Ana cin dodon kodi, hada magani da kayan gyaran jiki da su. Photo: TRT Afrika

Daga Kudra Maliro

Kasuwancin dodon kodi na haskawa kuma na kara shahara a Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo, inda ke bai wa mazauna karkara da ke kusa da dazuzzuka hanyar samun kudade da kuma abinci mai gina jiki.

Tsawon shekaru, manoma na samun ranar fita daji lokacin damuna, ba wai saboda amfanin gonarsu ya samu isasshen ruwa ba, sai don yadda dodon kodi suke fitowa sosai a dazukan.

Jama’ar karkarar na kama halittun da ke tafiya a hankali tare da sayar da su a kasuwannin birane a raye ko bayan an babbake su.

Kama dodon kodi sana’a ce dadaddiya da aka samo daga kaka da kakanni a yankuna masu zafi da ke Afirka.

Manoma a Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo na kama dodon kodi a lokacin damuna. Photo: TRT Afrika.

A Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo, wasu 'yan dukurkuran mutane gajeru ne suka fi kama dodon kodin. Su ne mutanen da aka ce sun fara zama a kasar.

Dodon kodi na taimakon iyalai

Kasuwanci ne babba a garuruwa da biranen Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo, inda dodon kodi uku ko hudu ke kai wa darajar dalar Amurka daya a wajen masu sayarwa daya-daya, wadanda su kuma suke saya a kan farashin sari daga hannun manoman a kan dala 0.75.

Kasuwancin dodon kodi na amfanar iyalai da dama a Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

Celestine tana kasuwancin dodon kodi tun sama da shekara goma, kuma ta bayyana yadda take farin ciki da alfanun da take samu.

Ta ce “Da wannan kasuwancin kadai na samu damar tura ‘ya’yana da jikokina zuwa makaranta, ina ciyar da iyalina inda a yanzu haka nake kan gina gida.”

Abinci mai gina jiki

A kasashen Afirka da dama musamman yankunan sahara ana kyamar dodon kodi.

Daga baya ne aka gano yana dauke da sinadarin gina jiki na protein. Ba kowa ke cin dodon kodi ba.

Kwararru sun bayyana amfanin dodon kodi wajen gina jiki amma mutane da yawa ba sa iya ci. Photo: TRT Afrika.

Wasu na yi masa kallon tsana da ma tsartar da yawu idan suka gan shi, duk da cewar kwararru sun bayyana suna dauke da sinadaran gina jiki sosai.

“Suna da sinadarin protein da yawa, za a iya dafa farin dodon kodi mara kashi da mai ko kuma kandas,” in ji Botende Baelongani, kwararren likitan masu fama da ciwon sukari da ke aiki a Babban Asibitin Makiso na garin Kisangani.

Ya shaida wa TRT Afirka cewa ”Ba shi da maiko kuma yana dauke da sinadaran vitamin B, D da E. Namansa na dauke da sinadarin asid wanda ke da amfani sosai wajen lafiyar koda da hantar dan adam.”

Ya kara da cewa “Ana cin naman dodon kodi da shinkafa ko ayaba ko rogo da sauran nau'o'in abinci da mutane ke yi.”

Kayan kwalliya

Ba kawai sinadarin gina jikin da dodon kodi ke dauke da shi ne ya sanya shi shuhura ba. Ana amfani da wadannan halittu masu kokon baya wajen samar da magungunan gargajiya da ma yin tsubbace-tsubbace a Jumhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

A kasashe da dama da suka hada da Ivory Coast ana sayar da dodon kodi a kasuwanni. Photo: Reuters

Ana kuma amfani da dodon kodi wajen samar da wasu magungunan zamani da kayan gyaran jiki – musamman ma kokon bayansu.

Akwai dubban jinsin halittar dodon kodi a duniya, amma ba dukkan su ne ke da alfanu ba.

Akwai kusan nau’uka 600 na dodon kodi da ke da hatsari – mafi yawansu na rayuwa a cikin ruwa. Saboda haka sanin yadda za a tantance wanne ne za a iya ci na da matukar muhimmanci ga al’umma.

TRT Afrika