Mutane sun yi ta murna da goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulkin a kan titunan birnin Libreville. / Hoto: Reuters

Daga Sylvia Chebet

Gabon ta zamo kasar Afirka ta baya-bayan nan da ta gamu da juyin mulki bayan da sojoji suka hambarar da Shugaba Ali Bongo daga karagar mulki a ranar Laraba da safe.

Sa'o'i bayan nan ne saisojojin suka nada shugaban dakaru na musamman da ke tsaron fadar shugaban kasa, Janar Brice Clotaire Oligui Nguema, a matsayin sabon shugaban kasar.

Sojojin sun yi juyin mulkin ne jim kadan bayan da aka ayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar mai cike da ce-ce-ku-ce, inda zai yi tazarce karo na uku da wa'adin shekaru bakwai, bayan kama mulki a shekarar 2009.

Babban dan hamayyar Bongo a zaben shi ne Albert Ondo Ossa, wanda sauran 'yan hamayya da dama da suka tsaya takarar suka hade kai suka goya masa baya, kwanaki kadan kafin zaben.

'Yan hamayyar sun yi watsi da sakamakon zaben suna cewa an tafka magudi. Su ma masu sa-ido kan zaben sun ce zaben ba sahihi ba ne, saboda an toshe intanet kuma an haramta wa kafafen watsa labarai na kasashen duniya yin rahoto kan zaben.

'Mutane kadan ne suka tsammaci faruwar hakan'

Duk da korafe-korafen da aka samu a kan zaben, hambarar da Bongo da aka yi jim kadan bayan sanar da sakamakon samun nasararsa a zaben, ya zo wa mutane da dama da ba-zata, a cewar wasu masu sharhi kan al'amuran siyasa.

"Mutane kadan ne suka tsammaci faruwar juyin mulki kan sakamakon zaben. Kuma hakan abu ne da ya kamata ya faru tun da dadewa don kawo karshen dogon lokacin da zuri'ar Bongo ta dauka tana mulki a Gabon," a cewar Remadji Hoinathy, wani babban mai bincike a Cibiyar Ilimin Tsaro ta Afirka.

Sojoji sun yi fareti a birnin na biyu mafi girma a Gabon bayan hambarar da shugaban kasa. Hoto: Reuters

Ali Bongo Ondimba mai shekara 64 ya yi mulki har karo biyu tun bayan zamansa shugaban kasa a 2009, bayan mutuwar mahaifinsa, Omar, wanda ya shafe shekara 42 yana mulki.

Da gaggawa

Akwai zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin iya shugabanci da ake yi wa mulkin zuri'ar Bongo, wacce ta shafe tsawon shekara 56 tana mulkin kasar ta yankin Tsakiyar Afirka mai arzikin man fetur.

“Lokacin da aka yi juyin mulkin jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben, da kuma irin yadda nan da nan sojojin suka cimma hakan, sun nuna cewa dama an tsara yin hakan tun tuni," a cewar Joseph Siegle, daraktan bincike a Cibiyar Nazari kan Tsare-Tsare a Fannonin cigaba ta Afirka.

Ba wannan ne karo na farko da sojoji suka so yi wa Ali Bongo juyin mulki ba. A watan Janairun 2019, wata tawagar sojoji sun yi kokarin yi masa juyin mulki amma nan da nan aka dakile abin, aka fi karfinsu. Shekara biyar bayan nan, sai a yanzu sojoji suka yi nasarar kawar da shi daga mulkin.

Ali Bongo ya nemi da abokansa a fadin duniya su kai masa dauki a yayin da aka yi masa daurin talala. Hoto: Others

Sojojin sun yi wa Bongo daurin talala kuma an kama mambobin majalisar ministocinsa da dama. Juyin mulkin ya zo bayan da ya gamu da shanyewar barin jiki a shekarar 2018, rashin lafiyar da ta sa har yake tafiya da sanda.

Arziki da talauci

Ana zargin iyalan shugaban kasar da cin hanci da rashawa tare da kanainaye dukiyar kasar su kadai, ta yadda ba ta kai wa ga talakawa a kasar da al'ummarta ba ta wuce miliyan 2.3 ba.

Kasar, wacce Faransa ta raina, mamba ce ta kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta OPEC. Amma mutane kalilan ne ke amfana da arzikin man nata. Kudin shigar da Gabon ke samu daga fetur ya kai dala bilitan shida a shekarar 2022, a cewar Hukumar Ba da Bayanai kan Makamashi ta Amurka.

A hannu guda kuma, akwai iyalan zuri'ar Bongo tara da ake bincika a Faransa, wasu kuma an fara binciken su kan almubazzarancu, a cewar Sherpa, wata kungiya ta Faransa mai zaman kanta da ke wayar da kai kan tsare gaskiya.

Masu bincike sun alakanta iyalan da batun mallakar wasu kadarori na fiye da dala miliyan 92 a Faransa, wadanda suka hada da katafaren gidaje a birnin Nice na Faransa, in ji kungiyar.

Sannan. kusan kashi 40 cikin 100 na 'yan Gabon da ke tsakanin shekara 15 zuwa 24 ba su da ayyukan yi, in ji wani bincike na Bankin Duniya.

'Yan Gabon da dama sun ce sun yi farin ciki da juyin mulkin. Hoto Reuters

“A yau babu abin da za mu yi da ya wuce farin ciki," kamar yadda wani dan Gabon John Nze ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP, inda ya kara da cewa: “Yanayin da aka shiga a kasar a baya ya durkusar da kowa. Babu ayyukan yi. Idan dai ka ga 'yan Gabon na murna, to saboda sun sha wahala ne a karkashin mulkin zuri'ar Bongo."

Gabon ce kasa ta shida a Tsakiyar Afirka da Yammacin Afirka da ta gamu da juyin mulki tun shekarar 2020.

Juyin mulkin sojin ya faru ne wata daya bayan da aka yi juyin mulki a Nijar, wanda sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Jerin juyin mulkin sun sanya damuwa kan shugabanci a yankunan Afirka, inda shugabannin yankunan ke ta kokarin shawo kan lamarin.

TRT Afrika