gericke bisa ga kokarinsa na fadada gwaje-gwajen da ya yi na amfanin gona da kasuwanci kayayyakin lambu da ke girma a waje.

Ya samar da wani tsarin shuka na tumatur mai tsayin ƙafa 25 a bayan gidansa ta hanyar amfani da ruwa da sinadarai kadai. Sakamakon gwajin nasa ya haifar da ƙarin bincike a fannin, wanda ya samar da tsarin hydroponics na zamani.

Masanin ilmin kiwo a Jamus Julius von Sachs da kuma masanin aikin gona Wilhelm Knop ne suka gabatar da tsarin farko da ake amfani da ruwa wanda ya dace da yanayin shuka ba tare da amfani da ƙasa ba.

Zaɓi mara cutarwa

"Akwai tsarin hydroponic da dama, kamar haɗin sinadarai abinci, da sinadarin fim, da wick, da kuma irin shuka ta cikin tukunya, Kowanne daga ciki na da alfanu da rashin alfanunsa,'' in ji Agbeanon.

Ya kuma ƙara da cewa ''Zaɓin ya dogara ne ga irin amfanin gonar da ake so da matsalar rashin wadataccen wuri da kuma albarkatun da ake da su a lokacin".

A kasar Habasha, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suna yawan karfafa gwiwar mutane kan su yi amfani da tsarin hydroponics, a daidai lokacin da aka shafe shekaru sama da talatin ana fama da fari a kasar.

“Kungiyoyin mu sun aiwatar da wannan aikin a yankin Waghimra, inda ake fama da karancin abincin kiwo na dabbobi wanda ke zama daya daga cikin manyan matsalolin da al’umma ke fuskanta, waɗanda kashi 90 cikin 100 suke dogaro kan kiwon dabbobi da kuma noma,'' a cewar wani sakamakon bincike na 2020 da wata kungiya mai zaman kanta Action Against Yunwa ta fitar.

Baya ga ganyayyaki da sauran kayan lambu, ana iya amfani da tsarin hydroponics wajen dasa ciyawar kiwon dabbobi./Hoto: Meschac Agbeanon

A wani rahoto da ya wallafa a 2021, Bankin Duniya ya lissafa tsarin hydroponics a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan da za a iya amfana da su wajen yaki da talauci da rashin aikin yi da kuma sauyin yanayi.

Rahoton ya kuma tabo batun matsalar kwari da hydroponics don karfafa ayyukan noma na gargajiya.

Yayin da za a iya amfani da tsarin hydroponics wajen yin noma mai yawa da kuma shuga tsirai da ke girma a ƙasa, masana kimiyya sun gano cewa wasu nau'in tsirai suna iya bunƙasa ta hanyar amfani da waɗannan dabaru.

Ganyayyakin sun haɗa da latas, waɗanda aka fi amfani da su wajen haɗa salad, da Kayan lambu irin su alayyahu da Kale suma sun dace da tsarin hydroponics.

Kazalika ana amfani da tsarin wajen shuka ganyayyaki masu kamshi kamar su Basil da faski da chives da coriander da mint da dai sauransu.

TRT Afrika