Wasu ma'aikata ma'akatar ajiyan makamashi a birnin Cape Town, South Africa, April 5, 2023 /Hoto: Reuters

Daga Horman Chitonge

Ga mutane da yawa, magana kan juyin juya halin fasaha a Afirka yana daidai da magana game da kamfanonin da suka habaka cikin kankanin lokaci.

Manazarta da suke shakka kan ko Afirka za ta iya kasancewa nahiya mai masana’antu, suna nuni da yadda ci gaban masana’antu ya gagari nahiyar. Amma wannan wata tambaya ce wadda ke da cike da kuskure.

Ya kamata a mayar da hankali ne kan ko akwai wani abu a cikin nahiyar wanda zai iya tayar da ci gaban masana’antu tare da sauya al’ummar Afirka.

A lokacin da a aka fito da tambaya ta wannan hanyar, ya fi saukin samun amsa dangane da irin shaidar da mutum ya gabatar a matsayin ginshikin amsar.

Akwai dalilai da suka janyo halin da Afirka ke ciki, kuma abubuwan da za su iya tayar da ko taimaka wa juyin juya halin masana’antu.

Ana alakanta juyin juya halin masana’antu da juyin juya halin masana’antun Birtaniya (BIR) da aka yi imanin cewar an yi a bayan karni na 18 ya wuce rabi.

Duk da haka, akwai cece-kuce kan ma’anarta. Wasu masana sun ce maganar na iya batar da mutum, idan ana magana kan BIR, domin ba a samu sauyi na kwatsam ba cikin al’umma— an samu sauye-sauyen ne a hankali ba kwatsam ba.

Wasu ma sun ce yanayin yadda tattalin arziki ke girma ya fi karanci a lokacin da aka fi alakantawa da farkon juyin juya halin masana’antu na Birtaniya fiye da lokacin da ya wuce gaba da shi.

Ba ma’anar maganar kadai ake musantawa ba. Iya ayyana dalilan da suka janyo juyin juya halin Birtaniya ma ya kasance abu mai cike da cece-kuce.

Masana kan tarihin tattalin arziki sun ci gaba da muhawara kan wannan batun, inda wasu ke bayyana cibiyoyin gwamnati a matsayin muhimmin abin da ya tayar da juyin juya halin masana’antu na Bitaniya (BIR), yayin da wasu ke alakanta shi da irin abubuwan da mutanen Birtaniya suka fuskanta.

Akwai kuma wadansu da suka yi ishara ga tasirin kimiyyar Newton, wadda ta janyo kirkire-kirkiren da suka sauya kere-kere na masana’antu da ma al’umma kanta.

Wannan ya nuna cewa “Bayyana juyin juya halin masana’antun wata babbar matsala ce ta kimiyyar zamantakewa, kuma an alakanata abubuwa da dama da suka faru a baya a matsayin ababen da suka janyo juyin juya halin.

Idan aka yi la’akari da cece-kucen da ya dabaibaye juyin juya halin masana’antu, a nan ana kiransa ci gaba mai dorewa na tsawon lokaci da aka samu a tattalin arziki wanda ya kawo sauyi a al’umma gaba daya.

Fannin hakar ma'adinai na kasar Rwanda na bunkasa cikin 'yan shekarun nan / Photo: Reuters

Sauya tunani

Juyin juya halin masana’antun Afirka zai bambanta da juyin juya halin masana’antu na baya a fuskoki daban-daban, domin yanayin Afirka ya bambanta da yanayin da sauran juyin juya halin masana’antun suka faru.

Amma Afirka ka iya koyon darrusa daga daga juyin juya halin masana’antu na baya.

Daya daga cikin muhimman abubuwa da za su iya janyo juyin juya halin masana’antun Afirka shi ne sauya tunani wanda galibi yake sauya dabi’a da yadda ake shawara da kuma burin mutane.

