Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya sanar da shigar Turkiyya cikin shari'ar tuhumar kisan kiyashin da ake yi wa Isra'ila a kotun ICJ, yana mai bayyana kudurin kasar na tabbatar da adalci da kuma goyon bayan 'yancin Falasdinu. Hoto: AA

Matakin da Turkiyya ta ɗauka na shiga tsakani a shari'ar kisan ƙare-dangi da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila a kotun ƙasa da ƙasa ta ICJ, wani gagarumin ci gaba ne a fagen shari'a kan ta'asar da ake ci gaba da yi.

Sashe na 63 na dokar ICJ ya bai wa Turkiyya damar shiga cikin lamarin, tare da ba ta damar gabatar da ra'ayoyinta kan lamarin.

Shari’ar da kanta ta shafi zargin kisan ƙare dangi da Isra’ila ta aikata, musamman game da ayyukanta a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023. Tuni dai kotun ICJ ta ba da umarni ga Tel Aviv, inda ta buƙaci sojojin Isra’ila da su guji aikata kisan ƙare dangi da kuma ɗaukar matakan tabbatar da agaji ya kai ga fararen hula a Gaza.

Sanarwar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan na shiga tsakanin da Ankara ta yi ya fayyace muhimmancin jajircewar ƙasar wajen ganin an yi adalci da kumama matsayarta a kan batun kisan ƙare dangin.

Matakin ya kuma yi daidai da manyan manufofin Turkiyya na ƙasashen waje, musamman dangane da matsayinta a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma goyon bayan da take bai wa Falasɗinu.

Shigar da Turkiyya a cikin wannan lamari yana ƙara kawo sabon salo ga shari'ar, da yiwuwar yin tasiri ga hukuncin da kuma nuna rikitaccen yanayin siyasa a yankin. A yayin da ake ci gaba da shari'ar, duniya za ta sa ido sosai don ganin yadda tsoma bakin Turkiyya zai taimaka wajen yin adalci da kuma makomar rikicin Isra'ila da Falasdinu.

"Za mu dage da yunƙurin tabbatar da cewa Isra'ila, wadda aka riga aka yanke mata hukunci a cikin lamirin ɗan'adam, ta fuskanci sakamakon shari'a saboda ayyukanta.

Tsawon shekaru 75, Isra'ila ta yi tana nuna wariyar launin fata, da shekaru 56 tana mulkin mallaka, da kuma shekaru 16 da ta shafe tana aiwatar da manufofin killace Falasdinu, da nufin mamaye yankunan Falasdinawa da samar da tsarin da zai bai wa 'yan kama wuri zauna damar keta hakkin jama'ar Falasdinu, "in ji Farfesa Cuneyt Yuksel, Shugaban Hukumar Shari'a ta Majalisar Dokokin Turkiyya.

"Isra'ila, ta hanyar hare-haren da take kai wa al'ummar Gazan da kuma maganganun shugabannin Isra'ila, na ƙarfafa kisan gillar da ake yi wa Gazan, ta bayyana manufarta na kisan kare dangi tare da keta yarjejeniyar 1948 da ta hana aikata laifukan kisan kiyashi.

"Dole ne a yi amfani da dokokin kasa da kasa kuma a kiyaye su daidai ga kowa da kowa a kowane yanayi, ba tare da ware wani sashe ba,” in ji shi.

"Muna fatan kotun ƙasa da ƙasa ita ma za ta yi aiki da wannan ƙa'ida, kuma muna sake bayyana cewa mu a matsayinmu na Turkiyya, za mu ba da dukkan goyon bayan da za mu iya kan wannan tsari a gaban kotun."

Sabon babi a shari'ar

Idan har aka amince da bukatar Turkiyya, za ta zama ƙasa ta farko a cikin mambobin Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Musulmai ta OIC da ta tsoma baki cikin wannan harka.

“Abin da muke fata daga kotun ICJ shi ne cewa kisan kiyashi, laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaƙi da Isra’ila ta aikata, ya kamata a bayyana su da kuma sanar da jama’a cikin gaggawa.

"Ya kamata a yanke hukuncin ƙarshe na Kotun ta yin abin da ya kamata, da kuma fara aiwatar da hukuncin da wuri-wuri, ta hanyar yin da la'akari da yanayi na ban mamaki da ke faruwa a yankin," in ji Yuksel.

Matakin zai kuma sake fayyace jajircewa Turkiyya na son a yi adalci, da yadda take azama wajen ɗaukar matakai kan batutuwan da suka shafi hakkin ɗan'adam da shari'ar ƙasa da ƙasa.

Shiga lamarin da Turkiyya za ta yi zai ba da muhimman ra'ayoyi kan yadda ya kamata a fassara wannan yarjejeniya ta fuskar zargin Isra'ila.

"Turkiyya na da burin ƙarfafa shari'ar Afirka ta Kudu da wannan matakin. A baya dai Nicaragua da Colombia sun yi kokarin shiga tsakani a cikin shari'a guda tare da wasu aikace-aikace daban-daban, amma har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan bukatarsu ba.

"Amfanin tsoma bakin Turkiye da sauran al'ummomi a cikin shari'ar Afirka ta Kudu shi ne cewa za ta iya samar da karin sabbin shaidu na keta dokokin da Isra'ila ta yi na yarjejeniyar kisan ƙare dangi," in ji lauyan Ba'amurke, Frank Romano.

"Har ila yau, za ta iya neman zaman sauraron shari'a na daban a gaban alkalan kotun ICJ, ta yadda za su iya ganin ƙarin shaidun keta hakkin ɗan'adam da Isra'ila ke yi, su kasance da niyyar ba da umarnin ƙarin matakan wucin-gadi, kamar ba da umarnin tsagaita wuta.

Yana iya zaburar da sauran mambobi, kamar membobin Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai, su shiga shari'ar Afirka ta Kudu. Hakan zai inganta lamarin Afirka ta Kudu," Romano ya ƙara da cewa.

TRT World