Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya ta ce ya zama dole a yi gyara a kudaden Aikin Hahajjin bana saboda karyewar kudin kasar. / Hoto: AA

Daga Abdulwasiu Hassan

Nazif B. Aliyu na daya daga gama-garin 'yan Nijeriya da batun tafiyar su Aikin Hajjin bana ta shiga rashin tabbas tun makon da ya gabata, bayan sanarwar da aka fitar a hukumance na kara yawan kudin saboda sauyar farashin canjin kudaden waje.

Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) a wani sako da ta fitar ta shafin X ta bayyana cewa maniyyatan da suka biya Naira miliyan 4.9 a baya, za su biya karin Naira miliyan 1.9 (kusan $1,461) nan da 28 ga Maris din da ya gabata.

A bangaren Nazif, farin cikin da yake da shi na tafiya kasa mafi tsarki ya dusashe da damuwa kan yadda zai iya nemo wadannan kudade cikin kankanin lokaci. Aikin Hajji daya daga cikin shika-shikan Musulunci ne.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Zuwa Hajji kiran Allah ne. Ko kana da kudin, za ka iya zuwa ne idan Allah Ya kira ka. Ya zuwa yanzu, ban sani ba ko zan fasa ko zan iya biya karin kudaden. Saboda ban ma taba raya hakan za ta faru ba."

Maniyyata aikin Hajji na cikin fargabar gaza zuwa kasa mai tsarki bana. Hoto/Reuters

A yayin da dambarwar da maniyyata irin su nazif ta karade shafukan sadarwa na intanet, da alamu mahukunta sun dan sassauto.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana za ta biya karin kudin ta hanyar bayar da tallafi. Wasu jihohi ma sun bi sawun tallafawa maniyyatan.

Aliyu A. Ali, wanda ya biya kudin Aikin Hajji ta hanyar adashen gata, ya ce ya samu sako daga NAHCON kan duk wanda ya biya kudin Aikin Hajji ta wannan hanyar ba zai biya karin wasu kudade ba.

Zuwa Aikin Hajji Wajibi ne a kan dukkan Musulmin da yake da iko: Hoto/Reuters

Hukumar ta tabbatar da wannan ta wani sako da ta fitar ta shafin X da ke cewa "Zuwa ga maniyyata karkashin Asusun Aikin Hajji (HSS), NAHCON ta sanar da cewa babu karin wani kudi ga wadanda aka riga aka karbi kudadensu karkashin tsarin. Hukumar ce za ta cika sauran."

Mataki a kurarren lokaci

A yayin da a yanzu ake ganin kamar an warware rikicin, mutane da yawa na tambayar ko mutane da suke jiran a fara jigilar su zuwa Aikin Hajji sun cancanci a jefa su a cikin damuwar nemo naira miliyan 1.9.

Sheikh Kabiru Gombe, babban jagora a kungiyar Izalatul Bid'ah Wa Ikamatussunah. ya ce a baya wata gwamnati ta bayar da tallafi ga Aikin Hajji, ya kamata a yanzu ma ya zama babu wani bambanci.

"Ba mu taba ganin rikici irin wannan ya shafi maniyyata ba a Nijeriya" in ji Shaikh Gombe a wajen tafsirin Azumin Ramadana a Abuja babban birnin Nijeriya. "Muna kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya goyi bayan maniyyata a wannan lokaci da suke da bukata."

Gwamnan Kano ya ce zai bayar da tallafin Naira 500,000 ga dukkan maniyyatan da suka fito daga jihar.

Ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohi da su bayar da tallafin don tabbatar ba a tursasa wa maniyyata da dama fasa zuwa Ibadar ba.

Aliyu Ali ya tuno da yadda ya ji irin haka a lokacin da ya samu sanarwar da NAHCON ta fitar.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Na ji bacin rai har ta kai ga na kasa bacci. Ina tunanin ta yaya zan hada karin kudin da ake neman, hakan ya dinga sanya min ciwon kai."

Kamar sauran maniyyata, Aliyu Ali ya yi imani da karfin addu'a wanda zai taimake shi a wannan tsaka mai wuya. "Na yanke hukuncin sayar da kadara da kuma addu'ar Allah Ya zaba min mafi alheri. A shirye nake yin duk abin da zan iya, na barwa Allah sauran.

Aliyu da wasu dubban maniyyata, za su samu damar zuwa Aikin Hajjin.

TRT Afrika