Babu wata hujja ko dalili na kai wa ƴan'uwana da ke Gaza hare-hare, wanda a yanzu ya kai wani mataki na kisan kiyashi in ji Erdogan. Hoto: AA

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jawo hankali kan mummunan halin jinƙai da ake ciki a Gaza ta Falasɗinu, yana mai jaddada cewa babu ruwa babu burodi ba abinci a Gaza a yanzu haka, wanda hakan ya saɓa wa Yarjejeniyar Ƙasashen Duniya ta Ƴancin Ɗan'adam.

Da yake magana a wani taro na Cibiyar Matasa ta Turkiyya (TUGVA) da aka yi a babban birnin ƙasar Ankara a ranar Alhamis, Erdogan ya jaddada cewa ba kamar sauran hukumomi ba, ya zama wajibi ƙasashe su girmama dokokin yaƙi da na ƴancin ɗan'adam.

"Muna ganin yadda wannan ɓangaren yake gushewa da sannu," ya ce.

Shugaban na Turkiyya ya ce yanke wuta da ruwa da fetur da abinci ga mutum miliyan biyu a Gaza "babu tausayi" kuma ba shi da muhalli "a dokokin yaƙi."

"Ina ƙasashen Yammacin Duniyar? Akwai wasu matakai da suka dauka a wannan gaɓar? Babu su," ya faɗa. "Babu wata hujja ko dalili na kai wa ƴan'uwana da ke Gaza hare-hare, wanda a yanzu ya kai wani mataki na kisan kiyashi."

Shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga dukkan masu hannu da ke da faɗa a ji a lamarin da su sassauta rikicin, yana mai cewa: "Ba ma son rikicin ya yaɗu zuwa yankinmu, maimakon a dinga goyon bayan wani ido a rufe, muna kira ga masu faɗa a ji a lamarin da su rage tashin hankalin."

A kan batun tsarin Amurka kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu kuwa, Erdogan tambaya ya yi cewa: "Kamata ya yi a ce ƙasa kamar Amurka ta tabbatar da mayar da zaman lafiya, ko kuwa ƙara rura wutar rikicin?

Munana yanayin rayuwa

Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da ɗaukar zafafan matakan soji a kan Gaza wacce dama an yi mata ƙawanya, a wani martani kan harin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta kai wa Isra'ilan.

Rikicin ya fara ne a lokacin da Hamas ta fara wani hari na Operation Al Aqsa Flood a kan Isra'ila, wani harin shammata da ya haɗa da harba rokoki cikin Isra'ila ta ƙasa da ta ruwa da ta sama.

Hamas ta ce harin ramuwa ne kan far wa Masallacin Ƙudus da ake yi a Gabashin Birnin Ƙudus da kuma yadda Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke kai wa Falasɗinawa hare-hare.

Ita ma rundunar sojin Isra'ila ta mayar da martani a wasu hare-hare da ta kira Operation Swords of Iron kan Hamas a Gaza.

Martanin na Isra'ila bai tsaya a kan hare-haren ba sai da ta yanke wuta da ruwa zuwa Gaza, lamarin da ya munana halin da ake ciki a yankin tun bayan wasu takunkumai da aka sanya masa a shekarar 2007.

Fiye da mutum 2,700 aka kashe tun bayan ɓarkewar rikicin a ranar Asabar, da suka haɗa da Falasɗinawa 1,400 da Isra'ilawa 1,300.

Ministan Makamashi Israel Katz a ranar Alhamis ya ce ba za a bai wa Gaza ruwa da lantarki da fetur ba har sai an saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.

AA