A wasu al'ummu tsada ko ingancin akwatin gawa yana nuna irin girman matsayin wanda ya mutu. Hoto: TRT Afrika.      

Daga Kudra Maliro

Mutane suna kara kirkiro wasu al'adu yayin suturta gawa ko makoki a Kamaru, inda mutane daga kowane bangare suke kashe kudi kan akwatunan gawa.

Wadannan akwatunan kasaitan ana yin su ne bisa la'akari da sana'ar mamacin. Kasuwancin akwatunan gawa yana ci gaba da bunkasa a Bamenda, yankin kasar da ake magana da harshen Turanci.

Wani birnin da ake hada-hada a yankin Arewa maso Yammacin Kamaru, Bamenda ya kwashe tsawon shekaru yana fama da tashe-tashen hankula.

Waje ne aka yi tsawon shekara shida ana yaki tsakanin 'yan aware da dakarun Kamaru.

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ya tilasta wa dubbai barin gidajensu ya kuma durkusar da tattalin arzikin Bamenda, idan aka kwatanta da wasu birane.

Mutane da dama musamman Kiristoci sun rungumi sabuwar al'adar yin akwatin gawa. Hoto: TRT Afrika.

A tsakiyar tashe-tashen hankali, "idan aka binne mutum, to ya yi sa'a da rakiyar 'yan uwa da masoya," kamar yadda Arnaud Kouamo, wani dan jaridan Kamaru da ke zaune a Bamenda, ya shaida wa TRT Afrika.

Karuwar bukatarsa

Kasuwar akwatin gawa tana kasa bunkasa. Ana ci gaba da yin bukukuwan jana'iza. A wasu al'ummomi shagulgulan jana'iza da tsadar akwatin gawa ya nuna girman matsayin wanda ya mutu.

Saboda yadda kasuwar akwatin gawa ta bude, kafintoci kamar Ndeh za a iya cewa su ma kasuwarsu ce ta bude.

"Na san wata mata wacce take da wani inji kuma take aikin kasuwancin akwatin gawa, saboda haka na fara aiki a matsayin kafinta mai yin akwatin gawa.

Kuma sai hakan ya zama wani abu da ke shaukin yi," kamar yadda Ndeh ya shaida wa TRT Afrika.

Mai shekara 43 din da ke aikin akwatin gawar ya ce galibin kwastomominsa Kiristoci ne.

Bamenda yana da mazauna kimanin 600,000, wasu daga cikinsu suna da niyyar sayar wa dan uwansu ko na kusa da su da ya rasu akwatin gawa don martaba shi da kudinsa ya kai dala 3,500.

A kan akwatin gawar ana rubuta sunan sana'ar mamacin. Hoto: TRT Afrika.

Ana yin akwatin gawar ne iri daban-daban akwai masu siffan lasikifa da mai siffar takalmi da mai siffar baibul da mai siffar mota ko kwalba wadanda wasunsu suke nuna irin burin karshe da mamacin yake da shi kafin mutuwarsa.

Sana'ar yin akwatin gawa tana bukatar kwarewa da basira. "Ina tsara kowane irin zane kamar lasifika da gidaje da baibul kai duk wani abu da kake bukata, zan iya yi akwatin siffarsa.

"Har ila yau zan iya yi maka siffan zaki da damisa da giwa ko kuma sauran siffan dabbobi," in ji Mista Ndeh.

Kauna da martabawa

Mutane da yawa mazauna Bamenda sun shaida wa TRT Afrika cewa suna alfahari da wannan sabuwar al'adar wadda suka ce tana martaba wadanda suka mutu saboda ana binne su a cikin akwati mai siffan wani abin sana'arsu lokacin suna raye.

Sai dai wasu suna ganin al'adar tana kara dora nauyi kan dangi yayin jana'iza.

"Dan uwana ya rasu wasu shekaru da suka wuce. Kwararren direba ne. Mu danginsa mun riga mun saya masa akwatin gawa amma sai abokan sana'arsa suka kawo masa wannan akwatin mai siffar mota.

"Hakan ya sosa zukatanmu sosai kuma ba mu annashuwa," in ji Dingana Raymond.

"Wannan kauna da martabawa ne daga abokan aikinsa duk da cewa ba ya raye," in ji Mista Dingana.

Wasu 'yan Kamaru suna cewa sabuwar al'adar ta sa bikin jana'izar ya kara tsada / Hoto: TRT Afrika.

A watan Yunin 2022, wani tsohon dan wasan Kamaru Nguéa Jacques, ya rasu, yana da shekara 67. Jacques ya taba taka leda a tawagar kasar Kamaru wato Indomitable Lions.

Taimaka wa wadanda suka yi rashi

Wata kafar yada labarai ta ruwaito cewa tsohon dan kwallon kafar Kamaru kuma Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kasar (FECAFOOT), Samuel Eto'o, ya ba shi kyautar akwatin gawa mai siffar takalmi wanda aka kiyasta kudinsa da dubban daloli don martaba shi.

Sai dai wannan sabuwar al'adar ta yin akwatin irin wanda kake so, kuma hakan ya jawo kashe kudi sosai.

Wasu suna ganin masu yin akwatin gawa kamarsu Mista Ndeh suna samun riba daga mutuwar wasu. Sai dai ya yi watsi da wannan zargi.

"Ba na yi wa kowa fatan mutuwa. Sai dai ana yin mutuwa, dangi sukan bukace ni da yi akwati. Ni ina ganin yaba min ma kamata a yi.

"Ina taimaka wa dangin mamaci su binne dan uwansu cikin daraja," in ji Mista Ndeh.

TRT Afrika