Yin zane kai-tsaye gaban masu kallo wata baiwa ce ta musamman da Isaac Chukwu yake da ita.Isaac Chukwu has broken out of the traditional studio setup to paint 'live' within a limited time frame at various events in Ghana.      

Daga Pauline Odhiambo

Yin zane kai-tsaye a gaban masu kallo wata baiwa ce da Isaac Chukwu yake da ita, inda ya yi zarra a tsakanin takwarorinsa a duniyar fasahar zane, musamman yadda yake iya fara zanensa ta baibai.

Lallai fasahar zanen kai-tsaye ta daga darajar Chukwu-Ya yi watsi da yadda aka saba zane a al’ada ta zama a waje daya a yi zane, inda yanzu yake halartar taro ya kuma yi zanen a gaban mutane a cikin qanqanin lokaci a Ghana.

“Zane ta baibai na nufin a fara zanen daga kasa zuwa sama. Ina fara zanen ne daga kafa, sannan in koma sama,” in ji mai zanen wanda ruwa biyu ne tsakanin Nijeriya da Ghana a tattaunawarsa da TRT Afrika.

“Mafi karancin lokacin da na yi zane shi ne minti biyu, inda na zana bangon fostar kudin wakokin fitaccen mawakin gambarar Ghana Sarkodie a wani taron kalankuwa a shekarar 2018.”

Fitaccen jarumin fim na Amurka, Idris Eba, wanda ya kasance a wajen taron wanda ya wakana a Accra ne saya zanen na Chukwu.

Chukwu ya yi wa fitattun mawakan Afirka ta Yamma zane, kamar su Shatta Wale da Stonebwoy da babban forodusan wakokin Nijeriya Don Jazzy da sauransu.

Ya taba yin zane guda tara a jere a wani wajen taron karrama wasu mutane-inda aka ba kowane wanda aka karrama zanen guda daya.

“Na zana Mataimakin Shugaban Kasa Mahamadu Bawumia a wajen wani taron da aka shirya domin karrama shi. Ko kafin a kammala cin abinci, har na kammala zanen,” inji shi.

Abin da ya taso yana sha’awa

Chukwu ya ce kwarewarsa a salon zane ta baibai bai rasa nasaba da dadewa da ya yi yana kallon wasu masu zanen na duniya.

Ya kuma ya kara samun kwarewa ta hanyar kallon wasu masu zanen na kasar Ghana.

Matashin mai shekara 26 yana da sama zane-zane guda 300 a hasashensa, wadanda suka kunshi na fitattun mutane a wuraren bikin zagoyowar ranar haihuwarsu, inda nan ya fi baje-kolin fasaharsa.

Yadda yake yi shi ne, a daidai lokacin da ake cigaba da shagalin bikin, Chukwu- wanda yake kafa allon zanensa inda mahalarta taro za su gani-sai ya fara zana wanda ake taron domin shi.

“Lokacin muna makarantar ban cika kokari sosai ba, amma idan an zo wajen zane-zane, sai abokan karatuna su rika rokona in musu zane-zanen da aka ba mu a darussanmu na kimiyya,” in ji shi.

“A lokacin ne na gane cewa ina da baiwar zane, duk da cewa ban dauke ta da muhimmanci ba.”

Mahaifiyar Chukwu, wadda malamar makaranta ce a makarantar da yake karatu ta sha fama da shi a kan ya mayar da hankalinsa wajen karatu, amma wasanni irin su kwallon kafa da sauransu sun fi dauke masa hankali.

A shekarar 2012 ce da mahaifinsa ya sha fama da jinya ce Chukwu ya fara daukar zane-zane da muhimmanci.

“Bayan mahaifina ya fara fama da shanyewar barin jiki ne na gane akwai bukatar in dage wajen neman kudi a matsayina na babba a gidan domin daukar nauyin mahaifiyata da kannai guda uku.”

Jarumin fim na Amurka Idris Eba ya saya zanen Chukwu a shekarar 2018. Hoto: saac Chukwu

Koyon zane

Kasancewarsa cikin masu kidar fareti na sojojin sakandire ya sa ya fara tunanin shiga aikin soja da zarar ya kammala sakandire, amma ganin irin wahalar da ake sha a wajen zama soja ya sa ya sauya tunani.

Sai ya fara tunanin zama dan wasa, amma malaman bangaren kirkira da fasaha na makarantar sai suka ba shi shawara ya dage da zane-zane.

“Sai na mayar da hankali kacokam ga zane-zanen, inda na dade ina koyon aikin har bayan na kammala sakandire, har na kai ga karantar kasuwancin zane-zane,” in ji shi.

“A Coci na fara zanen kai-tsaye a gaban mutane domin karrama bakin fastocin da suka zo mana. Nakan auna zanen da zan yi ne da masu wakokin yabo, ta yadda a daidai lokacin da suke kammala waka, ni ma na kammala zanen bakon, domin a mika masa.”

A hankali sai Chukwu ya fadada kasuwancin zane-zanensa tare da taimakon mutanen Cocinsu, inda suke gayyatarsa zuwa tarukan zagayowar ranar haihuwarsu da bukukuwansu.

“Ina jin dadin yin zane a cikin Coci saboda a kan ba ni lokaci domin in kammala zanen da nake yi bayan an kammala wa’azi,” inji Chukwu, wanda yanzu ya haura shekara takwasa yana wannan sana’a.

“Halartar wasu tarukan ta taimaka min wajen kara kwarewa, sannan na fara kwarewa a zane-zane masu dauke da rubuce-rubuce.”

Zane-zane masu dauke da rubuce-rubuce na nufin yin zane sannan a yi rubutu a ciki. Chukwu na fara tsara irin wannan zanen ne da manhajar canvas, sannan ya daura zanen a kansu, har su fita fes.

“Wasu lokutan nakan yi zane-zanen a wajen zanena, wato studiyon zane, sannan in nada bidiyo, yadda mutane za su iya kalla a wuraren taro,” inji matashin wanda ya koya wa kansa nada tare da tace bidiyo.

“Yawancin bidiyoyin da nake daurawa a intanet, ni ne nake dauka, sannan in tace su da wayata.”

Zane-zane ido a rufe

Chukwu yana kuma aiki a matsayin manajan aikace-aikace a wani wajen daukar hoto a Accra-aikin da yanzu ya kai shekara hudu yana yi, wanda a cewarsa ya taimaka masa wajen kara kwarewa.

“Yin aiki da masu zane da dama na Afrika ya taimaka min wajen kara kwarewa a wannan sana’a, sannan ya taimaka min wajen sauya fasalin yadda nake gudanar da ayyukana,” in ji shi.

Ya fara gudanar da zane idon shi a rufe kai-tsaye, amma ya ce akwai sauran lokacin kafin ya kara samun kwarewa a wannan fannin.

Chukwu yana samun hadakar aiki da masu wakokin baka da sauransu-inda yake musu zane da sauran ayyuka idan za su yi taro.

“Yanzu haka mun fara shirin shirya wani babban taro da wani mai rufa-ido domin masu sha’awar zane-zane da dabarun rufa ido,” in ji shi, sannan ya kara da cewa, “akwai dadi yadda mutane suke kaunar ayyukanmu.”

TRT Afrika