Shugaba Ali Bongo ya yi fama da rashin lafiya a kwanakin baya. Hoto/Getty Images

Rikicin siyasa da ake kai a halin yanzu a Gabon ya samo asali ne bayan an sanar da Ali Bongo Ondimba mai shekara 64 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar 26 ga watan Agusta, a daidai lokacin da ake neman wa'adi na uku.

Mista Bongo ya doke abokin hamayyarsa Albert Ondo Ossa tun a zagayen farko na zaben kasar, inda ya samu kaso 64.27 cikin 100 na kuri'un kasar, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta sanar.

Dan siyasar wanda yake son zuri'arsa ta ci gaba da mulkin kasar, zuri'ar tasa ta soma mulkin ne shekaru 55 da suka gabata a Gabon.

Ali Bongo ya zama shugaban kasa a 2009 bayan rasuwar mahaifinsa a 2009, Omar Bongo Ondimba wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 42, tun daga 1967.

Sai dai bayan shekara 14 a matsayinsa na shugaban kasa, wa'adi na uku na Bongo na tangal-tangal, bayan da wasu sojojin kasar a ranar Laraba da sassafe suka sanar da kwace iko da gwamnatin kasar.

Hawa kan mulki

Bayan rasuwar mahaifinsa a 2009, Ali Bongo ya zama shugaban kasa inda a 2011 ya yi nasara a zaben shugaban kasar wanda aka gudanar duk da cewa an yi ta zarge-zarge na magudin zabe a 2011.

Kuri'un da aka sake kirgawa sun saka Bongo a gaba da kashi 41.79 na kuri'un da aka kada. A 2016, ya sake yin nasara a zaben kasar inda ya sha da kyar.

A lokacin mulkin mahaifinsa, Bongo ya yi aiki a matsayin ministan harkokin wajen kasar tun daga 1989 zuwa 1991, kafin daga nan ya wakilci garinsu Bongoville a matsayin dan majalisa mai wakiltarsu tsawon shekara takwas, tun daga 1991-1999.

Bayan haka, sai aka sake nada shi ministan tsaro, inda ya yi shekara 10 kan mukamin, daga 1999 zuwa 2009 a lokacin da mahaifinsa ya rasu.

Iyalan Bongo

Iyalansa sun koma addinin Musulunci a 1973, wanda wannan sauyi ne da ya sauya sunayensu. An haife shi a matsayin Alain Bernard Bongo a ranar 9 ga watan Fabrairun 1959, a Congo Brazzaville, inda daga baya ya koma Ali Bongo Ondimba.

Mahaifinsa a baya sunansa Albert Bernard Bongo amma daga baya ya sauya sunansa zuwa Bongo Ondimba.

Omar Bongo ya yi mulki tsawon shekara 42 tun daga 1967 zuwa 2009. Hoto/AFP

A lokacin da Bongo yake dan shekara tara, an tura shi makarantar kudi a Neuilly da ke Faransa.

A 1978, Bongo ya yi album na wata waka mai taken 'A Brand New Man', wanda Charles Bobbit ya jagoranta, kuma shi ne manajan James Brown, inda 'yan amshin wakokin James Brown aka ji su a wakar tasa.

Bongo ya karanta shari'a inda ya kammala karatunsa daga Jami'ar Pantheon Sorbonne da ke Paris a 1978, inda ya samu digirinsa na biyu daga Jami'ar Wuhan da ke 1980.

Bongo ya auri matarsa ta farko Sylvia Valentin a 1989, wadda 'yar Faransa ce inda suke da 'ya'ya hudu.

Sai ya auri matarsa ta biyu Inge Collins daga Los Angles da ke Amurka a 1994 amma Collins ta nemi ya sake ta a 2015.

Tafiya mai tsawo

Ali Bongo ya shiga siyasa a 1981, a lokacin d aya shiga Jam'iyyar Gabonese Democratic Party, (PDG). A shekarar 1983, an zabe shi a kwamitin PDG inda ya zama daya daga cikin majalisar ministocin mahaifinsa.

Bayan nan ne sai ya zama wakili na musamman na mahaifinsa inda rike mukamin Babban Mataimaki na Musamman na kasar daga 1987 zuwa 1989.

Wani sauyi da aka yi wa kundin tsarin mulki na kayyade shekaru domin zama minista zuwa shekara 35 ya sa ya tafi.

A lokacin da yake wakilar kasar a Bongoville a majalisar kasar, ya zama Shugaban Majalisar Harkokin Musulunci na Gabon a 1996, da kuma Ministan Tsaro a 1999.

Bongo ya yi fama da shanyewar rabin jiki a Oktobar 2018, a lokacin da yake halartar wani taro a Riyadh da ke Saudiyya.

Sai dai bayan Janairun 2019, ya sake fama da wata matsalar. An yi yunkurin kifar da gwamnatinsa, sai dai lamarin ya gagara. Daga baya ya sanar da cewa zai sake takara a 2023

An gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Agusta inda hukumar zaben ta sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben a ranar 30 ga Agusta.

Sai dai sojoji sun sanar da cewa sun soke zaben, tare da kwace iko da gwamnatin kasar da kuma masa daurin-talala.

TRT Afrika