An samu jinkiri tun farko wurin gina matatar man Dangote wadda aka soma ginawa a 2013. Hoto/Bashir Ahmad/Twitter

Daga Abdulwasiu Hassan

Matatar mai mafi girma a Afrika kuma daya tilo mafi girma a duniya za a kaddamar da ita a Nijeriya a ranar Litinin wadda shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari zai kaddamar.

Matatar mai ta Dangote, wadda aka gina a birnin Legas, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka Aliko Dangote ne ya gina ta, kuma za ta iya tace gangar danyen mai 650,000 a duk rana.

Wasu suna ganin wannan matatar za ta iya kawo sauyi a fannin man fetur a Nijeriya da kasashen makwabta.

Duk da cewa tana daga cikin kasashen da ke kan gaba wurin samar da man fetur a duniya, Nijeriya ta dogara ne kan shigar da man fetur din da aka tace domin amfanin cikin gida tsawon shekaru, matatu hudu na kasar ba sa aiki yadda ya kamata.

Wannan ya jawo babban gibi a samar da fetur a Nijeriya. Kasar ta kashe sama da dala biliyan 12.44 wajen shigar da man fetur a 2022 kadai, kamar yadda babban bankin Nijeriya CBN ya tabbatar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya saka hannu kan wata doka a 2021 domin yin garambawul kan bangaren mai na Nijeriya. Hoto/Fadar Shugaban Kasa

Dangote ya yi alkawarin cewa matatar man za ta rinka tace isasshen mai da Nijeriya za ta yi amfani da shi kuma har a fitar.

A wata sanarwa da aka fitar kafin kaddamar da matatar, rukunin kamfanonin Dangote, wanda shi ne mamallakin matatar man, ya bayyana cewa matatar na da “tankuna 177 da za su iya daukar lita biliyan 4.742.”

Ya ce duk da cewa an yi matatar ne domin biyan bukatun Nijeriya na danyen man fetur 100 bisa 100, za ta iya tace sauran danyen mai daga Gabas ta Tsakiya da kuma danyen man Amurka.

“Idan tana aiki yadda ya kamata, matatar za ta iya samar da man da ake bukata a Nijeriya da kuma wanda za a fitar,” kamar yadda kamfanin ya sanar.

Nijeriya, wadda ke da jama’a sama da miliyan 200, na amfani da kimanin litar mai miliyan 60 a kowace rana, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

A tsawon shekaru, Nijeriya tana samar da gangar danyen mai miliyan biyu a duk rana haka kuma tattalin arzikinta ya dogara ne kan kudin da fetur din ke samarwa.

Wannan na nufin duk wani babban sauyi ga bangaren man fetur – mai kyau ko mara kyau – yana da tasiri kan tattalin arzikinta.

Ana yawan samun karancin man fetur a Nijeriya. Hoto/AP

Akasari ana samun man ne daga yankin Neja Delta da ke kudancin Nijeriya amma a shekarun baya bayan nan, an gano man fetur a arewacin kasar kuma ana sa ran soma cin moriyarsa nan ba da jimawa ba.

Komai-da-ruwanka

An gina matatar ne a Lekki Free Trade Zone da ke Legas, wuri ne a baya da ke da ruwa kwance amma an cike shi da kasa.

An soma shi ne a matsayin wani dan karamin aiki a 2013 amma daga baya aka fadada aikin a 2016.

An yi matatar ne a fili mai girman kadada 2,635, inda ke da akwai wurin tace mai da kuma wurin sarrafa sinadaren da ake samu daga fetur din da kuma takin zamani da tashar ruwa da kuma tashar samar da lantarki.

An ta samun shakku kan aikin matatar da farko inda wasu masu sharhi suke ganin cewa yanayin Nijeriya ba zai bari ba da kuma yadda matsalar tsaro ke kara kamari da kuma karuwar ‘yan bindiga da ke kai hari kan bututan mai.