Wannan sauyin tunanin ba wai na hankali ba ne kawai, wasu dalilai ne na yanayi suka janyo shi, wadanda a yanayin da Afirka ke ciki a yau sun hada da yawan arashin aikin yi da karancin aikin yi da kuma karancin kudin shiga.

Wannan ya janyo wani tunani cewar dole mu inganta yanayin yadda muke a matsayinmu na mutane a nahiyar.

Sauyin tunanin ya yi karfi sosai cikin matasan da nake zantawa da su a matsayina na mai ba da shawara da mai bincike da kuma masani.

Sakamakon wannan shi ne karin matakin kwarewa da kirkire-kirkire wajen tunkarar kalubale na yau da kullum da kuma fara samar da juyin juya halin kwarewa a hankali, wanda yake zuwa kafin a samu juyin juya halin masana’antu.

A yanayin da Afirka ke ciki a halin yanzu, maganar da ake cewar ‘tsabar bukata ce take janyo dukkan kirkire-kirkire’ ya zama wani muhimmin dalili.

Wannan a bayyane yake wajen karin son shiga harkar kasuwancin da ake samu.

Rashin samun aikin yi a ma’aikatu ne yake jnayo wannan, kuma wannan ne ya sa tsabar bukata ke janyo kirkire-kirkire.

Wadansu abubuwan da ka iya kawo sauyin sun hada da sauyin shekaru da jinsi na mutane, wanda karin yawan mutane masu aiki cikin gaggawa ke janyowa inda ake hasashen cewar nahiyar ce za ta samar da kashi 35 cikin 100 na ma’aikatan duniya a shekarar 2050, kuma nahiyar za ta samu rabin ma’aikata zuwa shekarar 2100.

Afirka ce nahiya ta biyu a yawan mutane a duniya , kuma wasu na ganin ya kamata wannan ya kasance wata fa'ida a gareta./ Photo: Reuters

Karuwar birane ma na cikin abubuwan da za su tayar da juyin juya halin masana’antun Afirka, wanda aka alakanta da yadda mutane ke kokarin bi da mawuyacin yanayin da suke ciki.

Karin matsi a kan fili yayin da ake samun karancin yawan masu aiki a kan filayen noma a yanayi na karancin amfani gona ka iya zama wani sanadi.

Cinikayya mara shinge tare da kimiyyar komfuta

Ababen da za su tayar da juyin juya halin masana’antun Afirka tare da za su iya samar da wani yanayi na sauyi, amma idan ana son wannan sauyin ya dore dole a samu ababen da za su taimaka masa.

Muhimman abubuwan da za su taiamaka wa wannan sauyin su ake kira muhimman fannoni irin su sufuri da sadarwa da ayyukan da ke taiamaka wa kasuwanci da aiki da makamashi da aikin komfuta da aikin ruwa da ayyukan al’umma irin su kiwon lafiya da ilimi.

Samar da kasuwa bai daya da kuma hanyar inganta kayayyakin sayarwa na yanki (RVCs) ta hanyar yarjejeniyar kasuwa bai daya na Afirka (ACFTA), wani abu ne da ke taimaka wa juyin juya hali na masana’antu a Afirka.

Ida kana son dukkan wadannan masu taiamaka wa juyin juya halin masana’antu su sa juyin ya dore, dole a samu samu tsarin masana’antu na gwamnati mai aiki da zai hada komai don tabbatar da cewa ana samun ci gaba cikin gaggawa.

Akwai wata fahimtar da ta shahara cewar harkar intanet za ta tayar da juyin juya halin masana’antu a Afirka.

Duk da cewar harkar intanet na da muhimmanci wajen samar da yanayi mai taimakawa wajen samar da sauyin masana’antu, ababen da ke asalin tayar da juyin juya halin masana’antu suna shimfide a yanayi da kuma albarkatun nahiyar.

Marubucin, Farfesa Horman Chitonge, malami ne a cibiyar nazari kan Afirka, a Jami’ar Cape Town.

Togaciya: Ra’ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai ne su zama ra’ayi ko mahanga ta TRT Afrika ba

TRT Afrika