Tatsuniyoyin Kenzaru - an bayar da labarin Zau a Swahili. Hoto: Tales of Kenzaru

Daga Charles Mgbolu da Gaure Mdee

Akwai wani sabon gem na zamani a jerin wasannin da ke kan Xbox, Playstation 5, Nitendo Switch da Microsoft Windows wanda ke da alaka sosai da labaran al'adun Swahil.

Tatsuniyar Kenzaru: Zau, da Abubakar Salim ya samar, jarumi dan Birtaniya da Kenya kuma dan kasuwa, wasannin gem ne da aka bayar da su a yaren Swahili kuma suna bayar da labarin Zau, wani matashi da ya tafi wata kasa mai kyau amma mai hatsari don kama ruhanai da nufin su dawo da mahaifinsa da ya mutu duniya.

Rasuwar mahaifin Salim sakamakon kamuwa da ciwon daji 'yan shekaru da suka gabata ne ya ba shi karfin gwiwar hada gem din.

A cikin gem din na Zau akwai kwazazzaɓai, magangarar ruwa da manyan hatsabiban ruhanai wadanda sai ya yake su ne yake iya yin gaba a tafiyarsa.

Masu tsokaci ba iyakacin gudanar yaki da ke kayatar da masu yin gem din da sanya su gaza kosawa da shi ba ne suka yi tsokaci a kai, har ma da bazar Afirka da gem din ke nunawa.

Masu yin gem din na kallon Zau a yankuna da salon gidajen Afirka, daga gidaje masu nau'ika daban-daban, da tarin yashin sahara da ke jan hankalin idanuwa, zuwa ga korran ganyaye dunkulallu da ke bayyana kyawun dazukan Afirka.

Tatsuniyar Kenzaru na habaka labaran Afirka ta hanyar gem. Hoto: Tales of Kenzaru

Leon Oscar Lwoga mai samar da wannin gem mai zaman kansa ya fada wa TRT Afirka cewa "Abun ban sha'awa ne ganin gem kamar na tatsuniyoyin Kenzara dag mhangar Afirka.

"Kamar wata sabuwar iskar shaƙa ce. Wani sabon abu ne na daban, wani da babu irin sa. Tabbas, wannan abu na sanya 'yan Afirka su ji cewa ana ganin su a dukkan fadin duniya."

"Gem din na taimaka musu wajen kulla alaka da mutane da suke kamar su ta hanyoyi da yawa. Yana da kyau a kalli cewa akwai karfafawa sosai kan bayar da labarin Afirka daga mahangar Afirka." in ji shi.

Haka kuma gem din na sake bayyana habaka da yaduwar labarai da almarorin Afirka.

Labarai da almarorin Afirka, wata gwagwarmaya ce ta adabi, wake da wasannin gargajiya da ake bayyana su a sigar fim na zamani ta hanyar fitar da tarihi da al'adun bakar fata.

Tatsuniyar Kenzaru na da jigo daga labarai da almarorin Afirka. Hoto: Tales of Kenzaru

Labarai da almarorin Afirka a zamanance na sake dawo wa a kishirwar neman sabbin mahanga kan labaran Afirka. Nasarar fina-finan Hollywood irin su Black Panther sun sake yada wannan manufa da jigo.

Lwoga ya kara da cewa "Ba a Afirka ake hada wasan gem din gaba daya ba; yana iya zama hanyar nishadi da kuma bayar da labarai. Kamar fina-finai da litattafai, gem ma na iya zama hanyar bayar da labarai."

Ya kara da cewa "Suna bayyana duniya irin karfi da kokarin da muke da shi. Ina tunani mutane da yawa ba su san abubuwa da dama game da wannan nahiya ba. Idan ka samu wasannin gem da aka samar a Afirka game da 'yan Afirka, hanya ce da za mu yada tarihinmu."

Tatsuniyoyin Kenzaru sun samu yabo sosai daga masu tsokaci kan gem. Hoto: Tales of Kenzaru

Masana'antar samar da wasannin gem a duniya na gudanar da kasuwancin biliyoyin daloli kuma ta wanzu tsawon shekaru.

A 2022, kudaden shigar da aka samu daga kasuwancin gem a duniya baki daya ya kai kusan dalar Amurka biliyan 347, inda wasannin gem na wayoyin hannu suke samar da dala biliyan $248, kamar yadda Statita suka bayyana.

Kasuwar gem din na ta habaka kuma tana kara samun fasahar inganta ta inda suke bude sabbin damarmaki ga masu samar da gem din, da nufin samar da kwarewa ta hanyar sabbin fasahar kere-kere da ke zuwa kamar wasannin gem na cloud da VR.

"Wannan zai karfafa gwiwar masu samar da gem da yawa na Afirka su ji kamar 'idan wani kamar ni ya samar da ingantaccen gem; to, in tunani an iya yin abu irin haka'" in ji Lwoga.

TRT Afrika