Sai dai Aliko Dangote, ya rufe kunnuwansa da idanuwansa ya ci gaba da wannan aikin inda ya ce wannan aikin matatar zai maggance matsalolin da kasar ke fama da su daga ciki har da na tsaro.

Matatar man Dangote za ta samar da mai fiye da wanda Nijeriya ke bukata Hoto/Bashir Ahmad/Twitter

“Da zarar ka samar da ayyukan yi, za a samu karancin mutanen da ke zuwa kai hare-hare,” kamar yadda Aliko ya bayyana bayan da ;yan jarida suka tambaye shi ko harin da ‘yan bindiga ke kaiwa a Nijeriya zai kawo cikas wurin aikin matatar mansa.

‘Ba Nijeriya kadai za ta amfana ba’

Kamfanin Dangote ya bayyana cewa matatar man fetur din za ta iya tace danyen man fetur daga cikin Nijeriya da kuma wajen kasar.

Ana kuma sa ran kamfanin zai rinka fitar da wani kaso na man da ya tace zuwa kasashen waje.

Idan matatar ta soma aiki, akwai yiwuwar kasashen Afirka za su rage kudin da suke kashewa wurin shigo da man da aka tace daga kasashen waje, kamar yadda Idakolo Gabriel Gbolade ya bayyana, wani masani kan harkokin kudi a Nijeriya.

Dalilin hakan shi ne a halin yanzu ba za su rinka shigar da mai kasashensu daga wuri mai nisa ba.

Amma har yanzu ba a sani ba ko zuwa yaushe matatar za ta soma tace mai da ya kai ganga 650,000 a duk rana. Mista Gbolade wanda shi ne jagoran kamfanin Capital Management Firm SD&D ya shaida wa TRT Afrika cewa matatar man za ta iya “tabbatar da Nijeriya ta samu dala biliyan 10 a duk shekara daga fitar da man” kuma zai taimaka wa kasar matuka sakamakon zai rage mata gibi.

Ya bayyana cewa wannan zai taimaka wurin kara daga darajar kudin kasar wato Naira. Gabannin kaddamar da aikin, kamfanin mai na Nijeriya NNPC ya aika da gangar danyen mai 300,000 domin soma aiki, kamar yadda wani mai taimaka wa shugaban Nijeriya ya bayyana.

Shin matatar za ta iya kawo saukin farashin fetur?

An soma gina matatar man Dangote a 2013 domin kammala aikinta a cikin shekara uku, inda aka yi kiyasin cewa za a kashe dala biliyan takwas.

Sai dai ba a soma ginin ba sai a 2016 inda aka sake samun jinkiri sakamakon matsalolin tattalin arziki da kuma annobar korona.

Karancin man fetur ya shawo jawo layin man fetur a Nijeriya. Hoto/AA

Kudin da za a kashe wurin gina matatar ya karu zuwa dala biliyan 19 sakamakon sauyin tattalin arziki.

Duk da an shafe shekaru ana jinkiri, an kammala matatar a yanzu inda ake sa ran za ta samar da isashen mai ga Nijeriya.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka, Akinwumi Adesina bai boye jin dadinsa ba a lokacin da ya kai ziyara matatar.

Masanin harkokin kudi Gbolade ya ce yana kyautata zaton wannan aikin zai samar da sama da ayyuka 100,000 kai tsaye da kuma wadanda ba kai tsaye ba.

Ba a sani a fili ba ko za a samu saukin kudin man fetur idan wannan matatar ta soma aiki.

Kaddamar da matatar na zuwa ne a lokacin da hukumomin Nijeriya ke shirin cire tallafin man fetur wanda zai sa ‘yan kasuwa su sayar da fetur kan farashin da suka yanke.

Wannan matakin ya jawo karin farashin man fetur a Nijeriya.

Mai sharhi Gbolade na ganin duk da kalubalen da ke kan tattalin arzikin Nijeriya, talakan Nijeriya zai karu daga matatar man idan tana aiki.

TRT Afrika