Kayayyakin da ake kai wa Falasɗinu dole sai an rubuta musu Isra'ila ko an rubuta "ta Isra'ila." / Hoto: Reuters

Kasuwanci tsakanin Turkiyya da Isra'ila ya ragu sosai tun bayan da Isra'ila ta mamaye Gaza a bara, kamar yadda bayanai daga Ma'aikatar Cinikiyya ta Turkiyya suka nuna.

Daga ranar 7 ga Oktoban bara zuwa 20 ga watan Maris na wannan shekara, jimillar yawan cinikayya tsakanin Turkiyya da Isra'ila ya ragu da kashi 33 cikin 100, kamar yadda bayanan da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya gano daga majiya a ma'aikatar.

Bayanan sun nuna cewa, kayayyakin da Turkiyya ke fitarwa zuwa Isra'ila sun ragu da kashi 30, yayin da kayayyakin da take shigowa da su daga Isra'ila suka ragu da kashi 43.4 cikin 100.

'Yan ƙasar Turkiyya da kamfanonin Turkiyya suna ta soke odar kayayyakin da suka yi tare da Isra'ila, kuma da ma yawancin kasuwancin, kamfanoni masu zaman kansu ne suke yi, da kamfanonin ƙasa-da-ƙasa, ba wai na gwamnati ba.

Kayayyakin da aka tura daga Turkiyya zuwa Falasɗinu suna wucewa ne ta Isra'ila, da shingenta na kwastam, saboda Falasɗinu ba ta da hukuma ko kayan aikinta na kwastam.

'Shiga ta Isra'ila'

Duka kayayyakin da ake kai wa Falasɗinu dole sai an rubuta musu Isra'ila ko an rubuta "ta Isra'ila" a jikinsu.

Bugu da ƙari, Isra'ila ba ta amincewa da mu'amalar shari'a tsakanin Falasɗinu da wasu ƙasashen daban, kuma ba ta barin cinikayyar kasuwanci ta hanyar iyakar Rafah da ta haɗa Gaza da Masar.

Sakamakon haka, cinikayyar wasu ƙasashen da Falasɗinu kusan a koyaushe ana rubuta cewa kasuwanci ne da Isra'ila, a bayanan da suke ƙididdigar kasuwanci na duniya.

Isra'ila ta afka wa Gaza da mummunan yaƙi tun lokacin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ƙaddamar da wani hari a Oktoban bara, wanda ya kashe ƙasa da mutane 1,200.

Tun bayan nan, kusan Falasɗinawa 33,200 ne hare-haren Isra'ila ya kashe, sannan mutane 75,900 suka raunata, baya ga rushe-rushe da ƙarancin kayan buƙatun rayuwa a yankin.

Haka nan, Isra'ila ta ƙaƙaba wa Gaza takunkumi, inda al'ummar yankin musamman mazauna arewacin Gaza, suke fama da yunwa.

Yaƙin Isra'ila ya tilasta wa kashi 85 na al'ummar Gaza rasa matsuguninsu, ga kuma matsanancin ƙarancin abinci da ruwa mai tsafta, da magunguna, yayin da aka lahanta kashi 60 na kayayyakin more rayuwa a yankin, cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ana zargin Isra'ila da kisan ƙare dangi a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta (ICJ), wadda a makon da ya gabata aka nemi ta ƙara ƙaimi don hana faruwan rashin abinci a Gaza.

AA